Tun ina yaro nike addu’ar Allah Ya sa shata ya yi mini waka – Liman Na ’Yalleman
Aminiya: Ko za ta yi mana bayanin takaitaccen tarihin rayuwarka?Na ’Yalleman: Ni sunana Liman Na-’Yalleman. An haife ni sama da shekaru 76 da suka wuce a ‘Yalleman da ke jihar Jigawa a halin yanzu. Na tashi, na girma, har na yi karatun allo, amma fannin fikihu ban wuce ahalari ba. Sannan ni dan kasuwa ne, […]

Aminiya: Ko za ta yi mana bayanin takaitaccen tarihin rayuwarka?
Na ’Yalleman: Ni sunana Liman Na-’Yalleman. An haife ni sama da shekaru 76 da suka wuce a ‘Yalleman da ke jihar Jigawa a halin yanzu. Na tashi, na girma, har na yi karatun allo, amma fannin fikihu ban wuce ahalari ba. Sannan ni dan kasuwa ne, na yi yawo kasashen duniya a harkar kasuwanci, har ma ina yin magana da wadansu harsuna, wadanda suka hada da namu na Afirka da kuma na kasashen Turai. Mun rika kai takalma da atamfofi da leshi, wadansu kayan kuma mun rika yin fiton shigo da su cikin kasar nan.
Aminiya: Batun iyali fa?
Na ’Yalleman: Idan kana nufin ’ya’yana, to ina da ’ya’ya 11. Kuma jikokina 21, har ma da wadda za a aurar nan gaba kadan.
Aminiya: Ko za ka iya zayyano sunayen kasashen da ka ziyarta da irin harsunan da kake magana da su baya ga Hausa?
Na ’Yalleman: Na gaya maka ban yi karatu mai zurfi ba, kuma Ahalari kawai na yi, amma na ziyarci akalla kasashe 19, kuma kasashen su ne, Afirka ta Yamma da Ingila da Faransa da Switzertland. Sannan a nahiyar Asiya na ziyarci akalla kasashe uku. /Harsunan da nike magana da su, su ne Yarbanci da Linganla (yaren Kongo) da Faransanci). Wadannan harsuna da na lissafa maka duk ina iya yin magana da su, musamman abin da ya shafi ciniki.
Aminiya: Wato dai kasuwanci ya kai ka wadannan kasashen?
Na ’Yalleman: E, Kasuwanci ya kai ni, amma na fi dadewa a kasar Kongo. Domin a tsakanin shekarun 1963 zuwa 1967 aka koro baki daga kasar Kongo, sai na dawo gida.
Aminiya: Ko Malam ya taba siyasa?
Na ’Yalleman: Tabbas na yi siyasar NEPU da NPC.
Aminiya: Ko an taba kama ka aka daure kamar yadda aka rika yi wa ’ya’yan jam’iyyar NEPU ta Malam Aminu Kano?
Na ’Yalleman: Ai mu ’ya’yan masu kudi ne, don haka ba a kama mu ba. Saboda attajirai da sarakuna a wancan lokacin bakinsu guda. Ka ga ma wannan gidan da ka ganni a cikinsa, asalinsa Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero ya bai wa mahaifina filin.
Aminiya: Ko ka yi takarar siyasa?
Na ’Yalleman: A’a, domin ban yi karatun da zan yi takara ba, amma na nuna matukar soyayya ga jam’iyyar PRP, da kuma aka rabu da Malam Aminu da Rimi sai na bi Malam. Wannan siyasar kuwa da ake yi a yanzu ba irin ta mu ba ce, domin duk da cewa ba ni da kudi ba zan iya zuwa ina hawa hayis(mota), ina binsu, wani ya ba ni Naira dubu ko kasa da haka. Mun dai bar wa yara ’yan baya su je su yi ta yi.
Aminiya: Ko za ka bayyana mana abokan fataucinka da gwagwrmayar rayuwa?
Na ’Yalleman: Akwai Alhaji Jibrin Baba da Sule Baba, duk mun zauna da su a kasar Kongo. Sai Abu Darma, wanda a faifan garmaho daya aka yi mana waka da shi; wakarsa a gaba, tawa kuwa aka yi ta a bayan faifan. Akwai su Umaru danduna da Sarki Labaran da Uwawu, wadanda akasarinsu an ji su a wakokin Shata
Aminiya: Ya ya aka yi kuka hadu da Shata?
Na ’Yalleman: Ai tun ina karami nike ta rokon Allah Ya sanya Shata ya yi mini waka. Na yi addu’a Allah Ya ba ni abin da zan bai wa Shata ya yi mini waka.
Aminiya: Ko burinka ya cika, wato addu’arka ta samu karbuwa?
Na ’Yalleman: E, domin Shata ya yi mini waka.
Aminiya: Wacce kyauta ka yi wa Shata ta burge shi har ya yi maka waka?
Na ’Yalleman: Gaskiyar lamari kudi ba su cika burge Shata ba, har ya yi wa mutum wata. Kai dai na dace. A lokacin da ya yi wa Alhaji Widi waka, sai na kara rikicewa da son lallai Shata ya yi mini waka, domin a gabanmu aka yi. A bikin G.M. Hamza na yi masa kyauta, inda ya yi mini waka a shekarar 1976. Na taba bai wa Shata Fam 20.
Aminiya: Wacce daukaka wakar Shata ta haifar maka?
Na ’Yalleman: Wakar shata ta sa sunana ya kai wurare da dama. Kuma ya kai mu wurare da dama, domin mun je Funtuwa tare da shi, inda muka samu shiga sosai. Kusan duk inda na je idan aka ce ga Liman Na ’Yalleman, sai ka ga mutane na kallona, suna son su ganni. Da kun tambaye ni halayyar Shata, da kun fahimci kowane irin mutum ne shi.
Aminiya: Ko za ka yi mana bayani kan halayyar Shata?
Na ’Yalleman: Shata mutumin kirki ne da ya san masoyinsa. Ba ya wasa da masoyinsa ko yana gaban Sarkin Daura idan ya hango ka sai ya taso. Shi ya fara kai ni gaban Sarkin Daura Alhaji Muhammadu Bashar da sauran manyan mutane. Kuma Shata yana da kyauta, domin sai da ya dawo yana bayar da kyauta ga wadanda ya yi wa waka, wadanda suka ba shi wani abu a da. Kai har ni ma.
Aminiya: Kana nufin ya dauki dawainiyarku daga baya?
Na ’Yalleman: A’a, ba dawainiyarmu ya dauka ba, amma dai idan muka hadu da shi, sai ya yi mana kyauta, musamman ma da muka dawo yanzu babu kudi kamar da. Kowa ya san yadda Umaru danduna ya rika bai wa Shata kudi, amma sai da Shata ya dawo shi yake bai wa Umaru danduna kudi.
Aminiya: Ko kana jin cewa akwai mawakin da ya fi Shata iya waka a mawakan Hausa na wannan zamanin?
Na ’Yalleman: Gaskiya ina jin babu mai hikima da basira irin tasa. Sannan duk wanda ya taso yana waka mafi yawanci in ba sa’a aka yi ba, to ka ba shi shekara biyu za ka ga an daina sonsa. Shi kuwa Shata har ya mutu ana sonsa. Kuma a lokacin da Shata yake raye, akwai wasan da zai yi sai ka ga mutum sama da dubu 10 sun zo kallonsa. Dangane da basirarsa, zan iya tunawa a cikin wakata ya kira ni “Gwandar dawa wa ke ba ki ruwa?” wato yana nufin a lokacin ina raba kudi, amma ba ni da uban gida a Kano.