Tun ina makaranta na kuduri aniyar zama marubuciya – A’ishatu Gidado Idris

An fi sanin ta da lakanin ‘Uwa’ amma sunanta na yanka A’ishatu Gidado Idris. Ta kasance kwararriyar marubuciya a harsunan Hausa da Ingilishi, sannan kuma ita kwararriya ce wajen ilimin taurari da na sanin halayyar dan Adam. Wace ce ita kuma yaya aka yi ta zama marubuciya? Wadannan da ma wasu tambayoyin, duk ta amsa […]

Tun ina makaranta na kuduri aniyar zama marubuciya – A’ishatu Gidado Idris
Tun ina makaranta na kuduri aniyar zama marubuciya – A’ishatu Gidado Idris

An fi sanin ta da lakanin ‘Uwa’ amma sunanta na yanka A’ishatu Gidado Idris. Ta kasance kwararriyar marubuciya a harsunan Hausa da Ingilishi, sannan kuma ita kwararriya ce wajen ilimin taurari da na sanin halayyar dan Adam. Wace ce ita kuma yaya aka yi ta zama marubuciya? Wadannan da ma wasu tambayoyin, duk ta amsa wa Aminiya, a wata tattaunawa ta musamman da ita:

Bari mu fara da jin tarihinki a takaice.
Ni dai mutuniyar Zariya ce kuma haifuwar can amma ba can na taso ba. An haife ni a 1960 kuma na yi makarantu da dama amma iyaka ta Sakandare. Na fara Diploma amma ban gama ba saboda takardar shaida ta ta kueen Amina Collage Kaduna ce. Ba na aiki amma ina rubutun littattafai, duka a Hausa da kuma Ingilishi. Ina da ’ya’ya uku kuma yanzu ina zaman aure ne a Abuja.
Kin kasance marubuciya, ta yaya kika fara harkar rubutu kuma me ya ja hankalinki har haka ta tabbata?
Na taso na ga hakan nake kawai. Yanayina ne na hakan, domin ko a makarantar sakandare, ina cikin masu shiga gasar rubuce-rubuce kuma ina daya daga cikin masu yi wa makaranta rubutu na labarai a lokacin. Don son harkar karatun littattafan da ba a aike ni in karanta ba, aka ba ni mukamin ‘Library Prefect.’ Na karanta littattafai da yawa. A nan na kara samun kwarewa a rubutu. Ko a lokacin na yi alkawarin zan zama marubuciya. Ina sha’awar in ga na yi magana ta zama magana.
Abin da ya ja hankalina shi ne, zama ni kadai da nakan yi da kuma nazarin zuci a kan ababen rayuwa da nake yi a kowane lokaci. Ta haka na san cewa akwai magana a zuciyata.
Ko za ki kara bayani game da irin rubuce-rubucen da kika yi a lokacin kina sakandare? Kin taba cin gasa a lokacin kuma da wani labari ne?
A lokacin ana ba mu maudu’i ne da za mu yi rubutun a kai. Yawanci maganar zamantakewa ne. To kuma ka ga sha’awata irin wannan ce. Marubuci, marubuci ne kuma yana iya rubutu a kan komai amma ni kam ban kware a rubutun komai ba illa na zamtakewa. Kuma duk littattafana duk sun kunshi harkar aure ne da zamantakewa. Na rubuta littattafan da aka buga guda biyar na Ingilishi da kuma uku na Hausa, yanzu ina kan na hudun. Amma a lokacinmu ba a cika yi gasa ta mutun da mutun ba sai dai makaranta da makaranta. Kuma mu biyu ne muke sa makarantarmu ta ci nasara.
Har yanzu ban taba cin gasa ba a rubutuna. Ina fata dai zan yi kokarin shiga. Amma na samu amincewar jami’o’i biyu a jihata ta Kaduna, ana karanta littattafaina ta fuskar Adabi kuma Jami’ar ABU Zariya sun yi amfani da littafina Duniyar Gizo ga dalibai masu neman digiri na biyu, shekaru biyar da suka wuce.
A wace shekara kika fara rubuta littafi kuma wanne aka fara bugawa? Ya zuwa yanzu guda nawa kika rubuta kuma guda nawa suka shiga kasuwa?
Na fara rubutawa a 1990, an fara buga littafina 1991 mai suna Rabiat kuma Informat ne suka buga. Bayan wannan, na buga littattafai hudu: Picking Up the Pieces, Rabiat’s Diary, Memoirs of a Modern Hausa Girl da Reply to a Letter, wanda shi ne zai fito a makon gobe in sha Allah. Na Hausa kuma su ne: Duniyar Gizo, Macentaka da Kace-Nace. Ina da niyya da kudurin daukar rubutuna da muhimmanci fiye da yadda na dauke shi a da.
To, tsakanin Hausa da Ingilishi, wane yare kika fi jin dadin rubutu da shi kuma saboda me?
A da nafi jin dadin rubutu da Ingilishi amma ka ga ikon Allah na fi son yi da Hausa. Dalili shi ne, na fi samun abin cewa da yarena. Wancan aro na yi kuma na fi ganin littattafan Hausa za su fi tasiri ga al’ummata.
Cikin littattafanki, wanne ya fi burge ki kuma me ya sa?
Cikin littattafaina, Duniyar Gizo ya fi burge ni saboda yadda tsarinsa yake. Labari ne amma kuma muhawara ne. Na fi jin dadin rubuta shi kuma nazarin da na yi ya burge ni, saboda a dabarance na tsara shi. Cikin dabara na hada mata da mijinta suka fahimci juna ta wata hanya da ya wuce na sulhun ’yan uwa ko abokai. Na shirya yadda suka hadu ta duniyar gizo, ya kuma sake bikonta ba tare da ta san shi ne ba, domin ya canja suna kuma ba hotonsa. Matar da mijin sun rabu ne a baya kuma ta yi alkawarin ba ta ba shi.
A harkar rubuce-rubuce, wane kalubale kika taba fuskanta wanda ba za ki manta da shi ba?
E, na samu kuwa. Akwai lokacin da ake son littattafaina za a yi amfani da su a makaranta amma sai ya zamana ba ni da kudin bugawa nan take. Na so a dan jira aka ki, dole na rasa wannan damar. Nakan ba da littattafaina sai wasu su ce ba za su karba ba saboda wai ba na cikin marubutan da ake yayi. Amma Kola Bookshop da Hamdal suna mani matukar kokari. Kuma wanda ba zan iya mantawa ba shi ne wanda za a sa littafina a neman Award International (Gasar Duniya), aka ba ni lokaci sai rashin lafiya ta shake ni har lokacin ya wuce. Shi y asa yanzu zan tara duk littattafaina in buga su, in aje saboda idan an nema in mika.
Wane abu kika samu albarkar rubutu kuma kike alfahari da shi a rayuwarki?
Na samu Kyaututtukan Karramawa guda biyu albarkacin rubutu. Ina alfahari da su. Suna nan na yi ado da su. Amma har yanzu ban samu kudi ba saboda rubutu amma kuma alhamdu lillahi, na samu karbuwa wajen jama’a da yawa da mutuntawa. Ai na gode.
Cikin manyan marubuta na zamani da na dauri, na gida da na waje, wanne ko wacce ta fi burge ki kuma kike son koyi da su?
A cikin na waje, ina son rubutun wani mutum mai suna Khalid Hussein. A gida, ina matukar son rubutun Mahmoon Baba Ahmed da Ado Ahmed Gidan Dabino. Wadannan suna da wani abu da nake so, watau fito da gwani da zaa fafata da su. Kuma Mahmoon ya san halin zamantakwa sossai. Kuma Ado ya san sirrin soyayya da kuma zamantakwa. Khalid Hussain ya san muhimmancin zuciyar dan Adam da kuma damuwarsa. Ina son rubutun sha’iri marigayi Alkilu Aliyu. Amina Abdulmalik da Ibrahim Sheme sun burge ni, shi da littafin ’Yartsana, ita kuma da littafinta Ruwan Raina.
Duk wadannan marubuta ne da ke burge ni, suna nuna mani a rubutunsu cewan akwai mutane kala-kala kuma suna fidda halin dan Adam baro-baro, ba wai abin da kawai ake yayi ba. Babban gwarzona, shi ne Mahmoon. Da za a gane rubutunsa, da na dace.
Batun fim kuma fa, ko cikin littattafanki akwai wanda aka mayar zuwa fim, idan babu ko kina da niyyar yin haka nan gaba?
E, an so a mayar da Rabiat zuwa fim shekaru 15 a baya amma abin ya watse. Na sake gwada littafin Picking Up the Pieces, yunkurin shi ma ya zama wani wasan kwaikwayon. To sai na ce sha’anin bai karbe ni ba.
Ana kukan al’ummarmu suna da nuna halin ko’in kula da karatu, ko a matsayinki na marubuciya, akwai wata shawara ko jan hankali da za ki yi musu?
E, gaskiya ne, ana iya jan hanakalinsu da laffuza masu kyau cikin lallashi, cewan ilimi na iya ba ka komai na duniya idan kana da shi kuma har ka iya amfani da shi ta hanyar da ya kamata. Akwai yadda za a kwadaitar da su da son ilimin. Idan misali na tsara rubutu wanda zai nuna masu matsala, sannan kuma in nuna masu yadda ake kau da matsalar, ai za su so sanin hakan ta karatu. Ai watau marubutan wani lokaci suna rubuta labari ne kawai na karanta-ka-ji-dadi-ka-wuce, ba wani darasi abin koyi, shi ya sa. Ai ko rubutun soyyaya da ake ganin kamar ba muhimmanci, akwai ilimi a cikinsa idan marubuci ya gane. Abin damuwa shi ne, sai ka ga matashi bai gane yadda rayuwa take ba kuma ba ya son ya gane.
Marubuta fa, ko kina da wani kira a gare su, musamman na zamani? Domin wasu na kukan cewa suna gurbata tarbiyya ne maimakon gyara, inda har ma Farfesa Ibrahim Malumfashi ya kira su da ‘Adabin Kasuwar Kano.’
Irin wadannan marubutan, to ai saboda su ne ba a iya sabo da irin namu rubutun. Su ne masu danne sha’awar namu rubutun na fadakarwa. Mutanenmu ba su son a gaya masu gaskiyar magana sai wasan duniya ko wasu maganganu na shirme, wai ana raya soyayya. Ni idan ina maganar soyayya, ina maganar yadda za a zauna cikinta ne lafiya ba wai yadda ake soyyayar ba a indiyance. Ai ko Indiyawan sun san gaskiya, suna neman tuwo ne. Saboda haka ina kira ga ’yan uwana marubuta, mu cire batsa da wasu shashanci a rubutunmu. Don Allah mu rubuta abin da zai fisshe mu da al’ummarmu kuma mu ji tsoron Allah,
don duk abin da muka rubuta adashi ni.