Tunanina da ra’ayina game da Malam Shekarau

Nata’ala Sambo Babi (Nasaba) 08063673656, [email protected] shi ne wakilin mujallar ‘Muryar Arewa.’ A matsayinsa na Bagizage a Sakkwato, ya yi nazari game da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, daga bisani kuma ya amayar da ra’ayinsa a kansa kamar haka:A bayyane yake a yau ba wani sashe ko bangare na rayuwar jama’a da za […]

Tunanina da ra’ayina game da Malam Shekarau
Tunanina da ra’ayina game da Malam Shekarau

Nata’ala Sambo Babi (Nasaba) 08063673656, [email protected] shi ne wakilin mujallar ‘Muryar Arewa.’ A matsayinsa na Bagizage a Sakkwato, ya yi nazari game da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, daga bisani kuma ya amayar da ra’ayinsa a kansa kamar haka:
A bayyane yake a yau ba wani sashe ko bangare na rayuwar jama’a da za a rasa wani jigo da ya tsere wa tsara, wanda ba iyawarsa ko hikimarsa ko dabararsa ne suka sa tauraruwarsa ta dushe hasken sauran taurari ba, sai dai iyawa da kuma iko irin na mabuwayin Sarkin da ke yin yadda ya so, a inda ya so, a kan wanda ya so, a lokacin da ya so, walau ana so, ko ba a so.
Kuma tabbas masu hikimar zance sun yi gaskiya da suke cewa, idan ana dara fitar da uwa ake yi. Shi ya sa har kullum, ake ci gaba da samun mutane da suka yi fice, suka yi zarra a fannonin rayuwar jama’a ta yau da kullum. Sai dai kuma, ita wannan daukaka, ba haja ba ce, ko wata riga da za a baje a kasuwa domin kowa ya je ya saya, ya saka. A’a, wannan baiwa ce ta min indallahi, kyauta ce ta Ubangiji, wanda cikin hikimarSa yake fitar da amale a kowane garken rakuma.
Shakka babu, a so shi ko a ki shi a farfajiyar siyasar duniyar yau, siyasa a siyasance ya yi wa tsara ratar da sai  dai su biyo baya, domin Allah Ya tarfa wa garinsa nono, kazalika zakaransa ya yi caran da aka jiwo amonsa a haujin siyasar akida, siyasar ci gaban jama’a. A haka babban abin lura shi ne, yana gudanar da siyasa ne a matakin sallama da salama, hasali ma ya yi hannun riga da siyasar gaba ko nunin yatsu.
Malam Ibrahim Shekarau Sardauan Kano, a duniyar siyasar yau ba ya bukatar kowace irin gabatarwa. Idan ana maganar zaratan ’yan siyasar da suka himmatu, suka jajirce suka kuma yi tsayuwar dakan kyautata jin dadi da walwalar al’ummarsu ta yadda jagorancin shekaru takwas da ya yi wa al’ummar Kanawan Dabo a jiya, miliyoyin al’umma ke ci gaba da morar dimbin ayyukansa na alheri da ya da sa a yau.
Shi ya sa a yau duk da ya shugabanci katafariyar Jihar Kano wadda ke cike da rudu da kwamacalar siyasa da mabambantan al’umma amma a yau da ya kwashe sama da shekau biyu da sauka a kan gadon mulki, al’umma na ci gaba da kewar rabuwa da gwamnatinsa mai adalci, wacce ta rungumi su.
Ko ba a fada ba an san cewar har kullum dai ginin da zai yi karko da inganci da tsawon kwana, ana dora shi ne a kan tubali mai inganci, wanda zai iya jimirin nauyi da sauye-sauyen yanayi. Haka lamarin yake a sauran al’amurran rayuwar  jama’a, domin dukkanin wata tafiya ta jama’a, ana yi mata kyakkyawan shiri ne. Da irin wannan shirin ne wasu suka ga shekaranjiya, suka ga jiya, har ga shi yau ma ana damawa da su, kuma da rashin irin wannan shirin ne wasu suka yi ta-leko-ta-koma.
Da wannan, za a iya fahimtar cewa, ko a lokacin da Malam ya yanke shawarar tsunduma kogin siyasa, tuni ya dade da fafe goransa, domin kuwa ya san inda aka fito, ya san inda ake, don haka yana da yakinin inda alkiblar ya kamata ta dosa  a gobe, domin ganin goben ta fi yau da jiya da ma shekaranjiya, sa’annan gata ko jibi, ta ginu a kan kyakkyawan tafarkin da goben ta shimfida. Ma’ana dai, ba hawan kawara ya yi wa lamurran siyasa ba, kamar yadda wasu ke yi wa lamarin haye.
Hausawa sun ce, idan ka ji wane ba banza ba.  A kan haka, kwarewa  da gogewar da ya yo guzuri daga fagen aikin gwamnati, inda ya shafe tsawon shekaru yana yi wa al’umma hidima, a fagen ilimi, su suka haskaka masa hanyar daidaita lamurra, don haka da wannan guzuri na maganin zazzakar tafiyar siyasar kasar nan ya shigo fagen siyasa a 2003. Da wannan guzurin ne ya samu nasarar  bai wa mara da kunya, da shi ne ya tabbatar da mafarkin da jama’a suka dade suna yi na samun shugabanci nagari, da shi ne har ila yau ya tabbatar wa duniya cewa sanin wurin bugu shi ne kira, domin ya magance kishirwa da yunwar rashin kyakkyawan shugabanci da suka dade suna zama kadangaren bakin tulu ga ci gaban jama’a. Ya kawo guguwar sauyi a fagen siyasa, ba wai ta Jihar Kano ba kurum, inda ya shafe shekaru takwas yana mulki a matsayin gwamna, a’a, har ma a matakin kasa baki daya, inda ya jaddada falsafar amfani da makamin siyasa domin inganta rayuwar jama’a. Ya sauya tunanin dubun dubatar wadanda ke yi wa shugabanci kallon wata kafa ta amfanar kai kurum, domin kuwa, ya assasa tasa tafiyar ne da akidar fifita muradun wadanda ake mulki a wajen aiwatar da duk wani abu da za a yi dominsu, wanda kuma zai amfane su.
Babban abin tarihin da ya kafa, na zamowa mutum na farko a kafatanin tarihin siyasar kasar nan, da ya jagoranci Jihar Kano sau biyu jere da juna, a matsayin gwamnan farar hula, sun isa su kawar da duk wata tababar mai tababa cewa, kwararren malamin ba wai kimiyyar lissafi kurum ya nakalta ba, har ma da kimiyyar tafiyar da lamurra mabambantan al’umma, ganin cewa Jihar Kano, ita ce jiha ta biyu mafi tarin yawan al’umma a kasar nan, wannan yana nufin, adalcin da zai gamsar da mutane irin wadannan, har su sake lamuncewa da damka amanarsu ga duk wani shugaba, ba abu ne da zai misaltu ba.
Ba zai zamo abin mamaki ko abin musantawa ba, idan aka kira shi babban jigo a siyasa, babban madugu uban tafiya, gando matarar ruwa, rimi kere itace.

Hidindimun Gizagawa na wannan makon:

A labarin farin ciki, Bagizage Safiyanu Abdul Yaro Gangari, Suleja-Jihar Neja (08169998464), za a daura masa aure ne a gobe Asabar da karfe biyu na rana. Za a hadu ne a garejin mota na Suleja.
Bagizage Sanusi CBN (08038320203) ya samu karuwar haihuwar mace a Talatar da ta gabata.
Muna rokon Allah Ya sanya wa auren albarka kuma ya albarkaci jaririyar CBN, Ya dayyaba mana zuri’a gaba daya, amin. – Gizago.
A labarin jajantawa kuwa, Allah Ya yi wa mijin Hajiya A’isha Lawan Tarauni (08034509554) rasuwa a makon day a gabata. Hajiyar dai ita ce Shugabar Mata Gizagawan Najeriya.
Muna rokon Allah Ya jikansa da rahama. Mu kuma da muka rage, Allah Ya ba mu ikon cikawa da ingantaccen imani, idan namu lokacin ya zo. Amin. – Gizago.
Ga sabbin Gizagawan da suka samu rijista:
1-Sanusi Nalandan Zawiyya Gusau, 08067791410 (GZG653ZMF). 2-Aminu Police Jangwarzo, 08026604448 (GZG654LGS). 3-Alhassan Mai Gidan Wanka, 08039422353 (GZG655LGS). 4-Musba Bakanike, 08060216595 (GZG656LGS).