Tuna Baya: Tarihin Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa
Alhaji, Sir Abubakar Tafawa Balewa, dattijon nan da hotonsa ke jikin takardar Naira Biyar shi ne shugaban gwamnatin Najeriya na farko bayan samun ƴancin kai. Shi ne ya karɓi ragamar mulkin Najeriya daga hannun Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu a ranar 1 ga Oktoban 1960. Tsawon shekaru shida da ya yi a matsayin firaministan ƴantacciyar […]
Alhaji, Sir Abubakar Tafawa Balewa, dattijon nan da hotonsa ke jikin takardar Naira Biyar shi ne shugaban gwamnatin Najeriya na farko bayan samun ƴancin kai.
Shi ne ya karɓi ragamar mulkin Najeriya daga hannun Sarauniyar Ingila Elizabeth ta Biyu a ranar 1 ga Oktoban 1960.
Tsawon shekaru shida da ya yi a matsayin firaministan ƴantacciyar Najeriya ya dasa harsashin cigaban ƙasa da bunƙasa tattalin arziki.
Sai dai ya sha fama da rikice-rikicen siyasa da na ƙabilanci waɗanda daga ƙarshe suka jawo sojoji suka kashe shi a wani yunƙurin juyin mulki da bai nasara ba.
Shiga nan domin kallon bidiyon cikakken tarihinsa.