‘Tun ina shekara bakwai mahaifina yake kwanciya da ni’
’Yar magidanci ta kai kai shi kara saboda ya matsa da yin fasikanci da ita
Wani mutum mai shekara 49 ya fada komar jami’an ’yan sanda a kan zargin yi wa ’yarsa mai shekara 12 da haihuwa fyade.
Sanarwar da Kakakin rundunar ’yan sandan jihar DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar, ta ce an kama mutumin ne bayan da ’yar ta kai shi kara a ofishin ’yan sanda da ke Itele Ota a Jihar Ogun.
- Daliban Kaduna: Har yanzu iyayen daliban ba su gana da su ba
- Babu tabbas za a yi jarabawar Mayu/Yuni a 2021 —WAEC
- Buhari ya nada sabon Shugaban ’Yan sandan Najeriya
DSP Abimbola Oyeyemi ya sanar cewa yarinyar ta ce tuna tana shekara bakwai da haihuwa mahaifin ya soma kwanciya da ita.
Muryar Amurka ta ruwaito cewa, kaiwa makura ta matakin gajiya da wannan lamari na kwanciya da ita ba a son rai ba, ya sanya yarinyar ta yanke shawarar kai korafi caji ofis domin ganin an kawo karshen wannan keta mata haddi da mahaifin ke yi.
Bayan shigar da korafin ne, DPO na ofishin ’yan sandan Itele Ota, CSP Monday Unoegbe, ya tura wata runduna ta yi bincike tare da kamo mutumin da ake zargi.
DSP Oyeyemi ya ce, wanda ake zargin ya amsa laifin wanda a cewarsa rashin samun nutsuwar magance sha’awarsa ta da namiji da matarsa ya sanya ya fara zakke wa ’yar cikinsa.
Mutumin ya shaida wa ’yan sandan cewa, “matarsa ta tsufa kuma ba ta ba shi sha’awa.”
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Edward Awolowa Ajogun, ya bayar da umarnin ci gaba da gudanar da bincike a kan mutumin domin samun hujjojin gurfanar da shi a gaban kuliya.
Ya kuma bayar da umarnin kai yarinyar asibiti domin a tabbatar da ingancin lafiyarta.