Tun ina yaro nake fuskantar matsala saboda fallasa barna – Sarkin Sanusi II

Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II ya hau gadon sarautar Kano a watan Yunin 2014 bayan rasuwar marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, wanda ya yi sarautar tsawon shekaru 50. A wanann tatatunawar, wanda masanin tsimi da tanadi da tsare-tsaren tattatlin arziki ya yi bayani a kan rayuwarsa da kuma abin da ya shafi tattalin arzikin […]

Tun ina yaro nake fuskantar matsala saboda fallasa barna – Sarkin Sanusi II

Mai martaba Sarki Sanusu II tare da iyalinsaSarkin Kano Muhamamdu Sanusi II ya hau gadon sarautar Kano a watan Yunin 2014 bayan rasuwar marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, wanda ya yi sarautar tsawon shekaru 50. A wanann tatatunawar, wanda masanin tsimi da tanadi da tsare-tsaren tattatlin arziki ya yi bayani a kan rayuwarsa da kuma abin da ya shafi tattalin arzikin kasa, don murnar bikin rantsar da shi a matsayin Sarkin Kano na 57. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Aminiya: Babban burinka shi ne ka gaji kakanka, ya ka ji a lokacin da aka sanar da kai cewa masu zaben sarki sun sanya ka a jerin wadanda za su gaji marigayi Sarkin Kano?
Sarkin Kano: Zai yi wahala mutum ya bayyana irin godiyar da dan sarki yake ji a lokacin da ya samu sarauta. Sai dai kawai mutum ya bayyana godiyarsa ta yin amfani da maganar da Annabi Yusuf ya fada a lokacin da Allah Ya ba shi matsayi. A cikin Alkur’ani inda ya babana cewa ‘‘wannan shi ne fassarar mafarkina da Allah ya tabbatar da shi.” Akwai wani abu da dukkan Musulmi ya yi imani da shi, cewa, Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so. Haka kuma Shi Ya san dalilin da ya sa ya zabi wannan mutumi ya ba shi mulki a wannan lokaci. Haka kuma a duk lokacin da wani ya samu mulki, to sai ya kankan da kansa saboda ka san ba wai don ka fi wasu ’ya’yan sarkin wayo ba ne, kuma ba don ka fi wani kusanci ga Allah ba ne. Allah ya zabe ka ya ba ka mulki ne don ka gode masa. Abin da ya rage mana shi ne mu yi kokarin sauke nauyin da ke kanmu, ma’ana na ayyukan da Allah ya dora mana na jama’a.
Aminiya: Daga lokacin da ka fara karatu a Makarantar Firamare ta St. Annes Kaduna da kwalejin Kings da ke Legas, har zuwa Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, wadanne al’amura ne suka yi maka  tasiri a rayuwa?
Sarkin Kano: Abin sha’awa ne musamamn idan muka koma baya mukan iya tuna abubuwan da suka faru, wadanda muke ganin sun yi tasiri a rayuwarmu ta yanzu. Abin da zan iya tunawa a lokacin da na shiga Makrantar St. Annes ina dan shekara takwas (8), a wancan lokaci na jagoranci dalibai muka yi wata zanga-zanga a makarantar. A lokacin mukan ajiye akwatunanmu a ma’ajiyar da aka tanada. Don haka a duk karshen mako mai kula da dalibai takan gyara wurin, a kuma bude mana don mu yi amfani da kayan da ke cikin akwatunanmu. A duk lokacin da muka bude akwatunamu to sai mun ga wasu kayayyakinmu sun bace, ga shi kuma mun san mabudin a wurin jami’a mai kula da jin dadin dalibai yake, wato “Matron.” To akwai wani lokaci da na bude akwatina sai ban ga biskit dina ba, hakan ya sa na tunkari wannan jami’a da maganar, amma sai ta ce mini “Me kake nufi, kana so ka ce min barauniya ke nan?” sai ni kuma na ce mata ban sani ba, hakan ya sa ta mare ni. Ni kuma sai na jagoranci sauran dalibai muka gudanar da zanga-zanga zuwa ofishin shugaban makarantar. Duk da cewa an yi mana hukunci, to amma tun daga wannan rana kayayyakinmu ba su sake bata ba.
Tsawon rayuwata haka nake a duk lokacin da na ga wani abu ya bace ko ba daidai ba zan yi magana a kai, hakan kuma ya jawo nake shiga matsala. Wani abin ban sha’awa da wannan makaranta ta St. Annes duk da cewa makarantar darikar Katolika ce, to amma suna barin kowane dalibi ya yi addinin da yake so. A matsayinmu na Musulmi ana barinmu mu yi azumi mu kuma yi sallah, har metron dinmu kiristoci sukan tashe mu, mu yi sallar asuba. A wanann wurin ne aka koya mana amfanin hakuri da gaskiya. A karshe na fita da kyakkwan sakamko a jarabawar tafiya sakanidire, Shugaban Kwalejinmu ta Kings College ya rubuta wasikar taya murna ga shugaban makarantar Firamaren din mu.
Aminiya: Shin kana da sha’awar ilimin addinin Kirista (CRK) a lokacin da kake karatu a makarantar St. Anne?
Sarkin Kano: Lokacin da na shiga Kwalejin Kings na kasance dalibi mai kwazo a bangaren ilimin littafin Bible, musamamn ma tsohon alkawari har na samu maki mafi daraja a wannan fannin, har ma na fi sauran dalibai da suke kiristoci. Abin da ya jawo hakan shi ne saboda na san duk abubuuwaun da suke ciki a Alkur’ani tun daga kan yadda Allah ya yi halitta da hikayoyin Annabawa da sauransu. Duk dalibin da ya yi karatun Islamiyya a gida yana da fahimta fiye da sauran dalibai ’yan uwansa kiristoci. Yadda na samu ilimi a bangaren ilimin addinin kirista, ya sa na samu matsala a lokacin da na zo Kano neman tallafin karatuna a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Mutumin da yake kula da abin sai ya ce”Bai kamata malaman da ke kwalejin Kings su rika sa ’ya’yanmu suna karantar ilimin addinin Kirista ba” sai na yi sauri na gaya masa cewa ni na zabi na karanci wanann fannin. Sai ya ce “kai dan gidan sarauta, amma ka tafi har Legas ka karanci ilimin addinin Kirista. A wancan lokaci hakan bakon al’amari ne, amma ni a gare ni abu ne na karin ilimi. Ina ganin cewa kamata ya yi mu rika mayar da hankali ga abubuwan da za su kawo mana hadin kai, ba wadanda za su raba kawunanmu ba.
Aminiya: Bayan burinka na zama sarki ya cika, to me kuma kake son cimmawa a rayuwa?
Sarkin Kano: A fannin wani abu na mulki ko na duniya, ba ni da wani buri. Addu’ata ita ce daga fada sai kabarina. Babu wani abu da nake muradi na mulki. Na taso a fada, a wurina babu wani matsayi da ya kai Sarkin Kano. Abin da mutum ya kamata ya bari shi ne kyakkyawan tarihi.
Abin da nake fata in yi aikin da mutanen Kano za su yi min addu’a a duk lokacin da suka tuna da kyakkyawan shugabancin da na yi musu. Babu wani matsayi da Allah bai ba ni a duniya ba.
Aminiya: An san Kano a matsayin cibiyar kasuwanci, hakan kuwa ba ya rasa nasaba da irin son jama’a da mutanen Kanon ke da shi, me za ka yi don ganin ka karfafa wannnan al’amari?
Sarkin Kano: karfi da arzikin Kano abu ne da aka gina su akan wasu al’amura masu kyau. Farko akwai kyawawan dabi’u na Musulunci da suka hada da gaskiya da amana da hakuri da jama’a da kuma imani. Batun iya mu’amala da jama’a da aka san mutanen Kano da shi zai kara karko don amfanin kowa da kowa.
Aminiya:  A lokacin shugabancinka a matsayin Gwamnan babbab bankin Najeriya, tattalin arzikin kaasar nan ya daidaita, ya aka yi hakan ta kasance?
Sarkin Kano: A rayuwata ina jin ba zan iya karbar duk wani mukami da ban shirya yin aiki a kansa ba. Ina kuma ganin bai kyautu mutum ya karbi mukamin da ya san ba zai iya rikewa ba. Haka kuma bai kamata mutum ya bayar da wani mukami ga mutumin da ya san ba zai iya sauke nauyin da aka dora masa ba. Ina jin an zabe ni a matsayin Gwamnan Babban Banki saboda ganin irin yanayin da aka shiga. A lokacin da matsalolin tattalin arziki suka baibaiye kasa, gwamnati tana neman wanda zai iya yin wannan aikin. Kasancewar duk tsawon lokacin da na dauka a aikin banki har zuwa samun mukamin da na yi na yi shi ne a kan tarairayar asarar hadadar dukiya, wato abin da a Turanci ake kira da “risk management.”  Babban aikin da aka dora min shi ne na ceto bankunan kasar nan daga rushewa. Abin da na fara yi, shi ne, sai na sanya wa kaina wani tsari, inda zan rika auna nasarar aikin da nake gudanarwa, yadda za mu fuskanci rigingimun bankuna ba tare da masu ajiya a bankuna sun yi asarar ko kwabo ba, duk da cewa masu hannun jari za su iya yin asara, ma’aikatan banki za su iya rasa aikinsu, masu karbar bashi za su rasa kadarorinsu, to amma abu ne mai matukar amfani a ce masu ajiya  ba su rasa kudinsu ba. Abu na  biyu, shi ne, yadda ake gudanar da canjin kudin kasar nan. Akwai bambanci mai girma tsakanin abin da na tarar da wanda na samar a matsayin farashin gwamnati. Abu na uku shi ne batun daidaita farashi da sauko da hauhawar farashin kayayyaki. Matukar mutum zai takaita aikinsa a kan abubuwa uku zuwa hudu ba guda 100 a lokaci guda ba, to zai yi nasara. Idan aka dubi tarihin tsawon zamana a matsayin Gwamnan Babban Bankin Najeriya ba wani mai ajiya da zai ce kudinsa ya bata. Haka kuma darajar Naira a wadancan shekaru ya daidaita. Haka kuma an yi maganin hauhawar farashin kayayyaki. Haka kuma na kawo canji a yanayin biyan kudade a kasar nan.
Aminiya: Da za ka sake samun dama ka rike matsayin da ka rike na jagorancin tatatlin arzikin kasar nan za ka sake maimaita abin da ka yi a baya?
Sarkin Kano: Abin da ake bukata shi ne babban banki ya zama ya cimma burin samar da daidaito a harkar tattalin arzikin kasa.  A lokacin shugabancina mun cimma wannan manufa. Akwai bambanci mai yawa tsakanin abin da yake daidai da kuma wanda ya fi shahara. Abin da ya fi shahara ba shi ne koyaushe yake zama daidai ba. A ganina abin da muka yi a Babban banki daidai ne kuma an yi shi a lokacin da ya dace.
Aminiya: Ka hau gadon mulki a lokacin da ake fama da matsalar tattatlin arzikin kasa, wacce gudummowa za ka bayar wajen shawo kan wannan matsala?
Sarkin Kano: Idan ka samu kanka a irin wannan matsayin, abin da mutum zai yi shi ne ya nemo dukkanin bangarori daban-daban da suka hada da na masu ilimi da masana tattatlin arziki da na rayuwar yau da kullum don bunkasa yanayin rayuwar jama’a. Wannan shi ne abin da zan ci gaba da yi don bunkasa halin rayuwa zamantakewar al’ummar Jihar Kano.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya