Tun a sakandare na fara wasan kwaikwayo – Sani dan Gwari
Sani Ibrahim Tsiga wanda aka fi sani da dan Gwari, fitaccen dan wasan barkwanci ne da ke fitowa a fina-fanan Hausa, a hirar da ya yi da Aminiya a kwanakin baya, ya bayyana yadda ya fara wasan kwaikwayo da nasarorin da ya samu a harkar da kuma wasu daga cikin kalubalen da ya fuskanta: Tarihina […]

Sani Ibrahim Tsiga wanda aka fi sani da dan Gwari, fitaccen dan wasan barkwanci ne da ke fitowa a fina-fanan Hausa, a hirar da ya yi da Aminiya a kwanakin baya, ya bayyana yadda ya fara wasan kwaikwayo da nasarorin da ya samu a harkar da kuma wasu daga cikin kalubalen da ya fuskanta:
Tarihina a takaice
Assalamu alaikum. Sunana Sani Ibrahim Tsiga, wanda aka fi sani da dan Gwari. An haife ni a Sabon Gari, Tudun Wada, Kaduna a shekarar 1975. Mahaifina kuma mutumin Tsiga ne ta Jihar Katsina. Na yi makarantar firamare a garin Rigasa, daga nan ne kuma na wuce sakandare a garin Rigachikun.
Dalilin da ya sa na shiga harkar fim
Na fara ne da wasan dabe lokacin da nake makarantar sakandare. Na yi rawar koroso kafin na fara fitowa a shirye-shiryen NTA da na gidan Rediyon Najeriya na Kaduna irin su: ‘Gidan Kashe Ahu’ da kuma ‘Duniya Budurwar Wawa’. Daga nan ne kuma sai Allah Ya hada ni da Rabilu Musa (dan Ibro) wanda a yanzu muke harkokin fina-finan Hausa tare. Kafin haduwa ta da dan Ibro ina fitowa ne a wasa a matsayin dan Auta, amma ko da muka fara tafiya da shi, sai ya ce ba zai yiwu na ci gaba a haka ba. Saboda akwai wanda ke taka wannan matsayin, hakan ya sa na canza zuwa dan Gwari. Amma ban fara hakan da ka ba, saboda sai da na tuntubi jama’ar Gbagyi (Gwari) da na sani don sanin su waye gwarawa. Na fahimci al’adunsu da dabi’o’insu saboda na nishadantar da jama’a ba tare da na saba wa al’ummar Gbagyi ba.
Yawan fina-finan da na yi
A kalla ba za su kasa guda dari hudu ba. Sun hada da: ‘Ibro dan Ruwa’ da ‘Ka Girmi Sana’a ’ da ‘Rikita-Rikita’ da ‘Gwari-Gwari’ da ‘Waye barawo? ’ da “karangiya’ da Da’u’ da Babbar Yarinya’ dai sauransu.
Dalilin da ya sa a yanzu ba ma fitowa tare da Ibro
Idan ka ga haka to daya daga cikinmu ba ya gari ne, ko kuma marubucin labarin bai sa da shi ba cikin ’yan wasan fim din ba, saboda kowane labari yana da irin tsarinsa. Amma tsakanina da Ibro akwai kyakkyawar dangantaka, babu wani sabani. Hasali ma shi maigidana ne. Ya za ma dole na yaba masa saboda irin dimbin taimakon da ya ba ni wanda ya hada da na kudi da karfafa gwiwa a lokacin da na fara sana’ar fim.
kalubale
Ba a raba rayuwa da kalubale. Amma babban kalubalen da ni na fara fuskanta a rayuwata shi ne rasuwar iyayena a lokacin da nake makarantar sakandare.
Nasarorin da na samu
Alhamdulillahi, na samu ci gaba a sana’ar. Misali na yi aure kuma na gina gida. Na kuma ziyarci kasashen duniya da dama, wanda ciki har da kasar Sudan da Ghana da Togo da Ibory Coast da sauransu.
Burina
Ni ba ni da wani buri da ya wuce in cika da imani.
Iyali
Ina da mata daya da kuma ’ya’ya bakwai.