Tuhumar da Malami yake fuskanta reshe ne ya juye da mujiya — Sowore
Sowore ya tunatar da Malami yadda suka gurfanar da shi a zamanin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya yi musayar yawu da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, a harabar kotu da ke Abuja.
Sowore ya zolayi tsohon ministan da cewa tuhumar da yake fuskanta ta cin hanci da rashawa reshe ne ya juye da mujiya, la’akari da tsarin shari’ar da ya muzguna masa da shi a lokacin da yake madafan iko a yanzu ya juya kansa.
Wannan dai ya faru ne gabanin fara zaman shari’ar tuhume-tuhume 16 da Hukumar Yaƙi da Rashawa EFCC ta shigar kan Malami, da suka shafi zargin halasta kuɗin haram.
Sowore ya tunatar da Malami yadda suka gurfanar da shi a zamanin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Ya bayyana cewa sai da suka riƙa gargaɗinsa kan matsalolin tsarin shari’a amma ya yi biris, amma ga shi yanzu yana fuskantar irin wannan yanayi kan wannan tsari da ya riƙa taƙama da shi.
“Yanzu ka ji yadda ake ji idan ana gallaza wa mutum… irin tsarin da ka yi riƙo da shi har kana taƙama yanzu ga shi yana aiki a kanka,” in ji Sowore.
A dai harabar kotun, Sowore ya kuma yi ƙoƙarin bai wa Malami hular gwagwarmayar da yake jagoranta ta ‘Revolution Now’, yana mai neman ya shigo a ci gaba da damawa da shi amma Malamin ya ƙi karɓa, inda ya bayyana cewa: “Ni ina da tawa hular.”
Kazalika, Malami ya yi martani da cewa halin da yake ciki ba yana nufin an yi rinjaye a kan shi ba ne, yana mai cewa, “duk yadda aka juya ba za taɓa kai ni ƙasa ba.”
Wannan sabuwar cacar baki ta sake tayar da tsohuwar gabar da ke tsakanin su tun shekarar 2019, lokacin da aka kama Sowore bayan shirya gangamin ‘Revolution Now’, inda aka tuhume shi da laifuffuka ciki har da cin amanar ƙasa.
A ɓangaren siyasa, Malami ya ce har yanzu yana halartar tarukan jam’iyyar ADC, duk da cewa bai samu halartar wani muhimmin taron jama’iyyar da aka gudanar a Ibadan ba.