Tukuici ga mai azumi (3)

Zakkar Fid-da-Kai: ZakkarFid-da-Kai ita ce zakkar da ake yi idan aka gama azumin Ramadan, an ce ya halatta a fitar da ita kafin a gama azumi da kwana uku ko kwana biyu, ko kwana daya ko a daren Sallah ko washegari ranar Sallah kafin a je masallaci. Domin an samu daga dan Abbas (Allah Ya […]

Tukuici ga mai azumi (3)
Tukuici ga mai azumi (3)

Zakkar Fid-da-Kai:

ZakkarFid-da-Kai ita ce zakkar da ake yi idan aka gama azumin Ramadan, an ce ya halatta a fitar da ita kafin a gama azumi da kwana uku ko kwana biyu, ko kwana daya ko a daren Sallah ko washegari ranar Sallah kafin a je masallaci. Domin an samu daga dan Abbas (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Annabi (SAW) ya wajabta mana Zakkar Fid-da-Kai don tsarkakke mai azumi daga miyagun maganganu da kuma kura-kurai. Kuma ciyarwa ce ga talaka. Wanda ya ba da ita kafin a je masallacin Idi ya samu ladar zakka cikakke, amma wanda ya ba da ita bayan dawowa daga masallacin Idi, wannan yana da ladar sadaka ce kawai.” Abu Dauda ne ya ruwaito.
Ita Zakkatul Fidiri tana kan mai gida ne da wadanda suke karkashinsa kamar matarsa da ’ya’yansa maza da mata da ma’aikatan da suke karkashinsa.
Azumin da ake so mutum ya rika yi bayan na Ramadan:
1. Guda shida a watan Shawwal, domin Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya yi azumin watan Ramadan ya kuma yi shida a watan Shawwal, to, za a ba shi ladar wanda ya shekara yana azumi.”
2. Azumin Litinin da Alhamis: Saboda Annabi (SAW) yana yawaita azumi ranar Litinin da Alhamis, sai aka tambaye shi yaya kake yawaita azumi ranar Litinin da Alhamis sai ya ce a ranakun ne ake daukar ayyukan bayi zuwa ga Allah.
3. Yin azumi uku ko wane wata, ranar goma sha uku da sha hudu da sha biyar ga wata kuma suna da lada kamar mutum ya yi azumin shekara ne. Domin duk wani aikin alheri za a ba ka lada goma.
4. Sai azumi guda tara da ake so mutum ya yi a watan Zul-Hajji da kuma guda daya na Ranar Arfa. Idan mutum ba aikin Hajji yake yi ba a wannan ranar.
5. Azumin Tasu’a da Ashura wato azumin ranar tara da kuma goma ga watan daya na Musulunci (Muharram), shi ne ake cewa azumin Tasu’a da Ashura.
Azumin da aka hana yi:
1. Azumi ranar kokwanto, (wato idan ba a tabbatar da ganin wata) a ranar 29 ga watan Sha’aban ba, dalili kuwa don ba a sani ba Ramadan ne ake ciki ko Sha’aban, saboda wannan shakkar ne aka hana yin azumi a wannan rana.
2. An hana yin azumi ranar Idi – Idil Fidiri (karamar Sallah) ko Idil-Kabir (Babbar Sallah). An rawaito Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya yi azumi ranar Idi ya saba wa Baban kasimu, (wato Annabi -SAW- ke nan don yana da da, da ake kiransa da Alkasim, sai ake kiran Annabi da Baban AI-kasim
3. An hana azumi bayan Sallah da kwana daya ko kwana biyu ko kwana uku.
4. Kebe ranar Juma’a ita kadai da yin azumi shi ma an hana.
5. Bai halatta ga mace ta yi azumin nafila ba sai da izinin mijinta.
Nasihohi zuwa ga masu azumi:
Ya ‘yan uwa Musuimi! Ku yi aiki da wadannan nasihohi:
1. Ka yi azumin watan Ramadan kana mai imani da Allah kuma ka kyauta ta shi don a gafarta maka laifuffukanka da suka gabata.
2. Kada ka yarda ka karya azumin watan Ramadan da gangan don yin haka yana daga cikin manyan laifuffuka.
3. Ka kuma tashi tsaye don yin SallarTarawihi, musamman a goman karshe wadanda ake samun
Daren LailatuI kadari a ciki don Allah (SWT) Ya ce: Alherin da ke cikin LailatuI kadari ya fi wata dubu.
4. Ka yi kokari abincinka da abinshanka su zamo na halal domin a karbi ayyukanka da addu’o’inka, kada ka yarda ka yi azumi sannan ka yi buda-baki da abin haram.
5. Ka yi kokari ka ba wani abin buda-baki ko ya buda-baki da abincinka don ka samu daidai ladan azuminsa.
5. Ka tsare salloli wato ka yi su a kan lokaci kuma tare da jama’a domin ka samu ladar jam’i kuma
Allah Ya tsare ka daga musifar rayuwa.
7. Ka yawaita sadaka domin sadakar da ta fi lada, sadakar da aka yi a Watan Ramadan.
8. Ka tsare muhimmancin lokacinka domin ayyuka nagari, don lokaci ya fi kudi tsada, don za a tambaye ka lokuta da aka ba ka me ka yi da shi kuma za a yi maka hisabi a kansa, daga karshe kuma a saka maka aikin da ka yi a rayuwarka, na alheri ko na sharri.
9. Ka je Umara in kana da hali a cikin watan Ramadan domin Umara a Ramadan tana daidai da aikin Hajji.
10. Ka yi kokari ka yi Sahur, idan so samu ne ka yi hakuri zuwa karshen dare kafin ketowar alfijir, domin Allah yana sanya albarka a cikin Sahur.
11. Ka gaggauta buda-baki da zarar rana ta fadi domin ka samu yardar Allah.
12. Ka yi kokarin yin wankan janaba in ka sadu da iyalinka a cikin daren azumi don ka samu damar yin Sallah cikin tsarki da tsabta cikkakiya tare da jama’a.
13. Ka yi amfani da damar da ka samu a cikin Ramadan, don ka dukufa ga karatun AIkur’ani domin ya zama hujjarka, ba hujja a kanka ba, kuma ya zama mai cetonka ranar tashin AIkiyama.
14. Ka tsare harshenka, kada ka yi karya kuma kada ka la’anci wani kuma kada ka yi gibar wani. Kuma ka tsare idonka, ka tsare kunnenka daga jen kade-kade da wake-wake da raye-raye da wasanni kuma ka tsare hanunka daga sata ko daukar abin da ba naka ba. Ka tsare kafarka zuwa in da bai dace ba a shari’a; domin azumi ba wai barin ci ko sha ba ne kawai, a’a kamewa ne daga dukkan abin da Allah Ya haramta, wannan shi ne hakikanin ma’anar azumi.
15. Ka yi kokari ka danne zuciyarka, ka yi hakuri, ka jure, kuma ka daure kada ka yi fadace-fadace da zage-zage: ka yi kokari ka zama natsatse, amintacce don ka samu ladar azumi cikakke.
16. Ka yi kwadayin samun tsoron Allah, a cikin azumin a sarari da boye ka rika tuna Shi ka kuma gode maSa saboda ni’imomin da Ya yi maka, kuma aikata dukkan abubuwan da Ya umurce ka, kuma ka nisanci duk abin da ya hana.
17. Ka yawaita tuba zuwa ga Allah don neman gafararSa, ka kuma roki Aljanna, ka kuma nemi tsari daga wuta a koyaushe musamman a lokacin bude-baki da sahur, domin suna daga cikin lokuta masu muhimmanci.
18. Ka yawaita adu’o’i dare da rana don tsare kanka da matanka da ’ya’yanka da kuma sauran ’yan uwa Musulmi gaba daya domin yin haka Ibada ne. Allah Ya ce mu roke Shi, kuma Ya yi alkawarin amsa mana.
19. Ka koma ga Allah ta hanyar tuba ta gaskiya cikin dukkan lokutanka, abin da zai nuna gaskiya kuma shi ne barin sabonSa, da kuma nadama a kan abin da ya gabata na laifuffukanka da niyya kuma a kan ba za ka sake komawa ba ga aikata aikin zunubi nan gaba, hakika Allah Yana gafarta wa wanda ya tuba.
20. Ka yi azumi shida a watan Shawwal domin Annabi (SAW) ya ce wanda ya yi azumin watan Ramadan ya bi da guda shida za a ba shi ladar wanda ya shekara yana azumi.
-21. Ka yi azumin Ranar Arfa, wato ranar tara ga watan Zul-Hajji, domin wanda ya yi shi ana gafarta masa zunubin shekara biyu – shekarar da ta wuce da shekara mai zuwa.
22. Ka yi azumin Ranar Ashura, wato goma ga watan Muharram tare da Azumin Tasu’a wato tara ga Muharram, watan daya a Musulunci, domin in mutum ya yi ana gafarta masa zunubin shekara daya.
23. Ka ci gaba da imani da tsoron Allah da aiki na gari da nisantar duk wani mummunar aiki bayan Ramadan kamar yadda ka yi a Ramadan, domin Ubangijin Ramadan shi ne Ubangijin kowane wata, kuma ka ci gaba da tsare dokokin Allah har mutuwarka, domin Allah Ya ce, “Ka bauta wa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka.”
24. Ka bayyana alamomin ibada, ka yi Sallah tare da jama’a, ka yi kuma Zakka a sarari har ma ka tafi aikin Hajji, bayan haka ka bayyana tubarka ta hanyar barin miyagun al’adu da bidi’o’i da nesantar camfe-camfe da kuma nesantar shirka babba ko karama domin wadannan abubuwa ne da suka saba wa shari’a.
25. Ka yawaita salati da taslimi ga Annabi (SAW) da iyalansa da sahabbansa da mabiyansa baki daya.
A karshe, muna rokon Allah Ya sanya mu cikin wadanda suka yi azumin watan Ramadan da kuma
nafiifilin Ramadan- bisa imani da Allah da kyautatawa, muna rokonSa Ya gafarta mana abin da
muka aikata na laifuffukanmu da abin da muka jinkirtar. Allah Ka sanya mu cikin wadanda suka yi
azumin watan Ramadana da kuma alherin daren
LailatuI kadar, kuma ka sanya mu cikin wadanda suka rabauta da gafararKa, ya Mai girma da
daukaka, ya Ubangiji Kai ne Mai rangwame kuma Ka na son rangwame Ka yi mana rangwame, ya
Ubangiji! Ka amsa mana ayyukanmu, hakika Kai Mai ji ne Masani.Ya Rayayye, Tsayayye da kanSa,
Ya Ma’abucin daukaka da Girma.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi (SAW) da mutanen gidansa da sahabansa da sauran muminai baki daya.
Imam Ahmad Adam Kutubi
Za a iya tuntubarsa ta:
08036095723