Tun ina dan shekara 13 na fara waka – dahiru Musa Jahun
“An ce da danka dan iska,To Baba ka zame iska, Ba ka koya wa danka tarbiyya. ***Sunana dahirun Musa,In kun kira ni zan amsa,Wani almajiri marar murya.” Malam dahiru Musa Jahun ke nan a daya daga cikin fitattun wakokinsa na gyaran tarbiyya da suka yi amo a shekarun 1980 lokacin da gwamnatin soji ta Manjo […]
“An ce da danka dan iska,
To Baba ka zame iska,
Ba ka koya wa danka tarbiyya.
***
Sunana dahirun Musa,
In kun kira ni zan amsa,
Wani almajiri marar murya.”
Malam dahiru Musa Jahun ke nan a daya daga cikin fitattun wakokinsa na gyaran tarbiyya da suka yi amo a shekarun 1980 lokacin da gwamnatin soji ta Manjo Janar Muhammadu Buhari ta kaddamar da shirin yaki da rashin tarbiyya. A tattaunawarsa da wakilinmu a gidansa da ke Unguwar Jahun a garin Bauchi, mawakin ya bayyana abin da ya sanya shi sha’awar waka duk da cewa ya fito ne daga gidan ilimi da sarauta, kuma ya bayyana wasu al’amura da suka shafi rayuwarsa:
Da farko za mu so ka gabatar mana da kanka?
Alhamdulillah,sunana dahiru Musa Jahun, sunan mahaifina Musa dan Hamidu. Ni mutumin Bauchi ne an haife ni a Unguwar Jahun a garin Bauchi kimanin shekara 73 da suka gabata. Na tashi a gaba yayyena domin mahaifina ban gan ni ba, saboda ya yi tafiya sai ya aiko a sanya min suna Muhammadu dahiru ba ya jin zai gan ni. Shi ke nan sai ya rasu ma kafin a yi min suna, sai aka aiko ya rasu, sai aka sanya min suna Muhammadu dahiru.
Yaya maganar karatu?
To, sai aka yi sa’a da kuma rashin sa’a duka. Wato sa’ar da aka yi, su yayyena almajirai ne, akwai Malam Muhammadu Inuwa, Babban Limamin Bauchi wanda ya rasu, shi ne babban wanmu. Tun muna yara bai yi sake da mu ba, ya tura mu makarantar addini dukkanmu mu kannensa.Kuma a karshe ya girma ya zo ya kafa makaranta, muka zo muna karatu a wurinsa. To, karatunmu gefe daya ne, kusan dukkanmu ba mu samu mun yi karatun boko bakusan in ce dukkanmu. Sai daizaka ganmu da bokon saboda Allah Ya yi mana kwakwalwar gane irin wadannan abubuwa. Kuma saboda son bokon ne na taba sanya kaina a makaranta amma aka ciro ni. Lokacin ina kamar dan shekara tara zuwa 10, lokacin ina tare da mahaifiyata a gidan da ta yi aure a gidan wani dattijo ana ce da shi Malam Fate Maidori. Muna zaune a gabansa aka bude makarantar firamare ta Unguwar Borno, sai ina jin sha’awa ina ganin abokaina wasu an sanya su, to a karshe sai na shigar da kaina. Na yi kamar mako daya ina zuwa sai aka ce shin ina nake zuwa, sai aka gano aka ce to in fita. Aka je aka cire ni saboda tsoron kada a ce don ba shi ya haife ni ba ya sa aka sanya ni a boko, tunda ya ga yayyena ba su yi ba. Shi ke nan aka cire ni ina da haushin haka. Na yi ta zama rayuwa irin ta yadda hali ya kama. To har muka zama samari, shekara 11 zuwa 13 na iya rubutun Arabiyya ina yi sosai saboda yayyena ba sa yi da wasa, har ta kai ina yagar takarda ina rubuce-rubuce.
Na fara rubuta wakokin Hausa tun ina da shekara 13, a lokacin tunda ni yaro ne matasa da ’yan mata da suke kusa sai a taru a cikin gida ina yi ana ji. To tun a nan abin ya rika shiga jikina, kuma sha’awar waka ta shiga raina ne saboda masu bara a lokacin idan kowa ya zo bara za ka samu wake yake yi, makaho ko kuturu ko masu bara idan suka zo suna yin bara suna wake a gidanmu ko a wani gida sai in yi ta bin su, har sai sun yi nisa a kira ni in dawo. Kuma duk abin da suka wake, sai in zo ina yi.
Mutane sun dauka ko albarkacin makarantar Islamiyya ne ka fara waken, ga shi ka ce daga gida ne. Shin ba ka taba makarantar Islamiyyar ba ne?
Na taba, kamar yadda na ce maka galibi karatun addini na yi, Islamiyyar ma na zo na kafa ta ce, sai na fahimci cewa yara da ’yan mata sun fi gane karatu ne ta hanyar wake, to sai in dauki babi guda in rera a wake. Babin da za ka yi fama da su a wata kana ta koya musu, idan na juya shi na mayar da shi ta hanyar wake a cikin kwana uku sai su haddace. Sanadin da wakokina suka fito ta hanyar Islamiyyya ke nan, amma da wakena na isa Islamiyya. Sai da na kai wajen shekara 30 ne muka kafa makarantar Islamiyya ta Nurul Islam wadda ita ce ta hudu a garin Bauchi, muna ganin abin da suke yi sai muka yi shawara cewa don me za a zo ana kidan kalangu a unguwarmu? To a dakina aka yi shawarar yadda za a yi ta kafa Islamiyyar. Na jagorancin kafawa, sai aka ga abin na ci gaba saboda waken nan da nake jejjefawa a ciki ya sa wa Islamiyyar farin jini sosai. Ni kuma fahimtata a lokacin komai wahalar da za ka sha a darasi in za ka sha shi a cikin wake, yara za su fi saurin ganewa haka mata.To dalili ke nan da na rika sassaka wakoki a karatun Islamiyya, daga nan kuma na zama mai wakokin ma.Rubutawakokin yana kaina ne, idan na dade ban rubuta wake ba, sai inji abin ba ya min dadi. Lokacin da nake yaro idan ana karatu sai in ji anacewa littafin da ake karantawa Basamawi, a wa’azi ana fada, sai na dauka duk abin da za a karanta shi ma an sako shi ne, to sai na dauki abin da karfi. A lokacin malama lokacin in dai za a yi wani abu kamar daren Sallah ko wani muhimmin abin da za a yi in dai da malamai, to ba wa’azi za a yi, a dauki littafi ana fassara ba, a’a za a samu wani gwanin wake ne wanda zai zo ya yi wake irin na su Shugabanmu Shehu Usman dan Fodiyo da sauran wakoki na addini. Su za a zo a kwana ana yi, mutane kuma ba su gajiya, ni kuma sai in yi ta dauka. Sai ya zama ina cewa can da aka ce kaza da a sa kaza mana, amma tunda littafi ne da aka sauko da shi ba gyara. Da na fara girma sai na fara ganewa a karshen waken ana cewa wane ne ya yi. Sai na fara cewa wanen Annabi ne sai a ce a’a malami ne, to fahimtar cewa wane ne ya yi, sai na gane cewa ashemutum zai iya yi. To a lokacin sai na rika daukar waken ina sa abubuwan da nake so.
To cikin sauri sai na fara iya karanta rubutun boko, tunda ina da sha’awa, akwai wani littafi na Hamisu Yadudu a lokacin nakan karanta. To a ciki sai in ga Hamisu Yadudu kuma da boko aka yi, sai in ce a wuri kaza da kyansa a sa kaza, to sai in na yi nawa sai in sa kaza din, sai in rika wakewa. Mutane suka shiga taruwa suna saurara ta.Sai kuma wannan ya kawo mu wani lokaci na wayewa da ake yi a shekara inda ’yan matan unguwa sukan taru su nada Sarkin Musulmi da Sarkin Kano da Sarkin Zazzau da Sarkin Nupe da Sarkin Bauchi da na Gombe da sauran sarakuna, sai a nemi wani wuri a yi fitar sarauta. Na wannan unguwa suna yi, na waccan unguwa su ma suna yi, su yi ado irin na maza a kwana uku ana yi musu bikin sarauta. To da wannan dalili sai na samu waken Mu’azu Hadeja da ya yi a kan sarakunan Arewa, ya fara daga Sarkin Musulmi zuwa kasa, sai ni ma na debi wadannan wakoki na juya na yi wa wadannan sarakuna na ’yan mata. Wannan sai ya jawo min farin jinin mutane, suna son in zo in wake wannan biki, sai ya dada karfafa min gwiwa saboda na ga jama’a suna so.
Da aka ci gaba, sai na fara gane ai ma in kana so ka isar da sako a gane da wuri an fi saurin ganewa in ka sa ta hanyar wake. Idan ka yi waka sau daya aka ji, koda ka yi shiru, zaka ji jama’a na ta maimaitawa, ya fi mutum ya yi magana haka kawai.Sai hakan yana kara min son yi wakar, tunda ba sai babban malami ko wani sahabi zai yi ba, in kana da tunani mai kyau ka rubuta jama’a su ji dadi za ka iya. To shi wannan ya sa na ji cewa ina son in yi magana da mutane, amma ni ba babban malami ba, ni ba sarki ba, sai na ga haka hanya ce ta isar da sako sai na kara sha’awar wakar.
Za ka iya tuno wata fitacciyar waka da ka rubuta a lokacin da kuka bude makarantar Islamiyyar?
Eh, akwai wasu wakoki a lokacin, kamar wakar nan mai cewa:
“Ni dai na ce bismillahi,
Rahamu rahimun lillahi,
Ka jikanmu a ran tashi kabari.”
Sai yara su amsa da:
“Allah Sarki, Allah Akbar,
Allah a gare ka muke zikiri.”
To a wannan waka na sanya farillan tsarki da na alwala da farillan Sallah. Wakar tana nan a cikin kayayyakina.
Sai kuma wakar:
“Ta’ala ka sa mu cikin muminanka,
Ka samu cikin mabiya Annabi.”
Amsarta kuma ana ce:
“A ya ’yan uwana mu yaki kasala,
Mu yaki juhala mu so Annabi.”
A cikin wannan waka, sai na sa aikin Hajji na sa azumi, sannan na yi wa yara yadda za su haddace sunayen surorin Alkur’ani daga Bakara zuwa Nasi, domin a tsakiyar wakar sai ina cewa ina rokon Ta’ala Ka jikanmu albarkacin Suratul Bakara, Ta’ala Ka jikanmu albarkacin Suratu Ali Imrana, Ta’ala Ka ba mu ganin Annabi haka na bi surori daidai har zuwa Nasi.Idan yaro ya haddace wakar in ka tambaye shi sunan surorin sai ya fada maka.
Na taba zama dan kwangila, kwangilar kuma ta karbe ni sosai, har an fara ba ni aiki, har da aikin gina hanya. To a aikin hanyar ne ma lokacin muna tsohuwar Jihar Arewa maso Gabas na bar kwangilar. Domin an ba ni aikin hanya da bishiyoyi kamar guda 50 a kan hanyar aka ce zan sassare su kuma zan yi magudanar ruwa gefe da gefe hanya ta fita. Hanyar tana nan daga kofar Barayan Bauchi ta fada ta yi ’Yan Doka ta bi Night Club, ni na yi wannan hanya. Sai aka yi kowace bishiya zan sare ta a kan ko sule 12 ne na manta dai yawan kudin, amma na fi karfafa sule 12. Sare bishiyoyin yana daga cikin kwangilana, sai aka zo aka kirga bishiyoyin Baturen hanya ya zo ya gani ya ce ya yi kyau, ya ce haka kake kwangilarka na ce haka nake yi. Ya ce haka kake yi na ce ranka ya dade ya yi kyau fa. Ya ce ina zuwa, sai na ga ya zo da leburori, sai a raba tarin itatuwan bishiyoyin wata bishiyar a raba ta waje uku, wata biyu, wata a raba ta hudu ma idan babba ce. Sai bishiyoyi suka zama dari da wani abu, ina kallonsu. Sai ya ce kawo takardarka na kawo sai ya rubuta a ciki ya ce bishiyoyi guda kaza ne ya sa hannu ya ce gobe ka zo ka karbi kudinka. Wannan sai ya sa na ji ba na son yi, kuma in haka ake kwangila to na fasa. Na dauki satifiket dina na dauki hotonsa sai na yaga gangariyar na ce na bar kwangilar. Na ce za a bata ni, shi kuwa har ya je ya yi boca ya fito da tsabar kudin an ninka min ninki uku, na dauki kudin nan na rika kyamar kudin nan daga baya na biya kudin zuwa aikin Hajji Naira 1,700 kudin kujera da guzuri, na sayi wata mota Naira 400, motar da ita nake zuwa Kano da ko’ina, na zo na gina wani daki.
Bayan na tafi Saudiyya (aikin Hajji) sai na rika rokon Allah cewa Ya ba ni wata sana’a na bar kwangila, sai na ji ina sha’awar waka. Na ga cewa na girma yanzu in je in ce ina so a koya min sana’a, tunda jama’a suna son waken nan bari in ci gaba da ita. Sai na dawo na mayar da hankali a kan Islamiyya da waken nan.
Za mu ci gaba