Tukunyar iskar gas ta jikkata mai juna biyu da ’ya’yanta 4 da ma’aurata
Akalla mutum 20 ne suka jikkata, ciki har da wata mace mai juna biyu da ’ya’yanta hudu da wasu ma’aurata bayan fashewar tukunyar iskar gas a garin Fatakwal
Akalla mutum 20 ne suka jikkata, ciki har da wata mace mai juna biyu da ’ya’yanta hudu da wasu ma’aurata bayan fashewar tukunyar iskar gas.
Lamarin ya faru ne a yankin Orazi da ke garin a Fatakwal, hedikwatar Jihar Ribas, inda aka garzaya da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal domin samun kulawa.
Wakilinmu ya gano cewa mutanen da tsautsayin ya rutsa da su har da mawkabta da masu wuceaw a lokacin da tukunyar iskar gas din ta yi bindiga ta farfasa gine-gine, lamarin da ya sa jama’a guje-gujen neman tsira.
Wakilin namu ya gano cewa tukunyar iskar gas din ta yi bindiga ne a wani shagon sayar da iskar gas a lokacin da wani ma’aikaci ke gyara wata tukunyar iskar gas da ta lalace.
- Mutum 4 sun mutu, bankuna sun ƙone a gobarar tankar mai
- Faɗa da Buratai: Matan ’yan Shi’a sun yi zanga-zanga a Kaduna
- NAJERIYA A YAU: Yadda ma’aikata za su daina jira kafin shigowar albashin watan Janairu
Tashin wuta daga tukunyar da ake gyaran ke da wuya, sai sauran da ke wurin suka tashi, inda aka yi ta samun bindiga da tarwatsewarsu tare da haddasa gobara.
Dan uwan iyalan da abin ya rutsa da su ya ce zuwa yanzu sun kashe sama da N500,000 a asibiti. Ya ce, “Kira na aka yi cewa dan uwana da matasarsa suna cikin wadanda abin ya rutsa da su.”
Mutumin wanda mazaunin unguwar ne ya ce mai sayar da iskar gas din ya jima yana gudanar da sana’ar a wajen.
Wani mazaunin wurin ya ce wata mace mai juna biyu da kimanin mutane 20 ne abin ya shafa a yankin.
Zuwa lokacin da muke kammala wannan labari dai ba mu iya samun kakakin ’yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko domin karin bayani ba.