Tukwicin zaben 2015: Mu gyara halayenmu (1)
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu. Bayan gaisuwa, Ina son in nuna, farin cikina ga ’yan Najeriya, da kuma jan hankalin masu karatu, kan cewar, wannan zaben da aka yi da kuma nasarar da aka samu, a ganina, ayoyi ne, da ya kamata a lura da su. Duk masu kaunar Janaral Muhammadu Buhari, hakika sun yi farin […]
Assalamu alaikum warahmatullahi wabarkatuhu. Bayan gaisuwa, Ina son in nuna, farin cikina ga ’yan Najeriya, da kuma jan hankalin masu karatu, kan cewar, wannan zaben da aka yi da kuma nasarar da aka samu, a ganina, ayoyi ne, da ya kamata a lura da su.
Duk masu kaunar Janaral Muhammadu Buhari, hakika sun yi farin ciki, da jin ya yi nasara ba sai an fada ba. Abin da ya kama ta mu yi, shi ne, mu tashi tsaye wajen yi musu addu’a, Allah ya taya su riko, ya kare su daga sharrin masharranta amin. Saboda kwalliya ta biya kudin sabulu. Irin wannan baiwa da Allah ya yi mana, ba karamin arziki ya yi mana ba. Sai mu kuma mu gyara halayenmu, da Musulmi da wanda ba Musulmi ba duka, don mu nuna wa Allah mun gode. Da yake wannan zamanin farir hula ne, ba kamar lokacin soja ba. Fatanmu, shi ne, Gwamnoni, Ministoci,da sauransu, su zama, m su tsoron Allah, masu kuma kishin kasa, kamar Janar din, ko za mu samu karin alkhairai daga wajen Allah. Fadar Allah da ya ce;
(“In kun gode, sai in kara muku,in kun butulce, lallai azabata mai tsanani ce’’).
Wani abin dubawa kuma shi ne, masu cewa duk wani dan takara da ba ya cikin jam’iyya mai mulki, ba zai yi nasara ba, kuma da, masu cewa talakawa ba su isa su kawo canji ba, sukan manta nasara daga Allah take. Ya kan bai wa wanda yake so, a kuma lokacin da yake so, shi ne kuma mamallakin dukkan masu mulki, Allah ya nuna musu lamarin ba haka yake ba, sei su kara imani, su san komai na Allah ne.
A nan ina rokon duk wanda Allah ya ba shi mukami, ya san Allah ne ya ba shi, tunda mun ga wannan karon kudi bai yi anfani ba, ballantana wani ya yi tunanin ce wa, kudinsa ne, yasa aka zabe shi. Su dage, su yi aikin kwarai. kuma a yi kokari a daina gaya wa abokan hamayya maganganun da ba dadi, don ba a san me zai faru a gaba ba, da kuma samun zaman lafiya da kuma hadin kai.
Aranar Asabar 28th ga watan Maris 2015 ‘yan Nijeriya, suka jefa kuri’a da zimmar Allah ya bai wa dan takararsu sa’a. Wasu sun kai karfe hudun dare kafin su jefa, amma ba su kosa ba, domin fatan samun nasara, Alhamdu lillah, Allah ya bai wa Janar nasara, da kuri’u miliyan (15,424,921). Mai bi masa kuma, shi ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan, mai kuri’u miliyan (12,853,162), sai kananan jam ’iyyu. Wannan shi ma ikon Allah ne, yadda ake yawan kukan ce wa, zabukan Najeriya a kullum, yana kunshe da murdiya, sai ga shi Allah ya yi ikonsa. Juriya da jama’a suka yi, da kuma fitowar da aka yi, ya biyo bayan irin halin kaka ni ka yi, da al’ummar kasa suka shiga ne, ta yadda ake yankan mutane, kamar dabbobi, ake kona garuruwan mutane, (wa’iyazu billah)].
Wata aya kuma, ita ce yadda kusan kashi 60% na ’yan Nijeriya suke son Janar ya zama Shugaban kasa, so na hakika ba na saye da kudi ba, sai kashi 25% su kuma suna dari-darin zaman shi Shugaban kasa, kada ya bincike su, a kuma daure su, sai kashin karshe, su kuma matsalarsu ita ce, kada na su ya bar mukamin da yake ne, daular da suke ciki ta kare, su tsiya ce, shi ne da muwarsu.
Wani abin dubawa kuma, shi ne,yadda amincewar da al’umma suka yi na cewa, shi mai gaskiya ne, mai kuma son abi doka, a kambama dukiyar al-umma, kuma a daina cin hanci da rashawa, dalilin haka ne ya sa kowa ya raja’a aka marawa mai girma Janar Buhari baya, saboda gani ake yi, kamar in ya hau komai zai gyaru. Allah ya tabbatar da haka amin.
Don haka addu’ata ga mutanen da suke neman mukamai don Allah a tsarkake zukata, a yi niyyar yi wa talakawa aiki, don ta ko’ina ana da bukatar aiyuka, ko Allah zai sa su cimma burinsu, na samun canji. A kuma sani cewa, amfani da na’urar tantance jama’a, wanda Farfesa Muhammadu Attahiru Jega ya yi, da ake kira (Card Reader) wacce na bai wa suna ‘yar amana, shi ne musabbabin kawo canji, don haka su ma u kuduri yin gaskiya da kuma rikon amana, addu’ar da nake yi, ba sai ‘yan APC nake yi wa ba, har da ma sauran jam’iyyun.
Masu burin iyalansu, idan sun hau za su mike kafa su shakata. Idan matansu,suka haihu,da sauransu,za su je a dunkula musu kudi, su yi hakuri, in har sun je ba a ba su komai ba,kada su yi fushi,ballantana ma, su fara zarginsu, su kuma taimaka musu da nasihar, kada su dauki kudin da ya fi karfin hakkinsu, da kuma bin doka da oda, shi ne ci gaban kasa, su sani wanda duk ya take doka, to, doka za ta kama shi, domin su samu su tsira da mutuncinsu.’Yan kasuwa da masu kudi suma su ba da, tasu gudummawa, su kakkafa masana’antu, domin kara, bunkasa kasa, don samun aiyukan yi, tunda anc e “Dambu in ya yi yawa ba ya jin mai’.’ Idan sun hada hannu da gwamnati, arzikinmu zai bunkasa.
Mu yi wa kanmu adalci, mu lura da cewa, duk wanda ya yi kudi na a zo a gani, burinsa ya je ya boye su a waje, sai kuma kokarin zuwa Dubai da Amerika da Engila da Indiya da dai sauransu,me zai hana mu ma, mu gyara tamu kasar, ‘yan kasar wajen, su yi sha’awar zuwa wajemmu. Me zai hana,kudin da suke boye wa a wajen,su sarrafa su a nan kasar, don mu bunkasa.Tunda suma mutanen su ne suke musu aikin,ba aljannu ko mala’iku ba, kuma su a kasarsu, kowa yana bin doka, babu cewa ni wane ne, ko dan wane, na fi karfin bin doka. Mu a Nijeriya, ko dan Kansila ma, ya isa ya karya doka ya kwana lafiya, mu cire son zuciya mu tabbatar da doka.
Za mu ci gaba in sha Allah!