Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar
Faransa tana watsa “labaran ƙarya da haddasa husuma” da zummar ɓata sunan Nijar da shugabanninta a idanun duniya.
Firaministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine, yayin jawabinsa a Babban Taron MDD
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar shekaru tana haifar da rikice-rikice da rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel, tun daga shekarar 1899.
Firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, ne ya yi wannan furuci ranar Asabar yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na ƙasar Amurka.
- Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba
- Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara
Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da ɗukar alhakin laifukan da suka aikata” a Nijar tun daga shekarar 1899.
A cikin jawabinsa, Lamine Zeine ya zargi Faransa da amfani da ƙungiyoyin da ya kira “na ta’addanci” domin tayar da zaune-tsaye a ƙasarsa da maƙwabtanta na yankin Sahale, inda ya buƙaci mahukunta a Paris da su “tuna tare da ɗaukar alhakin laifukan da suka aikata” tun daga shekarar 1899.
“Tun lokacin da muka fatattaki sojojinsu daga [Nijar] a 2023, gwamnatin Faransa take kitsa wani shiri na ƙarƙashin ƙasa domin wargaza ƙasata,” in ji Ali Lamine Zeine.
Kazalika ya zargi Faransa da “bayar da horo da kuɗi da kuma makamai ga ’yan ta’adda” tare da yunƙurin haifar da “rikicin ƙabilanci” a Jamhuriyar Nijar da yankin Sahel.
Firaministan na Nijar ya ƙara da cewa mahukunta a Paris sun ƙaddamar da wata gwagwarmaya ta watsa “labaran ƙarya da haddasa husuma” da zummar ɓata ƙasarsa da shugabanninta da hukumominta a idon duniya.
Lamine Zeine ya shaida wa taron UNGA cewa Faransa tana rura wutar rikicin “siyasa tsakanin ƙasata da kuma wasu maƙotanmu,” inda ya ƙara da cewa Faransa tana hana Nijar aiwatar da muhimman ayyukan ci-gaba tare da hana hukumomin kuɗinta sakat.
“Wannan ya haɗa da ƙiyayyar da Faransa take nuna mana wajen aiwatar da ayyukan ci-gaba ta hanyar hana masu son zuba jari na ƙasashen duniya irin su ADB da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya a ƙasarmu,” in ji shi.
Tun dai bayan kifar da gwamnatin farar hula ta Mohammed Bazoum da sojoji suka yi a shekarar 2023, dangartakar diflomasiyya tsakanin Faransa da Nijar ke ci gaba da tsami.