Tuna baya: Tarihin Umaru Musa Yar’Adua
Umaru Musa Ƴar’adua yi tsantseni da dukiyar al’umma, ya yafe wa ƴan ta’addar Niger Delta kuma ya ɗauki matakan mayar da Najeriya ɗaya daga cikin ƙasashe 20 da suka fi arziki a duniya.
Alhaji Umaru Musa Ƴar’adua shi ne shugaban ƙasar Najeriya na farar hula na farko da ya karɓi mulki daga hannun farar hula.
Ya yi gwamnan jihar Katsina tsawon shekaru takwas. Sannan ya riƙe shugabancin Najeriya tsawon shekaru uku.
- Tuna Baya: Tarihin Janar Ibrahim Babangida
- Tuna Baya: Tarihin Firaministan Najeriya Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa
Ya yi tsantseni da dukiyar al’umma, ya yafe wa ƴan ta’addar Niger Delta kuma ya ɗauki matakan mayar da Najeriya ɗaya daga cikin ƙasashe 20 da suka fi arziki a duniya.
Sai dai ya sha fama da rashin lafiya wacce ta tilasta masa tafiya jinya ƙasashen waje.
Bayan shekara uku ya na mulkin Najeriya ya rasu a fadar Aso Rock sanadiyyar cutar da ta addabe shi.
Amma har yanzu ana yabonsa kan matakan da ya fara ɗauka na tafiyar da mulkinsa.