Tukuici ga mai azumi (2)
Abubuwan da suka halatta ga mai azumi:1. Yin asuwaki da rana da itacen da ba shi da dandano, wato dadi ko zaki ko bauri ko wani dandanodaban.2. Yintafiyacikin watan azumi in bukatar hakatataso.3. Zuba ruwan sanyi a kai ko wanka da ruwan sanyi in zafi yayi yawa don a ji sanyi-sanyi.4. Cin abinci da daddare […]
Abubuwan da suka halatta ga mai azumi:
1. Yin asuwaki da rana da itacen da ba shi da dandano, wato dadi ko zaki ko bauri ko wani dandanodaban.
2. Yintafiyacikin watan azumi in bukatar hakatataso.
3. Zuba ruwan sanyi a kai ko wanka da ruwan sanyi in zafi yayi yawa don a ji sanyi-sanyi.
4. Cin abinci da daddare amma ban da rana.
5. Shan abin sha nahalal da daddare.
6. Saduwa da iyali da daddare amma ba da rana a cikin azumi.
7. Amfani da magani na shafawa amma in na sha ne sai da daddare.
8. Yin allura da rana, ba laifi, idan ba ta da dandano a baki, amma ta karin ruwa ba ta halatta da rana a azumi ba. Dalili kuwa idan ciwon zai kai a karawa mutum ruwa, to ya halatta ya sha azumin in ya samu sauki sai ya rama abin da ya sha.
9. Shafa turare idan ba na hayaki ba ne.
10. Sa tozali da daddare ban da rana.
Abubuwan da ke karya azumi
1.Saduwa da iyali da rana.
2. Fitar da maniyyi da rana na karya azumi sai dai in mafarki aka yi ya fita, to, wannan azumi bai karye ba.
3. Cin abinci da rana.
4. Shan abin sha da rana.
5. Wanda ya kago amai da gangan azuminsa ya karye.
6. Fitar jinin haila ga mace mai azumi.
7. Fitar jinin biki na karya azumi.
Mutanen da azumi bai wajaba a kansu ba
1. Kafiri: Azumi bai wajaba a kan Kafiri.
2. karamin yaro: Azumi bai wajaba a kansa ba har sai ya balaga kuma ana gane balagar yaro ta hanyoyi uku:
(i) Fitar maniyyi ta hanyar mafarki ko ta wata hanya daban.
(ii) Tsirar gashin hammata ko gaba.
(iii) Da shekara 12 ga mata ko 15 ko 18 ga wasu ’yara maza.
Amma mata daidai da abin da aka ambata da karin ganin jinin haila wato su mata alamomin balagarsu hudu ne.
3. Hauka: Babu azumi a kan mahaukaci har sai ya warke.
4. Tsoho tukuf, wanda baya iya bambance wadanda ke zuwa wurinsa, to su irin wadannan tsofoffi, maza ne ko mata sai su ciyar da Mudun Nabiyyi guda a mazaunin azuminsu a duk rana hara gama azumin.
5. Haka ma hukunci yake ga wanda ba zai iya azumi ba, koda lokacin sanyi ne, ko lokacin ruwa, saboda ciwon yunwa ko ciwon kishin ruwa kuma ba a tsammanin zai warke, shi ma zai ciyar da Mudun Nabiyyi kowace rana da ya sha azumin.
Wadanda azumi ya wajaba a kansu:
1. Mai hankali:Azumi wajibi ne a kansa.
2. Musulunci: Domin azumi bai wajaba a kan wanda ba Musulmi ba.
3. Balaga: Domin azumi bai wajaba a kan yaro ba.
3. Da tsarkakuwa daga jinin haila ko jinin biki ga mata.
4. Lafiya: Mara lafiya azumi bai wajaba a kansa ba har sai ya warke.