Tun ina dan shekara 13 na fara waka – dahiru Musa Jahun (2)

Abin ya dada buduwa lokacin siyasa, na so mutanen NPN su kira ni ba su kira ni ba, ni kuma na san ina waka ya kamata a kira ni. To sai mutanen NPP suka neme ni, wadda a karshe ta zama GNPP, wadda ina cikin wadanda suka rubuta GNPP din, sai na bi su. Aka […]

Tun ina dan shekara 13 na fara waka – dahiru Musa Jahun (2)
Tun ina dan shekara 13 na fara waka – dahiru Musa Jahun (2)

Abin ya dada buduwa lokacin siyasa, na so mutanen NPN su kira ni ba su kira ni ba, ni kuma na san ina waka ya kamata a kira ni. To sai mutanen NPP suka neme ni, wadda a karshe ta zama GNPP, wadda ina cikin wadanda suka rubuta GNPP din, sai na bi su. Aka ba ni shugaban reshen Jahun daga nan aka maishe ni Sakatare na karamar Hukumar Bauchi daga nan aka ba ni Sakataren Wasta Labarai na Jihar Bauchi. Daga nan sai Alhaji Waziri Ibrahim ya gan mu ya ce ya kwace wannan, dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi ka nemi wani maim aka (waka) ni na kwace wannan na mayar da shi na kasa. To a lokacin da zan tafi din nan, shi ne na yi wa dalibai wata waka mai tsayi wadda ita ce jama’a suka fi sani mai cewa:

“Wasu na ce kansu ya waye,
Bari kWaryar kanka ya waye,
Matukar ba ka san ibada ba.”   

A karshen wakar akwai inda nake cewa:

Ya Rabbu Ubangijin Lauhu,
Allah don Mursali Nuhu,
Domin Sayyidina Shehu,
Ya Rabbul Arshi, Allahu
Ka nufe mu ba za mu tabe ba.

Jama’a na roki kui hakuri,
Mai jahilci yana tsari,
Kada dai rigima ta ja hadari,
Yara kui nai wa alkawari,
Na san ba za ku mance ba.
     
To a cikin wannan waka na tsara ta da tsayi, na tsara wa yaran abubuwa daki-daki da nake jin har za mu je siyasar mu dawo suna da abin da za su rika yi. Domin na ce ’yan aji bakwai su koyar wa ’yan aji shida, ’yan aji shida su koyar wa ’yan aji biyar har zuwa kasa. Sai na ba su jagora cewa ga yadda za su yi, na ce dama kuna da abubuwan da za ku yi amma kuma ga wadannan wakoki za ku dade kuna yi kafin in dawo. To sanadin wakar “Wasu na ce kansu ya waye ke nan.”
Lokacin da aka samu Jihar Bauchi aka samu rediyo sai suka rika neman wanda zai rika yi musu wake, idan aka zo sai a ce ana son wanda zai rika yi musu waken addinin Musulunci za a yi kamar karfe shida na safe ko kamar karfe uku saura kaza a kowace rana, sai ya zamo zn je wajen ne a ce za a saurari wakan Musulunci tare da wane, haka kawai, in ma katobara ce babu wani mai tare ka, sai in kama in yi ta yi, in lokacin ya kare a ce in tsaya haka. Sai a ce kun saurari dahiru Musa Jahun ya yi wake, gaba da gaba ake yi lokacin. Ban san yawan wakokina ba, kuma ina wake da Hausa za ku ji an cire amshi a wakokina, to sanadin haka shi ne na taba zama shugaban masu waken Ishiriniya, shi ma lokaci ne na tasowa. Nan unguwar ni ne shugaba a shekara a hadu a yi tare sai aka zo ni ne ma shugabansu. Tunda ina da wannan ra’ayi na wake Ishiriniya tana da salo-salo 30, to sai a raina na shirya murya talatin idan ina karatun Ishiriya ina zuwa wani bangaren sai in canja wata muryar. Kuma zan iya murya talatin din ban tsaya ba. To sai ya zamo duk masu karatun Ishiriniyar suka hadu suka ce ni ne shugabansu. To a nan unguwar ina da wakili wanda in ba ni nan shi ne yake bayar da waken. Shi ne Malam Ibrahim Idris, Babban Limamin Izala na Bauchi. To muna tafiya kungiyar ta yi karfi, muna da makunshin hotuna (album) da muke yi wadansu sun zama malamai, wasu sun rasu. To ana cikin haka sai aka kira wani babban taro na karatun Ishiriniya, ni kuma ina da wani karatun Ishiriniyar da ake son muryata ni kadai a wani gida za a dauka. Sai na tafi can na ce in na gama zan same su. Da na gama na dawo sai na samu wakilin nawa bai je ba, wani ne ya je. Na karba na ci gaba da ja. Daga baya muka kira shi to da ma akwai tara sai muka yi masa tara ya biya, aka sake sai ya sake kin zuwa. Muka kira shi muka ce wakili ba ka son zuwa, to za mu rage karfinka. Sai ya ce shi fa wannan abu bidi’a ne “Ni ba zan rika zuwa ba,” inji Malam Ibrahim Idris. Sai muka rika tambayar kanmu yaya aka yi haka. Ashe ta kasa-kasa ya shiga wata kungiya, wato farkon fitowar Izala ke nan. Na hado maka wannan labari ne don daidaita sahun yadda za a yi ka gane yaya aka yi na zama shararren mawallafin wakokin Hausa ni kadai. Daga lokacin sai na ce tunda haka ne da yara masu amshin Hausa da masu na Ishiriniya daga yau duk na fasa. Domin in kana yin abu da wani, ranar da wanin ya ce ba zai yi ba, kai ma sai ka tsaya. Daga yanzu ni kadai zan rika yin abina, to yadda aka yi ke nan na fara wake ni kadai ba ni bukatar amshi, ba ni bukatar taimakawa don kada ka ki yi in tsaya.
To, sai aka= fara gayyata ta a hukuma lokacin mulkin soja Gwamna Sani Sami, da ina zuwa hukumar kadan-kadan ne, sai ya zamo da Buhari ya kama mulki aka ce yaki da rashin da’a. Ni kuma ina da wannan ra’ayi, ina so inji inda za a yi yaki da rashin kirki, komai wahala zan iya daurewa kuma koda yaya sai in ka ce min in bari. Muka ce shi ke nan, su suna ganin kamar ina yi musu aiki, ni ina ganin suna yi min aiki, domin an ce in zo in fadi gaskiya. Sai muka kama wakar tarbiyya, to wannan shi ne jama’a suka fi sanina da ita, saboda lokacin rediyo ya isa kusan ko’ina, kuma galibin taron da gayyatar na gwamnati ne ana watsa abin yana tafiya nesa. To shi ke nan na ci gaba da wakokin Tarbiyya na yi babi-babi har 14 daban-daban. Aka zo aka kawar da wannan mulki, wani ya hau shugabancin kasa ya junya nasa ya ce Mamsa ban yi sosai ba ni da sha’awar wannan.

Kamar yadda ka fada wakar Tarbiyya aka fi saninka da ita tunda ta yadu a Najeriya, ko ta s aka mori wani abu ta bangaren gwamnatin?
Wannan babbar magana ce, abin da zan ce na mora ta bangaren gwamnati alhamdulillahi, zai zamo na fito gaban mutane, masu jina sun gan ni cewa wancan shi ne dahiru Musa mai wake, na mori wannan. Kuma na samu wasu abubuwa a tara jama’a a yi biki a dauki ’yar tutar gwamnati ko wata lamba a ba ni a ce an gode min ga su nan fiye da goma. Amma a ce bari a yi min wani alheri saboda na yi wannan wake ban samu ba. Wannan ya sa ina taka-tsantsan, saboda duk da Buhari ya dawo mulki kuma ina da sha’awa, abin da ba a kira ka ba, sai ka yi taka-tsantsan. Yanzu haka sai ka ji mutane suna ce min me ya sa ba ka yi kaza ba, sai in ce zan yi.

Kana nufin gwamnatoci sun dauka sha’awa ce ta sanya ku wakar ba su dauki abin da kuke yi a matsayin sana’a ba balle su tallafa muku?
Ni dai ban samu wani abu da aka ce ga shi an ba ni saboda na yi kokari. Sai dai Obasanjo a mulkinsa na biyu an bugo a jarida cewa in zo ina cikin wadanda za a ba su lambar girmamawa ta kasa a Abuja. To wannan lamba a wajen gwamnati ko a wajenku ’yan takarda abin burgewa ne, amma mu da taimakon kudi shi ne wani abu. Sai a zamanin Abacha wata mata ta zo da mota ta ce kai ne dahiru Musa Jahun na ce eh. Ta ce daga Abuja take an turo ta ce ta bi duk inda aka aika sako a tabbatar ya sadu da mutum. Shin an kawo maka wani sako daga Abuja wurin Shugaban kasa? Na ce, a’a ba a akwo min ba. Ta ce, ba a kawo maka ba? Na ce ba a kawo ba. Ta ce yanzu baa bin da aka kawo maka ko mota ko wani abu ba. Na ce ba a kawo ba. Ta rubuta sunana da adireshina da lambar wayata. Ke nan an taba ba ni, ni ne ban gani ba. To tunda aka kama daya, watakila an bab ba ni. Haka na ci gaba ko a nan baya-bayan nan an kira nin ofishin Alhaji Atiku Abubakar aka ce in yi waka kan sayar da hannun jari a nan bangaren Arewa, to ganin ba a tallafawa a baya, sai aka zo fagen nawa za a ban. A ce za a ban kaza, sai a biya ni, domin na san wannan ko akwai lada a wurin Allah ladan ba yawa, saboda sakon nasu ne. Amma kamar na tarbiyya din nan shi ba ni ma bukatar a biya ni saboda ina ganinsa kamar addini ne.

Ko akwai wata makaranta ko jami’a da ta karrama ka saboda gudunmawar da ka bayar wajen bunkasa Hausa da adabin Hausa?
An sha kiranmu taro na marubuta wakokin Hausa kafin yaran nan masu kade-kade su fito. Amma tunda suka fito namu wakokin na tsabar Hausa ban ji suna yawan motsawa ba. Munt aba taro a Sakkwato da Daura da wurare da dama na mawaka. Kuma Jami’ar Bayero ta taba gayyata ta takardar har yanzu tana nan. Tun su Dokta Shehu Umar Abdullahi da Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya suna da rai. Na je sai aka ce muna son ka yi mana rikodin ka zo da wakoki na ce na zo da su da dan dama. karfe 8:00 na safe muka fara a sutudiyo dinsu muka karfe 2:00 suka ce sun kare na ce ba su kare ba, washegari haka sai mai daukar ya ce kai tuntuni kana ina ne? Na ce ina Bauchi, sai da muka yi wuni hudu muna dauka. To wannan na sa ran bayan na dawo a ce sun aiko min wata takarda ta cewa an ga wani abu na yabo. Watakila sun ga ban yi daidai ba sun ga abin tankadewa Hausar ba ta yi yadda suke so ba. Mai daukar duk wakar da na yi sai ya karbi takardar ya yi kwafenta ya ajiye. Sun ce ba su samu wanda ya yi kwana da kwanaki yana karanta wake kullum sabuwa ya yi kwana hudu bai kare ba, sai a kaina. A hakan na dawo da wasu wakokin kuma akwai wadanda ban je da su ba. dalibai masu zuwa su rubuta takardar shaidar kammala karatu a kaina suna da yawa daga jami’o’i da kwalejoji da sauransu, har na sanya musu doka cewa duk wanda ya rubuta kundinsa a kaina sai ya ba ni kwafe, ga wasu can.   

Me ya fi ba ka takaici a harkar waka?
Babban abin da yafi ba ni takaici shi ne yadda aka rasa wanda zai dauki nauyin buga wakokina a matsayin littafi. Na yi bakin kokarina domin a buga wakokin a littafi, na bi mutane har na gaji ba tare da na samu nasara ba. Yanzu haka ga jibgin wasu wakokin can a dirowa kundi-kundi a ajiye.
Na biyu lokacin da Obasanjo ya karrama ni da lambar yabo ta kasa, marigayi Sarkin Bauchi Alhaji Sulaiman Adamu ya jinjina min ya dauke zuwa Gidan Gwamna aka nuna wa Gwamna Ahmadu Mu’azu, Sarki ya ce wannan abin alfahari ne mu mutanen Bauchi da ake cewa ba mu iya Hausa a ce danmu ya samu lambar yabo ta kasa saboda harshen Hausa. Amma abin bakin ciki sai Gwamna Mu’azu a gaban mutane ya ce, na yi kokari, amma shi ba ya kaunata. Ina ganin tunaninsa ina siyasa amma ba na cikin jam’iyyarsa a lokacin, saboda mun taba yin siyasar jam’iyya da shi, alhali ni kuma ba na siyasa a lokacin. Kuma bai tambaya ba ya yanke wannan hukunci har wani jami’in gwamnatinsa ya ce in tambaye shi laifin me na yi masa amma na ce a’a.          

Yaya batun iyali?
To, ban yi aure da wuri ba, sai da na kai shekara 31, kuma ban samu haihuwa da wuri ba, har matata ta farko ta fita bisa rashin haihuwar. Amma na haihu sau 51, yanzu haka ina da ’ya’ya 42 masu rai, kuma ina da mata hudu.