Tun kafin jadawalin zabe na shirya takarata a 2019 – Ubaida Bello
“Tun gabanin Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da jadawalin gudanar da zaben 2019 a wannan mako, na riga na shirya tsab don tunkarar zaben a takarar dan majalisar dokokin Jihar Sakkwato, sai dai kawai fitarwar ta karamin kaimi.” Fitacciyar ‘yar siyasa kuma mace ‘yar takara kwaya daya tilo a Jihar […]

“Tun gabanin Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da jadawalin gudanar da zaben 2019 a wannan mako, na riga na shirya tsab don tunkarar zaben a takarar dan majalisar dokokin Jihar Sakkwato, sai dai kawai fitarwar ta karamin kaimi.”
Fitacciyar ‘yar siyasa kuma mace ‘yar takara kwaya daya tilo a Jihar Sokkwato, Hajiya Ubaida Bello ce ta bayyana haka a ranar Larabar da ta gabata a birnin jihar a shirye-shiyenta na fuskantar zabe mai zuwa.
“A Jihar Sakkwato akwai matukar bukatar samun mace wakiliya a majalisar dokokin jiha, don kowa ya san mata suna da rawar da za su taka ko ba komai za su taimaki ‘yan uwansu mata, domin ciwon mace na mace ne, kuma a halin yanzu kwamitin harkokin mata na majalisa namiji ke kula da shi, tamkar garin da babu matan da suka san abin da suke yi a haujin ilmi da zamantakewa. Don haka muka ga dacewar mu fito don samun sauyi mai alfanu” a cewar Ubaida.
Ta kara da cewar za ta yi tsaye ta kwato hakkin al’umma bisa ga tsarin da addini da al’ada suka amince don addininta ya ba ta damar kare kanta da neman hakki ba tare da wuce gona da iri ba. “wasu na cewa bai kamata mata su yi siyasa ba, to in haka ne su daina karbar rijista, su daina zabe tun da wadannan ma siyasa ce, gaskiya ba laifi ba ne na wakilci al’ummata, don mu mata zamu iya in an bamu dama”.
Hajiya Ubaida shugabar kungiyar sa kai da cigaba jama’a ta Hikima, ta ce siyasar mata abin da ke ci masu tuwo a kwarya bai fi sai sun kashe kudi a kira su ace masu su janye ba, su janye ba dadi gudun ka da a kira su marasa tarbiyya, amma bayan wannan ba sa jin tsoron komai don suna son a gyara siyasar ne duk wani mai kirki ya zo ya jagoranci jama’a a daina samun bara gurbi.
“wakilci nake son yi ba jagoranci ba, kuma a wannan kuduri babu gudu ba ja da baya, zan nemi kujerar ‘yar majilasar dokokin jihar Sakkwato mai wakiltar karamar hukumar Sakkwato ta Arewa ta daya da yarda za a ayyana na ci zabe a biyu ga watan Maris na 2019, don wakiltar jama’ata in da zasu samu romon dimukuradiyya ta bangarena kuma zan fatattaki bangar siyasa da maula ta hanyar fito da hanyoyin dogaro da kai da mutane za su amfana,” in ji Ubaida Bello