‘Tun ina firamare nake zane-zane’
Idris Adam Zubair matashi ne da Allah Ya ba shi baiwar zane-zane na kirkira inda yake iya zana duk abin da yake son kirkira, wato samar da abin da babu shi ta hanyar kirkira. Aminiya ta zanta da shi a garin Kafanchan inda ya bayyana lokacin da ya fara zanen da kalubalen da yake fuskanta […]
Idris Adam Zubair matashi ne da Allah Ya ba shi baiwar zane-zane na kirkira inda yake iya zana duk abin da yake son kirkira, wato samar da abin da babu shi ta hanyar kirkira. Aminiya ta zanta da shi a garin Kafanchan inda ya bayyana lokacin da ya fara zanen da kalubalen da yake fuskanta da burinsa a sana’ar.
Mene ne tarihinka a takaice?
Sunana Idris Adam Zubair. An haife ni a Layin Kano a garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna. Shekaruna za su kai 20, a yanzu haka ina makarantar sakandare.
Wane lokaci ka fara wannan sana’a ta zane-zane kuma me ya ja ra’ayinka a kai?
Na fara aikin zane-zane ne tun ina karami lokacin ina makarantar firamare. Kuma sha’awa ce ta ja ra’ayina ba komai ba. Ina sha’awar in ga mutum yana zane-zane musamman na kirkira. Ban taba zama ko zuwa wurin wani na koyi aikin nan ba, daga sha’awa kawai sai na nemi fensir da abin share rubutu (kilina) ina gwada kuma idan na ga wani na yi sai in tsaya in kalla, idan na koma gida sai in gwada da haka na taso. Ina sha’awar zuwa koyon aikin amma mahaifiyata takan hana ni domin a lokacin sana’ar dinki take so in koya saboda ana ganin zane-zanen kamar ba wani abu ba ne. To yadda nake yi idan na je shagon dinki na dawo sai in zauna a daki in yi ta famar yin duk abubuwan da suka fado a raina.
Me da me kake zanawa?
Na fi zana abubuwa na kirkira kamar in samar da wani gari ko birni ko kauye da duk abin da ke ciki da kewayen birnin ko kauyen. Hakazalika hoton mutum ko wani abu da za ka kawo in gan shi to zan zana maka shi.
Yanzu mene ne babban burinka a wannan sana’a?
Gaskiya babban burina shi ne Allah Ya daukaka ni har in zamo wanda ake ji da shi a wannan sana’a har in koyar da wadansu na kuma taimaka wa ’yan uwa da abokan arziki.
Wadanne matsaloli kake fuskanta a wannan aiki?
Babbar matsalata dai ba ta wuce ta rashin isassu kuma ingantattun kayan aiki na zamani ba, ta yadda idan na zana mutum ko wani gari haka sai ka rantse na’ura ce ta yi ba zanen hannu ba ne. A halin yanzu ba ni da karfin jarin mallakar kayayyakin aiki kuma ba wanda zai tallafa min amma da zan samu, da na wuce haka. Aiki ne da yake bukatar juriya domin idan kana yi wani lokaci ma sai a rika yi maka dariya ana kallon kamar ko rashin aikin yi ne ko kuma kana aikin banza ne alhali a birane da kasashen da aka ci gaba duk ana bukatar masu irin wannan fasaha ta hannu da ba inji ne ya zana ba.
Me da me ka ke bukata wajen aiwatar da wadannan zane-zanen?
Eh, yanzu dai ina amfani da fensir ne kawai da kala (launi), amma da zan samu jari akwai inki (tawada) ko launi mai kyau mai inganci ba irin wanda ba zai fito da komai radau ba, kuma kayayyaki ne masu tsada.
Akwai wani kira da kake da shi ga gwamnati ko kungiyoyi?
Kiran da zan yi wa gwamnatoci ko kungiyoyi shi ne a samu wadanda za su dauki nauyina in yi karatu don in je in kara kwarewa a kan wannan kwas tunda ana yin sa tun daga kwaleji zuwa jami’a. Na tabbata idan na hada wannan baiwar da karin ilimi, zan kai inda ba a tsammani. Hakan zai ba ni damar koda wasu kamfanonin da ke bukatar masu zane (cartoon) ba su dauke ni aiki ba to zan bunkasa sana’ata in ma horar da wadansu domin akwai alheri a ciki. Sannan ina bukatar a tallafa min da kayan aiki a halin da nake ciki wanda ko ta nan ma zan iya daukar nauyin wasu abubuwa da dama.