Tukuici ga mai azumi (3)
Wadanda azumi bai wajaba a kansu ba, amma dole su biya:1. Matafiyi idan ya sha azumi a cikin tafiya dole ne ya biya.2. Mara lafiya yana iya shan azumi duk lokacin da ya warke sai ya biya abin da ya sha.3. Mai haila ba azumi a kanta, amma in ta yi tsarki za ta biya […]
Wadanda azumi bai wajaba a kansu ba, amma dole su biya:
1. Matafiyi idan ya sha azumi a cikin tafiya dole ne ya biya.
2. Mara lafiya yana iya shan azumi duk lokacin da ya warke sai ya biya abin da ya sha.
3. Mai haila ba azumi a kanta, amma in ta yi tsarki za ta biya abin da ta sha, kuma idan mai haila ta dauki azumi sai jini ya zo mata kafin rana ta fadi, to, azuminta ya baci, haka nan kuma idan haila ya dauke mata da rana a Ramadan ba azumi a kanta a sauran wannan yinin sai dai za ta rama azumin ranar da sauran kwanakin da ta sha. Bugu da kari idan jinin ya dauke kafin fitowar alfijir ko da mintuna kadan ne kafin fitowar alfijir, to, azumi ya wajaba a kanta.
karin bayani: Shi ma jinin haihuwa (biki) kamar jinin haila ne cikin dukkan hukunce-hukuncensa.
4. Mace mai shayarwa idan ta ji tsoron danta ba zai samu nonon da za ta shayar da shi ba, sai ta ci abinci, to, tana iya cin abincin bayan azumi ya wuce sai ta rama gwargwadon abin da ta sha. Haka hukuncin yake ga mace mai ciki idan ta ji tsoron abin da ke cikinta, ita ma tana iya shan azumi kuma wajibi ne a kanta ta biya gwargwadon azumin da ta sha bayan ta haife cikin nata.
5. Wanda wani dalili ya sa ya sha azumi kamar ya yi kokari don kubutar da wata rai da za ta halaka saboda gobara ko nutsewa a ruwa, sai wurin kokarin kubutar wadannan mutane ya sha azumi, to bayan azumin zai rama gwargwadon abin da ya sha.
Sahur da ladarsa:
Sahur shi ne cin abinci a karshen dare kafin fitowar alfijiri da niyyar ibada. Sahur Sunnah ne don
Annabi (SAW) ya ce: “Bambancin azuminmu da azumin Ma’abota Littafi, cin abincin sahur.” (Muslim ya ruwaito). Annabi (SAW) ya ce: “Ku yi Sahur hakika akwai albarka a cikin yin Sahur.” (Muslim ya ruwaito).
An samu Hadisi daga Sabit (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Mun yi Sahur da Annabi (SAW) sai ya tashi zai yi Sallah sai na tambaye shi, na ce ayoyi nawa mutum zai iya karantawa a tsakanin kiran Sallah da barin Sahur? Sai Annabi (SAW) ya ce: “Tsakanin kiran Sallah da barin Sahur mutum zai iya karanta ayoyi hamsin.” Buhari ya ruwaito.
Buda-Baki:
Abin da ake nufi da buda-baki shi ne mai azumi ya ci wani abu ko ya sha wani abu yayin da ya tabbatar da rana ta fadi, yin haka yana daga cikin abin da ake so don Annabi (SAW) ya ce: “Al’ummata ba za su gushe (cikin nasara) ba, matukar suna gaggauta buda-baki.” Buhari ya ruwaito Hadisin.
Imam DSP Ahmad Adam Kutubi, 08036095723