Tun ina yaro na fara hidimar Shata – Aliyu Kankara

Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, malami ne a Jami’ar Tarayya Dutsin-ma a Jihar Katsina. A kwanakin baya ya fitar da sabon littafin tarihin marigayi Alhaji Mamman Shata, wanda ya sa wa taken SHATA: Mahadi Mai Dogon Zamani. Ya bayyana wa Aminiya yadda sha’awarsa kan Shata ta faro: Tun yaushe ka fara bibiyar wakoki da al’amuran marigayi […]

Tun ina yaro na fara hidimar Shata – Aliyu Kankara

Dokta Aliyu Ibrahim Kanqara, marubucin littafin Shata Mahadi Mai Dogon Zamani

Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, malami ne a Jami’ar Tarayya Dutsin-ma a Jihar Katsina. A kwanakin baya ya fitar da sabon littafin tarihin marigayi Alhaji Mamman Shata, wanda ya sa wa taken SHATA: Mahadi Mai Dogon Zamani. Ya bayyana wa Aminiya yadda sha’awarsa kan Shata ta faro:

Tun yaushe ka fara bibiyar wakoki da al’amuran marigayi Alhaji Mamman Shata Katsina?

Na fara kaunar Alhaji Shata da wakokinsa tun a 1974, lokacin muna Unguwar Kanawa, Kaduna. Lokacin ban wuce shekara shida da haihuwa ba. Tun iyayena ba su fahimta har suka gane. Ko a talabijin aka nuno shi yana waka, na kama murna ke nan. Da zarar kuma an dauke wuta, kafin ya ida wakar to har kuka nake yi kuma na dinga fushi ke nan har safe.

Ko a cikin 1975, wata rana da babana zai  tafi Katsina, ya ce in shirya in bi shi, tunda a sannan ban shiga firamare ba. Mun shiga Funtuwa a tsakanin Magariba da Isha’i, har muka bi santar gidan Shata. A daidai kofar gidan Shatan mun zo wucewa sai babana ya ce da ni: ‘Ali Gadanga, ga gidan Shata, ga shi can ma zaune kofar gida.’ Ya fadi mani haka ne saboda sanin da ya yi ina matukar son makadin. Sai na ce masa ‘mu tsaya in gan shi’ Sai ya ce: ‘a’a, saboda muna sauri.’ Amma gab da za mu wuce Allah Ya jiye mani muryar Shatan, na ji yana cewa ‘a zo a kwashe kwanonin abincin nan.’ Ba zan taba mance wannan ba.

A Funtuwa ke nan, to zamanka a Daura kuma fa?

A tsakanin 1976 da 1978 an kai ni riko Daura wajen wana Ahmed Ibrahim Kankara, lokacin yana aiki a can. To a can mukan ga wasan Shata a kofar fada in ya ziyarci Sarki, da kuma Niger Club da ke kan hanyar Zangon Daura. Har ma ni ne Shatan Islamiyya Firamare, inda na yi karatu. Idan an gama shara da marece, sai a zo bakin ofishin Hedimasta a yi wasan kwaikwayo. To, nan nikan dan yi wakokin Shata, ’yan ajinmu na yi mani amshi. Sunan Hedimasta din mu Hamisu Famili, wanda daga baya ya zama Matawallen Daura.

Daga Daura kuma sai ina?

Cikin 1979 ina aji 5 na Firamare a Kankara, (bayan babana ya bar Kaduna, mai riko na kuma ya bar Daura) sai Shata ya zo kamfe na GNPP a cikin tawagar ’yan siyasa a Kankara, nan muka yi ta bin motarsa da gudu, aka zagaya gari da mu, shi kuma yana waka. Wannan ta sa wanshekare ni da abokina Garba (Abubakar) Suleiman Kankara (yanzu yana aiki a Dakin Awon Jini na Asibitin Tarayya ta Katsina), muka sayo littafi mai warka 40, muka fara rubuta tarihinsa, har ma muka samu shugaban GNPP na yankin Kankara Alhaji Dadda’u Tela, muka zanta da shi, amma a lokacin ana ta yarinta, ba mu dauki abin da gaske ba, ba mu kuma rubuta komi ba. Sai dai me? Abin da yaro yake so kuma ya girma da abin nan a zuciyarsa, watarana sai ya tabbata. To, ashe Allah za Ya tabbatar da abin a gaba.

Ashe ka dade kana bibiyar al’amuran Shata haka?

A tsakanin 1986 da 1994, babana na aiki a Malumfashi, amma ina ziyartar abokaina a  tsakanin Daura, Dutsinma, Kankara, Funtuwa, Zariya da Katsina, duk samari masoya Shata sun san ni kuma inda duk na je ana maraba da ni, ana kuma son in zauna in ba da labari sabo na Shata da na kalato. Tun da saboda bibiyar al’amurransa, kafin in je wuri an riga an samu labarina, koda kuwa mutum bai taba gani na ba. Sai da ta kai ma a Malumfashi da Daura mun kafa Kungiya ta masoya Duna na Bilkin Sambo. Cikin 1987 na fara zuwa gidan Shata kuma muna haduwa da shi a Zariya, a Magume gidan Sani Gadagau, Ba-ka-toshi da Kano da Funtuwa da Katsina, Nasara Guest Inn, gidan Sa’in Katsina.

Shin wa ya fara kai ka wurin Shata?

Ba wanda ya fara kai ni ya gabatar da ni wurinsa, ni na kai kaina, musamman saboda dalilan can na sama. Cikin 1990, ina tsammanin ma ranar Lahadi (3/9/1990) ne, lokacin na kammala karatu a Kwalejin Kimiyya Da Fasaha (CAS) Zariya, na tafi Funtuwa na samu Shata, na kai masa wani littafi da na rubuta mai suna “Karon Battar Karfe” (na hikayar yaki ne). Na kwana har da safe ni da shi da Mati Bamba muka tafi ofishinsa na kan hanyar Zariya, lokacin yana shugaban Jam’iyyar SDP, nan muka wuni. Na gabatar masa da littafi, na kuma bukaci ina so ya biya kudi a wallafa littafin. Amma ban samu nasara ba, don bai ce ya amince ba, bai kuma ce ba ya yi ba.

Daga nan kuma fa?

Na yi wakokin Shata a CAS Zariya, a kungiyarmu ta Hausa, a matsayina na Shatan CAS, sannan lokacin da nake karatu a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, na zama Shatan ABU na kungiyar Hausa, duk don dalilin soyayyata da Shata, mai benen-bene na Izzatu Musawa. Ka ga ke nan wanda duk za ya ba da labarin ko nuna son Shata, a bayana yake. Wanda duk ya sha wuta baran tsire ne, kuma labarin dare a tambayi kura. Duniya ta san da haka.

Kana daya daga cikin mutane hudu da suka rubuta littafin tarihin Mamman Shata. Ka ba mu labarin yadda al’amarin ya faru ? Yaya aka yi kuka hadu kuma wace yarjejeniya kuka shiga da shi kafin ku fara?

A cikin 1992, lokacin ina karatun digiri na farko a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, aji na uku, Allah Ya hada ni da wani yaro a Jami’ar mai kwazo, mai ilimi, ana ce masa Kabiru Husaini Gwangwazo kuma lokacin yana karatun digiri a kan harshen Turanci. Mun fara haduwa da shi a taron OAU (Organization of African Unity) na wasan kwaikwayo na daliban Turanci, inda ya fito a matsayin Shugaban Zaire watau Mobutu Sese Sekou. Sha’awar da ya ba ni ta sa na nemi mu yi abotaka, ya amince. Muna nan, muna nan, ya zo wurina, ni ma in je wurinsa. Sai rannan na dauki littafina na Hausa da na rubuta mai suna “Sako Daga Birnin Al-Shabdad” (na hikaya ne), na ba Gwangwazo domin ya duba mani. Bayan kwanaki, sai wani dan rikici ya sanya aka rufe jami’ar. Ina gida Kankara sai na yi amfani da wannan damar na tafi Kano wajensa domin in amso littafin. Sai na tarar an tsare shi a ofishin ’yan sanda na Bompai saboda littafin Danmasanin Kano da ya rubuta, aka kaddamar, amma a baya ya ranci kudaden mutane saboda hidimar bai biya su ba, sun sa an kama shi.

To, a Unguwar Takuntawa inda yake da zama sai aka kai ni wajen abokan huldarsa. To, su suka kai ni wajensa a Bompai. Sai na tarar suna da wata kungiya mai suna Young Writers Club (YWC) Kano, wadda Kabirun ma mamba ne. To, nan suka rike ni na yi kwanaki a wajensu, suka yi mani abin arziki. Kuma suka ba ni fom na cika, na zama dan kungiya. Ina tuna cikinsu akwai Suleiman Uba, Rabi’u Mohammed Kura, Rabi’u Abubakar, Mohammed Garzali, da sauransu. A cikin shirye-shiryen kungiyar ana rubuta tarihin mutanen da suka shahara, ko na garuruwa. To, sai suka ba ni shawarar cewa me zai hana in tafi Funtuwa in nemo izinin rubuta tarihin Shata daga wajensa? Da dama sun yi tunanin hakan tun kafin in bakunce su.

To, ka amsa wannan bukata tasu?

Sai na amince, na tafi Funtuwa. Na yi sa’a na samu Shata a gida, na ba shi labarin abin da ake ciki da kudurin wannan kungiya, da abin da ta sanya ni in yi mata. Ya yi murna, har na ce masa ‘sun ce ka fadi mani ranar da kake a gari, don mu zo tare da su.’ Ba zan manta ba har ya kama fada yana ce mani ‘ai yanzu na girma, na daina yawon zage, bare a ce za a zo ba a same ni ba, sai dai fa ko in kun ji sanarwa a rediyo ana wani buki, watakila zan je, to sai ku dakata sai ran da kuka ji ba a yin wata sabga ko nadin sarauta.’ Muka rabu a haka.

Na koma Kano na shaida masu, suka ba ni dama da in rubuta littafin. Na fara rubutu, wanda ya kai ni har cikin 1994 (bayan shekara 2 ke nan) na kammala. Sai muka kai littafin ga Ahmed Mohammed, wani mai kamfanin buga littattafai a Gidan Goldie kusa da Singer, Kano. Ana ta cuku-cukun ya za a yi a samu kudi a buga shi, sai na tafi Hidimar Kasa a Legas, cikin watan Nuwamba, 1994.

Ranar da ma zani tafi, na biya ta Funtuwa na yi bankwana da Shata (Lahadi 13/11/1994), har ma na ba shi kwafin littafin, ya amsa ya rika ya duba. Har yana cewa ‘yanzu nan wannan duk aikin tarihina ne?’ Na ce masa ‘e.’ Ya yi fatar Allah sa albarka, sannan ya ce idan na dawo daga Ikko za mu zauna. Ya kuma lissafa mani wasu a Legas cewa idan na je in yi masu intabiyu, mutanensa kamar su Alhaji Na’Allah Dan Ibrahim. A Legas na gaisa da shi Na’Allah Dan Ibrahim, har da ma Alhaji Salmanu Agege, shugaban ’yan daudu na Afirka, da sauransu.

 

Za mu ci gaba