Tun ina makaranta nake sha’awar aikin jarida – Habiba Rabi’u Bako
Hajiya Habiba Rabi’u Bako tana daya daga cikin mata ’yan jarida da suka yi fice musamman wajen gabatar da shirin Yara Manyan Gobe da Shafa Labari Shuni, a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN), a zantawarta da Aminiya ta bayyana yadda ita da maigidanta suka zama ’yan jarida da kuma sauran batutuwa: Aminiya: Za mu […]
Hajiya Habiba Rabi’u Bako tana daya daga cikin mata ’yan jarida da suka yi fice musamman wajen gabatar da shirin Yara Manyan Gobe da Shafa Labari Shuni, a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN), a zantawarta da Aminiya ta bayyana yadda ita da maigidanta suka zama ’yan jarida da kuma sauran batutuwa:
Aminiya: Za mu so ki gabatar da kanki?
Habiba Rabi’u Bako: Assalamu alaikum sunana Habiba Muhammad Rabi’u Bako. An haife ni ne a ranar 6 ga watan Yuli 1949 a cikin garin Kaduna. Kodayake, duka iyayena biyu mutanen Kano ne.
Na fara makarantar Islamiyya a wata makaranta da ke Titin Zariya Road. A nan na yi karatu har Ubangiji Ya sa na sauke Alkur’ani. A bangaren karatun boko kuwa, na yi makarantar firamare a Katsina Road. Na wuce Kwalejin Horar da Malamai Mata (WTC) a cikin shekarun 1960. Daga nan sai aka yi mini aure da Alhaji Muhammad Rabi’u Bako. Idan na koma baya kadan, a gabanmu aka bai wa kasar nan ’yancin kai. Saboda lokacin muna ’yan makaranta an jera mu a gefen hanyar da Sarauniyyar Ingila za ta bi, muna daga tutar Najeriya.
Aminiya: Maigidanki ya fara aikin jarida lokacin da kuka yi aure?
Habiba Rabi’u Bako: Ah, lokacin yana dan jarida a gidan Rediyon Jihar Arewa da ke nan Kaduna. Lokacin ana kiransa Broadcasting Company of Northern Nigeria (BCNN) wanda daga baya ya koma Rediyon Tarayya na Kaduna.
Aminiya: Me ye ja hankalinki a aikin jarida?
Habiba Rabi’u Bako: Sha’awa ce, kuma ta samu asali ne tun muna makaranta. Saboda lokacin akwai Malam Yusufu Ladan wato dan Iyan Zazzau na yanzu. Da Malam Adamu Salihu da maigidana duka suna aiki a gidan rediyon BCNN. Ni kuma tun a makaranta ina kaunar aiki a rediyo. Saboda duk lokacin da malaminmu ya sanya mu karatun littafi. Idan na fara karatu sai ya ce, “Habiba ko za ki yi aikin jarida ne.” Kodayake lokacin ni kadai ce mace a ajinmu. Cikin abokan karatuna akwai Alhaji Yahaya Muhammad da Larai Muhammad da marigayi Bala Inuwa Dogo da sauransu.
Bayan aurena, sai na bayyana wa maigidana kuma ya ba ni goyon baya. Na fara zuwa gidan Rediyon Tarayya na Kaduna , ina gabatar da shirin Zabi Sonka da Asuba ta Gari. A lokuta da dama maigidana da kansa yake raka ni daga gida zuwa wajen aikin domin kamar Asuba ta Gari shirin zabi sabonka ne da ake kammalawa wajen karfe 12:00 na dare.
Idan na koma baya kadan, lokacin muna yara a makaranta Alhaji Yusufu Ladan yana zuwa ya dauko mu saboda mu shiga shirin Yara Manyan Gobe. Domin shi ne mai gabatar da shirin a lokacin. Yana da kyau jama’a su fahimci cewa tun a lokacin kaunar gabatar da shirin ya shiga zuciyata. Akwai wata rana da ya taba fada mini cewa yadda yake zuwa yana dauko mu daga makaranta, watakila mu ne za mu kawo wasu kuma mu zauna a kujerarsa domin gabatar da shirin. Na ce Allah Ya tabbatar da hakan. Yau da gobe ga shi hakan ya zo ya tabbata.
Aminiya: Wadanne shirye-shirye kika gabatar a FRCN?
Habiba Rabi’u Bako: Na gabatar da shirye-shirye kamar su: Zabi Sonka da Shafa Labari Shuni da Uwargida Barka da Rana da kwarya Tagari da Kallabi Tsakanin Rawwuna da wani sihrin zabi sonka na harshen Inglishi wato Tuesday Listener Choice. Wata rana da ba zan taba mantawa da ita ba ita ce ranar da aka dauke ni ma’aikaciyar dindindin a gidan Rediyon FRCN saboda yadda farin ciki ya lullube ni. Sai marigayi dahiru Modibbo ya ce yaya za ki yi da aiki da hidimar gida. Na ce masa ai maigidana da sauran ’yan uwana za su taya ni. Shi ke nan cikin yardar Allah aikina bai hana ni hidimar gida ba.
Aminiya: Wadanne abubuwa ne ba za ki manta da su ba a aikin jarida?
Habiba Rabi’u Bako: Akwai wata rana ina sauri na je gabatar da wani shirina. Na taho a guje ba na ganin wanda ke gabana domin na makara. Ina cikin haka ne sai na bangaje Shugaban Gidan Rediyon Alhaji dahiru Modibbo, bisa rashin sani. Ina dubawa sai na ga ashe shi ne. Sai na ce ka yi hakuri yallabai. Da bude bakinsa sai ya ce mene ne, lafiya? Sai na ce sauri nake na je na dauki shirina a sutudiyo, ba na so a samu wata matsala. Sai ya ce ba komai, ki kwantar da hankalinki. Ba komai.
Bayan na kammala, sai na ce wa kaina yaya ke nan. Na ce watakila a yau aikina a gidan rediyon ya kare ke nan. kila idan na koma ofis zan samu takardar sallama na jirana. Bayan wasu kwanaki, ko da masinja ya shigo ofis dina da takarda a hannunsa hankalina bai kwanta ba, musamman ganin ta fito ne daga shugaban gidan rediyon. Amma ina bude takadar sai na ga ya yaba mini ne da kuma kara mini kwarin gwiwa. Ya ce na ci gaba da abin da nake yi. Ya ji dadin yadda nake kula da aikina da muhimmanci.
Hakazalika, akwai wata rana muna cikin gabatar da shirin Zabi Sonka da ni da Yahaya Barau Rigachikun a Ranar Sallah. Muna cikin aiki, ashe yadda muke gabatar da shirin yana burge shi. Sai kawai Alhaji dahiru Modibbo ya taho dakin da muke gabatar da shirin, ya yi iso cewa idan mun sanya faifai mu fito yana nemanmu. Ba tare da wani bata lokaci ba muka bi umarninsa. Muka nufi ofis dinsa cikin fargabar cewa watakila mun aikata wani kuskure ne gagarumi. Sai ya ce mana sannunku da kokari. Muka ce masa mun gode. Ashe wai dalilin kiranmu shi ne saboda aikin da muke yi ya yi masa ne. Kuma ya neme mu ne kawai domin ya yaba mana, shi ke nan.
Aminiya: Cikin shirye-shiryen da kika gabatar wanne kika fi so?
Habiba Rabi’u Bako: Ai kowannensu gaskiya ina sonsa. Ka ga shirin Yara Manyan Gobe da shi na fara kuma kusan kowace makaranta da ke garin Kaduna da wadanda ke fili da lungu ba inda ban je na dauko yara ba. Saboda ni nake zuwa na bukaci su shiga shirin. Bayan hukumar makarantar ta amince ne kuma an sanya rana, sai mu tafi da motar gidan rediyo domin kawo su. Idan mun kammala shirin sai mu raba musu kyaututtuka kamar su littafai da abin rubutu da sauransu, kafin mu koma da su makaranta. Saboda mu ma a lokacin da ake kai mu irin haka ake mana. Domin haka sai muka yi koyi da wannan abin alherin da aka yi mana. Hakazalika, akwai lokacin da aka taba ba da ni aro zuwa sashin talabijin wato NTA, inda a can ma na gabatar da shirin Yara Manyan Gobe. bangaren wasan kwaikwayo kuwa, na shiga wasanni kamar su: Samanja Mazan Fama da Duniya Budurwar Wawa.
Aminiya: Ganin cewa ke da maigidanki duka ’yan jarida ne ku, ko kuna da magada a cikin ’ya’yanku?
Habiba Rabi’u Bako: Tabbas akwai. A yanzu haka akwai ’ya’yana da suke aiki a gidan Rediyon Najeriya (FRCN) ciki har da Abdullahi Bako.
Aminiya: Shin Ai’sha Audu Bako da ita ma take aiki a gidan Rediyon Najeriya (FRCN) diyarki ce?
Habiba Rabi’u Bako: A’a, amma akwai kyakkyawar dangantaka tsakanina da ita. A’isha ta dauke ni kamar mahaifiyarta, hakazalika ni kuma na dauke ta kamar diyar da na haifa a cikina.
Aminiya: Wadanne nasarori za ki ce kin samu a aikin jarida?
Habiba Rabi’u Bako: Babbar nasarar da nake ganin na samu ita ce ta ilimantar da al’umma daga damar da Ubangiji Ya ba ni ta zama ’yar jarida. Sai lambobin girmamawar da na samu musamman daga gidan rediyon FRCN lokacin bikin cikarsa shekara 50 da kafuwa da sauran kyaututtuka.
Aminiya: Kina da wani buri a halin yanzu?
Habiba Rabi’u Bako: Burina bai wuce yadda muka gama aikin nan lafiya, Allah Ya sa na baya da mu su ma su gama lafiya ba.
Aminiya: Wace shawara kike da ita ga matasa ’yan jarida?
Habiba Rabi’u Bako: Mu a lokacin da muka gudanar da aikinmu, ba za mu ce ba ma son kudin da ake biyanmu ba. Amma sha’awarmu ga aikin ita ta rinjayi komai. Saboda haka idan suka kara kaunar aikin za su samu amfani sosai.