Tuna Baya: Yadda al’amuran Arewa suka sukurkuce
A nan kusa da mu akwai abubuwa biyu da mutum zai gani ya san cewa da can mazaunan wannan yanki hamshakan manoma ne da makiyaya. Wani kangon katon siton ajiyar amfanin gona, wanda akalla zai dauki buhunhunan abin masarufi bila-adadin shi ne na farko.Abu na biyu kuma tankama-tankaman dakuna ne da aka labarta mana cewa […]
A nan kusa da mu akwai abubuwa biyu da mutum zai gani ya san cewa da can mazaunan wannan yanki hamshakan manoma ne da makiyaya.
Wani kangon katon siton ajiyar amfanin gona, wanda akalla zai dauki buhunhunan abin masarufi bila-adadin shi ne na farko.
Abu na biyu kuma tankama-tankaman dakuna ne da aka labarta mana cewa an gina su ne kawai don a rika kiwon kaji a ciki.
Abin takaici wancan sito yanzu ya zama mazaunin kara bayan an girbe amfanin gona da kaka, wato dai siton can ya samu sauyi daga wurin ajiyar kayan abincin da mutane ke ci zuwa na dabbobi, to ko wannan din ma da an ce rani ya yi za ka iske shi fayau!
Na biyun kuwa ya fi zama abin tausayi da jimami! Shi kam a halin da ake ciki ya koma kufai, sai dai duk wanda ya ji matsuwa ya zagaya ciki don sawake wa kansa, wato ya tashi daga sunansa na gidan kaji zuwa makewayi. Wannan ke nan a fannin noma da kiwon da muke tokabo da shi iyaye da kakanni; sai dai tarihi!
Ga shi kuma Allah Ya kawo mu karshen watan azumin Ramalanan 1435 bayan hijira. A irin wannan lokaci sarakunanmu masu alfarma da dimbin darajoji ke yin zagayen kasarsu, akalla na kwanaki biyu zuwa uku, musamman cikin birni. Zagayen na kara masu muhibba da cika fuska a idon duniya, yana yaukaka zumuncinsu da talakawansu, haka kuma shi ne silar da za ta sa su san matsalolin da ke baibaye a cikin garuruwansu. A yayin wannan zagaye suna caba ado da tufafin Hausawa; na Saraki, don adana tarihi. Zagayen na shajja’a al’umma wajen nuna kauna ga shuwagabanninsu, shi ne dai sila da ke sa na baya su sani tare da girmama tadodinsu. Yana fito da jaruntar masarautun Hausa ga sauran masu yi wa Hausawa kallon hadarin kaji. Wannan zagaye shi ake kira da ‘’Hawan Sallah!’’
Na samu wani labari, wai wani Baturen Ingila ne yake jin yadda ake hawan Sallah a kasar Hausa daga bakin takwarorinsa da suka taba gane wa idonsu, ya ji yadda suke kambama abin, shi kuwa sai ya sha alwashin zuwa don kashe kwarkwatar idonsa. Haka kuwa aka yi, Baturen nan ya kintaci ranar Sallah, sai ya yi wa Kano tsinke. Sarkin lokacin ya dora shi bisa doki, suka rankaya! Can sai ga tawagar ’yan hoto sun dakako gaban sarki don kwasar gaisuwa, Nasaranka ya saki baki galala yana ta kallon irin kasadar da suke. Haba wa! Ai ko da Mai Martaba ya lura da hakan, sai ya kyaftawa Sarkin ’yan taurin ido. Kafin ka ce kwabo, sai ya zaro wata gaya-wa-jini-na-wuce, ya nufo Nasara gadan-gadan! Da farko ya dauka abin na wasa ne, sai ya rika murmushi, ko da sarkin ’yan tauri ya karaso, sai ya dauki wani dan icce a kasa, ya fille shi fyat da wannan takobi. Nan fa Nasara ya tabbatar ashe karfe ne tsura. Bai tashi shan mamaki ba sai da ya ga wannan taliki ya bintsire idonsa, ya yi ta kwalba wannan takobi a ciki, sannan ya ga ya tattare fatar cikinsa ya, kanannade takobin a ciki, ya kira wani daga cikin yaransa ya ce ya ja. Sai ji kake kiiii! kamar karfe da karfe sun gamu; bambancin kawai babu tartsatsin wuta ne. Ya dai gama duk nune-nunensa na bajinta a gaban ‘Mai Jan Kunne.’ Shi kuwa wani lokacin sai dai ya kawar da kai, ko ya runtse ido; wai ba ya son ganin mutum ya yi mummunar cikawa.
Ba a tashi shan kallo ba sai da wannan dan hoto ya dirkaki dokin Nasara haikan! Tun Nasara na murmushi, har ta kai ga ya fara hade fuska, da dai ya ga abin kamar da gaske ne, sai ya fado daga kan doki ya dafe keya, kafa me na ci ban ba ki ba! Kun ga fa wannan ta faru ne ta dalilin Hawan Sallar da shi ma ke shirin zama tarihi, saboda matsalolin tsaron da suka zame mana tarnaki.
Haka kuma kowa ya kwana da sanin a duk masarauta ana samun dandazon jarumai da barada masu tumbe da iya kai kora. Na san ba za a taba mantawa da irin su danwaire ba, wanda ake wa kirari da “Gwanki Sha Bara!” Shi ma akwai wata hikaya tasa mai ban mamaki da ke nuna tsagwaron jarunta. Wai na ji an ce akwai wani lokaci da aka soki dansa da kibiya a ido, suna tsakar gwabza yaki, amma duk da haka yaron bai daina kai farmaki ba, sai ma ya karshe iccen kibiyar, don kar wani ya fisge ta kara masa azaba.
Da aka gama gumurzu ne sai aka zo don fitar masa da kibiyar, za a yi wasu ’yan dabaru sai ga Gwanki ya zo, ya ce a zare kibiyar, kuma idan yaron ya kuskura ya kifta wancan idon nasa daya, to shege ne, a yanka shi. Haka kuwa aka yi, yaro ya zama dan halas uwa da uba. Ka ji fa Sadaukan!
To ko wannan ma ina zaton sai dai tarihin a yau saboda son jikinmu da lalaci. Irin wadannan labaru na magabata a game da jajircewa da izza in aka yi ta ba ka, za ka tabbatar da cewa Bahaushe ya kai jarumi, tun da har Nasara ma na shakkunsa.
Da can Arewa kasa ce ta zaman lafiya da lumana; ko haki mutum ya karya ba daidai ba, za a tsawatar masa. Idan ban manta ba, na taba karanta wani rubutu da Farfesa Bunza ya yi a jaridar Aminiya, rubutun ya nuna tsantsar zaman lafiya da kaunar juna da badangalci da yakana irin na Bahaushe ga kula da karrama baki (Don haka Bahaushe ke cewa “Bakonka, Annabinka).’ Yanzu kuwa wancan zaman lafiya da kaunar baki namu wanda muke tinkaho da alfahari da shi ya zama tarihi!
Girmama juna da ganin kimar magabata wata babbar tadar Hausa/Fulani ce. Mutum dai ya duba yadda ake gaisuwa a fadar sarakunanmu. Kai a da in Basarake ya ce ka ciro masa wani sashe na jikinka, ko za ka mutu sai ka ciro, sannan ka yi godiya, duk don biyayya. Saraki kuwa sun fi kowa son kyautata wa talakawansu, ba su son hatsaniya, ba su kaunar tashin-tashina, komai kadan din ta. A nan ma na samu labarin wani Basarake a kasar Kano tun da dadewa, wanda ya kwantar da ballin talakawan wani gari da suka tayar a dalilin jangali, ba tare da an shaya daga ba; cikin ruwan sanyi. Anya kuwa irin hakan ma bai zama tarihi ba?
Idan kuwa duk wadancan abubuwa da wasunsu da dama sun zama tarihi a kasarmu ta Hausa, to me ya rage mana ke nan?
Hafiz ya aiko daga [email protected] <mailto:[email protected]>; (07060438556)