Tun ina yarinya nake sha’awar kasuwanci – D-Meenat

Wata matashiyar ’yar kasuwa kuma Shugabar Kamfanin Samar da Kayan Kwalliya na D-Meenart  da ke Kano, Amina Adamu Abbas  ta  ce tun tana yarinya ta tashi da son kasuwanci, inda ta yi kira ga yara su fara sana’a tun suna kanana, don hakan ya sa lokacin da suka girma ba za su fuskanci matsalar rashin […]

Tun ina yarinya nake sha’awar kasuwanci – D-Meenat

Wata matashiyar ’yar kasuwa kuma Shugabar Kamfanin Samar da Kayan Kwalliya na D-Meenart  da ke Kano, Amina Adamu Abbas  ta  ce tun tana yarinya ta tashi da son kasuwanci, inda ta yi kira ga yara su fara sana’a tun suna kanana, don hakan ya sa lokacin da suka girma ba za su fuskanci matsalar rashin aikin yi ba.

Matashiyar ta shaida wa Aminiya cewa ta karanci harkar kula da lafiyar hakori a Makarantar Kimiyyar  Lafiya ta Jihar Kano ce, amma ta fara harkar kayan kwaliya ce shekaru da dama da suka gabata lokacin da ta je Legas don ziyarar ’yan uwanta. “Bayan na kammala karatun sakandare ina jiran sakamako sai na je Legas don ziyarar ’yan uwanmu. To a can ne na shiga wata makaranta ta koyar da sana’o’i inda na koyi harkar harhada man shafawa da sabulu da sauransu. Bayan na dawo Kano sai na dan fara gwada abin da na koyo a Legas. Na fara da man shafawa da sabulu. A hankali a hankali na ci gaba da yin wasu kayayyakin da suka shafi kwaliyya da sauransu. Wanda ya kara min kwarin gwiwa shi ne kawuna, ya ba ni kwarin gwiwa sosai har ya sa na yi rajista da Hukumar CAC da ta NAFDAC,” inji ta.

A  cewar Amina, yanzu haka tana samar da kayayyaki nau’i 20 da take sayar da su  a wasu jihohin kasar nan har da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya. “Ina nan a haka har na kara bunkasa wannan sana’a tawa ya kai na kara yin wasu abubuwa da suka hada da man gashi da man wanke gashi da hodar aski da sauransu. Kuma alhamdulillahi  yanzu mutane sun gane ingancin kayayyakin da nake samarwa domin ba wai kawai a iya Kano ko Najeriya nake sayar da kayayyakina ba, har da kasashen da ke makwabtaka da mu. A kullum samun ci gaba nake yi a wannan sana’a,” inji ta.

Amina ta ce duk da cewa ta gaji saye da sayarwa daga mahaifiyarta amma  sha’awar sana’ar ce tasa take ci gaba da yinta.

Ta kara da cewa idan mutum yana so kasuwanci ko sana’arsa ta dore dole ya jajirce tare da yin hakuri “Sana’a sai an jajirce an yi hakuri domin akwai mutane da ke daukar kayan mutum su yi alkawarin za su biya lokaci kaza amma ba su biya a kan lokaci. Wata sa’a ma sai dai mutum ya hakura da bibiyar a biya shi bashinsa,” inji ta.

A cewarta la’akari da alfanun da take samu a cikin wannan harka ya sa ta yi tunanin  kafa  wata cibiya da za ta zama hanyar tallafa wa marasa galihu a cikin al’umma. “Ina da burin in ga matasa sun mayar da hankali wajen sana’a ko kasuwanci, hakan ya sa na bude wannan wuri domin tallafa wa matasa wajen koyon sana’a ko kasuwanci tare da nisantar harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi.  Yanzu haka muna horar da matasa marasa karfi idan mun gama horar da su mukan taimaka wa wadansunsu da kayan da za su fara sana’ar ko kasuwancin, saboda ba mu yi karfin da za mu iya tallafa wa kowa da kowa ba,” inji ta.

Ta kara da cewa “Kuma ina zuwa makarantun sakandare domin koya wa dalibai sana’o’in da za su dogara da kansu a nan gaba. Ni nake sayen kayayyakin da ake amfani da su wajen horar da daliban. Yanzu haka kwalliya ta fara biyan kudin sabulu don daliban da suka koyi aiki da yawa sun fara gwada abin da suka koya.”

Amina ta yi kira ga matasa su dauki  duk irin sana’ar da suka zaba da muhimmanci, domin a cewarta sana’a ita ce mutuncin mutum.

Ta kuma yi kira ga gwamnati ta rika tallafa wa masu kananan sana’o’i domin su samu karfin gwiwar gudanar da sana’o’insu. “Yanzu ni da a ce zan samu tallafin gwamnati musamman na injinan da zan yi amfani da su na tabbata sana’ata za ta bunkasa sosai da sosai. Kin ga a yanzu saboda rashin karfi da kananan injina nake gudanar da ayyukana,” inji ta.