Tun lokacin mulkin Shagari nake sana’ar yankan farce – Muhammad Inusa
Malam Muhammadu Inusa wani dattijo je da ya shekara fiye da talatin yana sana’ar yankan farce wanda a cikinsa ne kuma ya samu rufin asirin da yake ciyar da iyalinsa da kuma daukar nauyin karatun ‘ya’yansa. A cikin wannan tattaunnawa da yayi da Aminiya ya bayyana irin rufin asirin da harkar yankan farce ta yi […]
Malam Muhammadu Inusa wani dattijo je da ya shekara fiye da talatin yana sana’ar yankan farce wanda a cikinsa ne kuma ya samu rufin asirin da yake ciyar da iyalinsa da kuma daukar nauyin karatun ‘ya’yansa. A cikin wannan tattaunnawa da yayi da Aminiya ya bayyana irin rufin asirin da harkar yankan farce ta yi masa a rayuwa.
Aminiya: ka farad a gabatar da kanka?
Sunana Muhammadu Inusa kuma sana’ata ita ce yankan farce. Ina zaune ne a garin Kafanchan.
Aminiya: Tun wane lokaci ka fara wannan sana’ar?
Da farko na fara ne da sayar da kaya a 1981 amma daga shekarar 1982 kuma na fara aikin yankan farce ka ga yanzu wajen shekara 35 da kenan.
Aminiya: Ko za ka fada mana bambamcin wannan sana’ar a da da kuma yanzu?
Gaskiya akwai domin a lokacin ka ga mu na yankan farce ne a sule uku in an bamu kudi mai yawa shi ne sule biyar, a lokacin mulkin Shagari ke nan
Aminiya: Da yawan mutane na raina irin wannan aikin ko za ka fada mana wanne irin rufin asiri ka samu da wannan aikin na yankan farce?
Gaskiya ne ka ga yanzu haka ni ina da gidana na kaina wanda na gina duk da dai ban gama aikin ginin ba duka a sanadiyyar wannan sana’ar. Bayan haka ina da ‘ya’ya guda tara wanda da wannan aikin duka na ke daukar dawainiyarsu. Na samu rufin asiri sosai da wannan aikin.
Aminiya: Wadanne irin matsaloli ne ku ke fuskanta a wannan sana’ar?
Da ya ke ka ga na dade ina wannan sana’ar to da yawa daga cikin kwastomomin da na ke yi wa aiki wasunsu ba sa nan. Misali lokacin da ake aikin hakar ma’adinin Kwaranda akwai baki da yawa da na ke yi wa aiki wanda a yanzu ba sa nan. Wasun su sun koma da yawa kuma sun rasu.
Aminiya: Yanzu wane kira za ka yi wa matasa don kama sana’a?
Babu shakka zama babu aikin yi shike haifar da mutuwar zuciya ka ga mutum ya fara tunanin yadda zai dauki kayan da ba na shi ba daga nan kuma in ba a yi sa’a ba mutum sai ya zarce da sace-sace. Don haka kiran da zaun yi wa matasa shine su tashi su rungumi sana’a kuma masu sana’a musamman irin tamu shine kada su raina duk irin kallon wulakanci da raini da za a rika yi maka kada ka damu su ci gaba da hakuri.
Aminiya: Menene burinka a halin yanzu?
Kowa ma yana so ya samu ci gaba a harkar da ya ke yi. Ni yanzu babban burin a shi ne in ga na kammala aikin gidan nan da na ke yi har in kai ga tarewa a ciki kuma tunda na kai wani lokaci na girma ka ga ba batun canza wani sana’a sai dai tunda ‘ya’yana akwai wadanda su ka girma za su iya rike kansu.
Aminiya: A karshe menene kiranka ga gwamnatoci kan tallafawa masu sana’a?
Gwamnati ta rika waiwayarmu tunda in ka duba yanzu kusan ko ina ana samun yawaitar masu shiga wannan aikin saboda albarkar da ke ciki don haka gwamnati ta rika la’akari da hakan kada ta raina irin gudummawar da za ta bayar. Wani zai ce to wane jari wannan sana’a ke bukata kuma wane irin taimako za a bamu. To ai idan aka bamu taimakon za mu iya sanya shi ta wata hanyar ko da ace noma ne muna yi muna aikinmu ka ga ba zai shafi aikin ba.