Tun farkon daular Usumaniya aka kafa masarautar Akko – Sarkin Akko
Mai Martaba Sarkin Akko Alhaji Umar Muhammad Atiku, Sarkin Yanka ne mai daraja ta daya. A zantawarsa da Aminiya a fadarsa da ke garin Kumo, hedkwatar karamar hukumar Akko, ya bayyana takaitaccen tarihin masarautar, inda ya ce ta kafu ne tun a shekarar 1804 lokacin da Amada Gona da Bubayero suka yi karatu a wajen […]
Mai Martaba Sarkin Akko Alhaji Umar Muhammad Atiku, Sarkin Yanka ne mai daraja ta daya. A zantawarsa da Aminiya a fadarsa da ke garin Kumo, hedkwatar karamar hukumar Akko, ya bayyana takaitaccen tarihin masarautar, inda ya ce ta kafu ne tun a shekarar 1804 lokacin da Amada Gona da Bubayero suka yi karatu a wajen Shehu Usmanu danfodiyo suka karbo wa Gombe Tuta. Ga yadda hirar ta kasance.
Aminiya: Ranka dade ka bayyana mana takaitaccen tarihin kafuwar masarautar Akko da kuma yawan sarakunan da aka yi?
Gaskiya ba za a iya fadan yawansu da ka ba, amma dai masarautar Akko ta kafu ne tun a shekarar 1804 kuma lokaci daya aka kafa ta da duk wata masarauta ta Fulani da ke yankin arewacin Najeriya. Wadanda suka kafa masarautar Fulani ne da suka zo shekaru masu yawa da suka wuce daga kasar Mali da Senegal, a lokacin ana kiransu Ardabai wato Ardo Ardo, har suka kai ga kama kasashe ta hanyar yakarsu. A wancan lokacin wanda yake shugabantar bangaren Fulani na mu ne na nan Gona, ana kiransa Amada Gona. Tare da Bubayero suka je suka yi karatu a wajen Shehu Usamnu danfodiyo. To shi Amada Gona tarihi ya nuna cewa Shehu ya yi masa tayin Tuta kamar yadda ya bai wa Bubayero sai ya ce a, a, wanda aka bai wa Bubayero ta ishe su dukansu. Bayan sun dawo, Amada Gona su ne Fulanin wannan kasar Bubayero kuma Fulanin kasar Sheleng ne a Fetambere. Da Bubayero ya wuce kasar su bai samu karbuwa a wajen ‘yan uwansa ba sai ya dawo nan ya sake haduwa da shi Amada Gona da sauran Fulanin da suke nan aka yi yaki aka kafa daula, da yake lokacin ya samu dattawa ne sai suka ce shi Bubayero din ya Shugabance su a matsayin Sarki na farko a daular Usmaniya a masarautar Gombe, ana tafe a haka, har shekara ta 2001 lokacin da aka fasa masarautar Gombe aka kirkiro da karin masarautu guda bakwai da suka hada da masarautar Akko da Dukku da Deba da Yamaltu, a lokacin akwai Jara wanda yanzu babu ita an rushe ta akwai Nafada da Funakaye daga baya a shekara ta 2007 aka yi canje-canje wajen daga darajojinsu daga masu daraja ta 2 zuwa masu daraja ta 1. Har ila yau ana tafe har aka sake kirkiro da wasu masarautu. Kuma daga masarautar Akko aka cire Gona da Pindiga, hakan kuma ya biyo bayan yawan jama’a ne da suke karuwa a lokacin. Daga kirkiro masarautar Akko zuwa yanzu anyi manyan sarakuna guda 2 na daya ya fara daga shekara ta 2001 zuwa 2004 wanda a lokacin ne na karbe shi har zuwa yanzu. A tarihi, zuwa yanzu sarakunan da aka yi za su kai goma 18. Amm a da suna matsayin Galadima ne wato Hakimai ne da suke karkashin masarautar Gombe har zuwa 2000. Abin da ya biyo baya daga shekarar 1804 ma akwai jerin sarakuna na wannan masarauta ta Akko da suke karkashin Fulanin Gona su ma za su kai fiye da goma. Idan aka hada duka a wannan masarautar, anyi sarakuna tsakanin daga 30 zuwa 40.
Aminiya: Hakan ya nuna mana cewa wannan masarauta mayaka ne. Za mu iya cewa ba a taba cin Akko da yaki ba kenan?
Ah! Lailai babu batun cin Akko da yaki. Wannan bai zo a tarihi ba, sai dai wuraren da suka zamo a karkashin wannan masarauta domin lokacin da Akko take Akkon ta yi iyaka ta Gabas da masarautar Waja, a Arewa kuma tana iyaka da Dukku domin ta wuce Gombe. Inda Gombe take a yanzu Akko ne ta bai wa Sarkin Gombe don ayi hedkwatar Gombe a wajen, ta yamma kuma Akko ta kai har kusa da Dindima na kasar Bauchi sannan irin su Deba da Dadin-kowa duka suna karkashin masarautar Akko ne, haka Pindiga ma tana karkashin Akko a wancan lokacin babu batun Tangale a lokacin duka suna karkashin Akko ne, ba za dai a rasa ‘yan hare-hare ba, amma babu wadanda suka yi tasiri a ciki don ko yake-yake da aka yi lokacin zuwan Turawa ita Akko ba ta tabu ba sosai, akwai wani yaki da aka kawo daga Nbormi wani mutum daga garin Misau suka zo suka kawo hari a Akko lokacin hedkwata tana can Akko kuma akwai mazauni mai karfi a garin Tukulma wadanda duka na Fulanin Gona ne, wadannan runduna ta zo aka samu hadin baki da masarautar Gombe a kan sai aje a yaki Akko, amma anyi watanni ana kewaye da Tukulma amma haka aka hakura ba a samu nasara ba. Wadanda suka kawo harin haka suka koma inda suka fito, daga nan sai aka samu ci gaba da zaman lafiya a lokacin da take da karfin ta babu wanda ya isa ma ya tunkare ta da yaki, don masarautar Gombe ma a lokacin Galadiman Akko shi yake nada sarki kuma idan aka nada wanda bai masa ba yana iya sauke shi yasa wanda yake so. Tarihi ya nuna an taba yin hakan. Saboda Allah Ya azurta su da jarumai horarru a bangaren yaki ga dawakai da kuma sanin yadda ake sarrafa karfe.
Aminiya: Menene bukukuwan tarihi na al’ada na masarautar Akko bayan hawan Dawakai?
Kasancewar musulunci ya jima a Masarautar Akko, hakan yasa an jima da kawar da duk wasu wasanni na al’ada wanda musulunci bai koyar da su ba. Ba mu da wani wasan al’ada da ya wuce wasan hawan dawakai na sallah karama da babbar Sallah na hawan Sallah da hawan Daushe sai kuma bukukuwan aure. Bayan su bamu da wasu bukukuwa da muka bari ya shige mana ido wanda ya saba wa addini.