Tunani ko santi

Wata mata ce da mijinta ya samu kuxinsa sai ya sawo kaji aka yi farfesu. Daga cikin kajin akwai wani babban zakara, lokacin da suke cin farfesun, sai matar ta xauki cinyar zakara ta yaga, sai ta ce: “Hmmn, Allah sarki! Abin mamaki, xazu da rana zakara ya sare ni a qafa.” Sai mijin ya […]

Tunani ko santi
Tunani ko santi

Wata mata ce da mijinta ya samu kuxinsa sai ya sawo kaji aka yi farfesu. Daga cikin kajin akwai wani babban zakara, lokacin da suke cin farfesun, sai matar ta xauki cinyar zakara ta yaga, sai ta ce: “Hmmn, Allah sarki! Abin mamaki, xazu da rana zakara ya sare ni a qafa.” Sai mijin ya ce mata: “To, ai ke ma ga shi nan yanzu kina ramawa.” Sai ta ce: “Kai, ni ba fa santi nake yi ba.”

Daga Muhammad Lawal, Army Barracks Sakkwato, 08035975369