Tukuici ga mai azumi (2)

Mutanen da azumi bai wajaba a kansu ba  1. Kafiri: Azumi bai wajaba a kan Kafiri.2. karamin yaro: Azumi bai wajaba a kansa ba har sai ya balaga kuma ana gane balagar yaro ta hanyoyi uku:(i) Fitar maniyyi ta hanyar mafarki ko ta wata hanya daban.(ii) Tsirar gashin hammata ko gaba.(iii) Da shekara 12 ga […]

Tukuici ga mai azumi (2)
Tukuici ga mai azumi (2)

Mutanen da azumi bai wajaba a kansu ba 

1. Kafiri: Azumi bai wajaba a kan Kafiri.
2. karamin yaro: Azumi bai wajaba a kansa ba har sai ya balaga kuma ana gane balagar yaro ta hanyoyi uku:
(i) Fitar maniyyi ta hanyar mafarki ko ta wata hanya daban.
(ii) Tsirar gashin hammata ko gaba.
(iii) Da shekara 12 ga mata ko 15 ko 18 ga wasu ’yara maza.
Amma mata daidai da abin da aka ambata da karin ganin jinin haila wato su mata alamomin balagarsu hudu ne.
3. Hauka: Babu azumi a kan mahaukaci har sai ya warke.
4. Tsoho tukuf, wanda ba ya iya bambance wadanda ke zuwa wurinsa, to su irin wadannan tsofoffi, maza ne ko mata sai su ciyar da Mudun Nabiyyi guda a mazaunin azuminsu a duk rana har a gama azumin.
5. Haka ma hukunci yake ga wanda ba zai iya azumi ba, ko da lokacin sanyi ne, ko lokacin ruwa, saboda ciwon yunwa ko ciwon kishin ruwa kuma ba a tsammanin zai warke, shi ma zai ciyar da Mudun Nabiyyi kowace rana da ya sha azumin.
Wadanda azumi ya wajaba a kansu:
1. Mai hankali: Azumi wajibi ne a kansa.
2. Musulunci: Domin azumi bai wajaba a kan wand aba Musulmi ba.
3. Balaga: Domin azumi bai wajaba a kan yaro ba.
3. Da tsarkakuwa daga jinin haila ko jinin biki ga mata.
4. Lafiya: Mara lafiya azumi bai wajaba a kansa ba har sai ya warke.
Wadanda azumi bai wajaba a kansu ba, amma dole su biya:
1. Matafiyi idan ya sha azumi a cikin tafiya dole ne ya biya.
2. Mara lafiya yana iya shan azumi duk lokacin da ya warke sai ya biya abin da ya sha.
3. Mai haila ba azumi a kanta, amma in ta yi tsarki za ta biya abin da ta sha, kuma idan mai haila ta dauki azumi sai jini ya zo mata kafin rana ta fadi, to, azuminta ya baci, haka nan kuma idan haila ya dauke mata da rana a Ramadan ba azumi a kanta a sauran wannan yinin sai dai za ta rama azumin ranar da sauran kwanakin da ta sha. Bugu da kari idan jinin ya dauke kafin fitowar alfijir ko da mintuna kadan ne kafin fitowar alfijir, to, azumi ya wajaba a kanta.
karin bayani: Shi ma jinin haihuwa (biki) kamar jinin haila ne cikin dukkan hukunce-hukuncensa.
4. Mace mai shayarwa idan ta ji tsoron danta ba zai samu nonon da za ta shayar da shi ba, sai ta ci abinci, to, tana iya cin abincin bayan azumi ya wuce sai ta rama gwargwadon abin da ta sha. Haka hukuncin yake ga mace mai ciki idan ta ji tsoron abin da ke cikinta, ita ma tana iya shan azumi kuma wajibi ne a kanta ta biya gwargwadon azumin da ta sha bayan ta haife cikin nata.
5. Wanda wani dalili ya sa ya sha azumi kamar ya yi kokari don kubutar da wata rai da za ta halaka saboda gobara ko nutsewa a ruwa, sai wurin kokarin kubutar wadannan mutane ya sha azumi, to bayan azumin zai rama gwargwadon abin da ya sha.
Sahur:
Sahur shi ne cin abinci a karshen dare kafin fitowar alfijiri da niyyar ibada. Sahur Sunnah ne don Annabi (SAW) ya ce: “Bambancin azuminmu da azumin ma’abota littafi, cin abincin sahur.” (Muslim ya ruwaito).
Ladan yin Sahur:
Annabi (SAW) ya ce: “Ku yi Sahur hakika akwai albarka a cikin yin Sahur.” (Muslim ya ruwaito).
Lokacin Sahur
An samu Hadisi daga Sabit (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Mun yi Sahur da Annabi (SAW) sai ya tashi zai yi Sallah sai na tambaye shi, na ce ayoyi nawa mutum zai iya karantawa a tsakanin kiran SalLah da barin Sahur? Sai Annabi (SAW) ya ce: “Tsakanin kiran Sallah da barin Sahur mutum zai iya karanta ayoyi hamsin.” (Buhari ya ruwaito).
Buda-Baki:
Abin da ake nufi da buda-baki shi ne mai azumi ya ci wani abu ko ya sha wani abu yayin da ya tabbatar da rana ta fadi, yin haka yana daga cikin abin da ake so don Annabi (SAW) ya ce: “Al’ummata ba za su gushe (cikin nasara) ba, matukar suna gaggauta buda-baki.” (Buhari ya ruwaito Hadisin).
Abin da ake Buda-Baki da shi:
1, Kayan marmari, kamar lemu ko ayaba ko gwaiba da sauran kayayyakin marmari.
2. Dabino kowane iri danye ko busasshe.
3. In kuma ba a samu kayan marmari ko dabino ba, sai a yi buda-baki da ruwa. Saboda Annabi (SAW) ya kasance yana buda-baki ne kafin ya yi Sallah kuma yana yi ne da kwarran abubuwa wato ’ya’yan itatuwa ke nan kamar lemu da sauransu, in kuma bai samu ’ya’yan itatuwa ba sai ya yi da dabino, in babu sai ya yi da ruwa. (Tirmizi ya ruwaito).
Addu’ar Buda-Baki
“Allahumma lakas sumtu wa ala rizikika afdartu, Allahumma takabbal minni” Ma’ama: “Ya Allah gare Ka na yi azumi kuma da arzikinKa na yi buda-baki, Ya Ubangiji Ka karbi wannan azumi da na yi.”
Wadanda ake karbar addu’o’insu:
Daga cikin wadanda ake karbar addu’o’insu akwai addu’ar mai azumi yayin buda-baki. Domin Annabi (SAW) ya ce: “Mutum uku ana karbar addu’o’insu: Shugaba mai adalci da wanda aka zalunta da mai azumi lokacin buda-baki.
Ladan wanda ya ciyar da mai azumi:
Bai wa mai azumi abin buda-baki yana daga cikin sadaka mai lada da yawa, don Annabi (SAW) ya ce:
“Wanda ya ciyar da mai azumi yayin buda-baki, to za a ba shi kamar ladan mai azumin ba kuma tare da an rage wa mai azumin ladansa ba.” (Tirmizi ne ya ruwaito).
Hadisan karya a kan azumi:
1. Daga cikin hadisan da ake dangantawa ga Annabi (SAW) wadanda wasu malamai suke gani da’ifai ne akwai:
i. “Ku yi azumi za ku samu lafiya.”
ii. “Azumin watan Ramadan yana rataye a tsakanin sama da kasa har sai mutum ya bada Zakkatul Fitri.”
Wadansu malamai suna ganin cewa irin wadannan hadisai, suna daga cikin hadisan kwadaitarwa da kuma tsoratarwa don kada a yi sake.
Sallar Tarawihi:
Sallar Tarawihi tana daga cikin sallolin nafila da ake yi a cikin azumi kuma abin da ya sa ake kiranta Tarawihi, shi ne saboda zaman da ake yi a kowace raka’a biyu a yi sallama, wato an dauki wannan kamar zaman hutu ne. Yin Sallar Tarawihi sunnah ce. Gwargwadon raka’o’inta kuma goma sha uku (13) ne duk da Shafa’i daWutiri.
A wata ruwayar kuma an ce goma sha daya ne (11) duk da Shafa’i da Wutiri, saboda Hadisin da A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta ruwaito, cewa: “Annabi (SAW) ba ya kari a kan raka’o’i goma sha daya da yake yi a Ramadan ne ko ba a Ramadan ba.”
Nafilfilin dararen goma na karshen watan Ramadan:
Daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW), ya kasance idan goman karshe na watan Ramadan ya zo, to ba ya barci, sai ya tada mutanen gidansa maza da mata ya dage dantse a dukufa da nafilfili har karshen watan Ramadan.” (Buhari ya ruwaito).
I’itikafi:
Shi I’itikafi shi ne mutum ya zauna a masallaci don nafilfili da karatun AIkur’ani da addu’o’i don neman dacewa daga Allah duniya da Lahira. Shi kuma Sunnah ne da ake so, amma abin da aka fi so daga goman karshe na watan Ramadan. Kuma an ce karancinsa kwana daya da wuni, amma akasarinsa kwana uku. A wata ruwaya kuma an ce karancinsa kwana uku, amma mafi yawansa kwana goma har zuwa wata guda. Kowace ka zaba daga cikin wadannan maganganu ya yi daidai. An karbo daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: Annabi (SAW) ya kasance yana I’ittikafi a kwana goma na karshen Ramadan har ya bar duniya.