Tunatarwa ga al’umma

Duk yadda mutun ya kai da buri da tausayi, alkawarin Allah ba ya canjawa; matukar dai al’umma suna aikata Zina/Luwadi/Madigo – Allah Zai jarrabe su da annobar MUTUWA (ta hanyar Cutuka, Rikice-rikice irin na Maitatsine, Zangon Kataf, Boko Haram da makamantansu). Matukar al’umma suna tauye ma’auni/algus – Allah Zai kwashe albarkar kasar (kamar yadda Nairar […]

Tunatarwa ga al’umma

Duk yadda mutun ya kai da buri da tausayi, alkawarin Allah ba ya canjawa; matukar dai al’umma suna aikata Zina/Luwadi/Madigo – Allah Zai jarrabe su da annobar MUTUWA (ta hanyar Cutuka, Rikice-rikice irin na Maitatsine, Zangon Kataf, Boko Haram da makamantansu).

Matukar al’umma suna tauye ma’auni/algus – Allah Zai kwashe albarkar kasar (kamar yadda Nairar mu take rushewa, duk abin da ka sayar, yawan kudin ba za su isa ka sayo kamarsa ba). Matukar al’umma ba sa cika alkawari – Makiyan mu za su rinjayemu. Matukar mawadatan cikin mu ba sa fitar da zakka kamar yadda Allah Ya yi umarni – za a yi fari ko yunwa (koda kowa yana da kudi wadatattu, sai a rasa abincin da za a saya, ko kuma abincin ya wadata a ko’ina, amma ya kasance mafi yawan mutane ba su da kudin saya).

Matukar bama yin Shari’a da Littafin Allah Mai Tsarki – Za mu shiga dimuwa (masu cin mushen kare da Jaki, su sha giya su bugu su rika yi mana doka da za a rika yi mana Shari’a/Hukunci da ita – Wa’iyazu Billah).

Saboda haka Annabi (SAW) Ya yi mana umarni: “Idan muka ga abu mara kyau – mu kawar da shi da hannun mu, idan ba mu da ikon yin hakan – sai mu yi hani da baki, idan ba mu da iko sai mu ki abin a zuci –  wannan kuwa shi ne mafi raunin Imani”. 

Wanda bai kamata ba bacin Allah Ya ba mu karfi da lafiya da Ilimi, mu gwammace mu zamo cikin masu raunin Imani ba. Bacin mun san wasu ne suke jawo wa wasu. Koda ni da ku ba ma’aikata laifukan, wasu da suke aikatawa sai su jawo mana annobar duk gaba dayanmu (shi ya sa Annabi SAW Ya ce mu hana), masu mulki su suke da ikon hanawa ta hanyar hukunta duk wanda ya aikata kowanne irin laifi, kamar yadda Allah Ya yi umarni aka samar da kotu da alkalai da kurkuku da jami’an tsaro da shugabanni, kuma ake biyan su daga Baitul Mali (kudin al’umma/gwamnati).

Babu wanda Allah Ya fi so irin Shugaba Adali, babu wanda Allah Ya fi ki irin Shugaba azzalumi. Sai ka ga wasu suna da’awar imani da son Annabi (SAW), amma suna Luwadi! kaunar Annabi (SAW) ba za ta hadu da yada fasadi a cikin al’umma ba!!! Masu ci da addini, ‘yan damfara, matsubbata da matsafa a yi hattara. Hukuncin Allah (SWT) yana nan tafe, kuma bayin Allah na kwarai suna nan a voye, duk lokacin da Allah Ya ara musu dama – karyar makaryata/azzalumai/fajirai/matsafa ta kare, sai sun raina kansu tun a nan duniya. 

Allah (SWT) shi ne ya ce: “Ya Haramta wa Kansa zalunci, Ya umarci dukkanin BayinSa muma kada mu yi zalunci”. Annabi (SAW) Ya gargade mu a kan abubuwa biyar (5) da na jero a sama (zina/luwadi/madigo ; tauye ma’auni ; rashin cika alkawari ; rashin fitar da zakka da rashin yin Shari’a da Littafin Allah Mai Tsarki). Duk wanda bai iya hana al’umma yin zina/luwadi/madigo ba – bai isa ya hana Allah Ya saukar musu da annobar mutuwa ba. Haka duk Gwamnatin data kasa hana Tauye Ma’auni/Algus ba za ta iya hana rushewar darajar Naira da sauran albarkatun kasa ba. Kamar yadda duk al’ummar da ba ta hanu da rashin cika alkawari ba – Makiyan su za su rinjaye su. Idan kuma aka kasa karvar zakka daga mawadata a bai wa wadanda Allah Ya ce a rika bawa – za a hadu da fari ko yunwa. Idan ba a yin Shari’a da Littafin Allah Mai Tsarki – za a shiga rudu. Allah Ya haliccemu ne don mu bauta maSa Shi Kadai, ba tare da abokin tarayya ba, Ya saukar mana da littafinSa kunshe da yadda za mu bauta masa da yadda za mu rayu da juna, Ya aiko Annabi, musamman wanda Ya koyar da mu yadda Allah Yake so mu bauta masa, da yadda za mu zauna da juna mu rayu kyakkyawar rayuwa, ba tare da kowanne irin zalunci ba. Kamar yadda aka halatta yin kotu da alkalai da kurkuku da jami’an tsaro da shugabanni masu zartar da hukunci, kamar yadda Annabi (SAW) Ya ce: “koda ‘yarSa Fadima ce aka samu ta yi sata, zai sa a yanke mata hannu”. Allah Ya sa mu gane, amin.

Alh. AbdulKarim daiyabu  

Shugaban Rundunar Adalci Ta Kasa

(Movement for Justice In Nigeria – MOJIN) 

Tsohon Shugaban kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Masana’antu, Ma’adanai da Harkokin Noma ta Jihar Kano 

(Kano Chamber of Commerce, Industry, Mines and Agriculture – KACCIMA) Tsohon Shugaban Jam’iyyar Alliance for Democracy (AD) na Kasa.

Tel: 08023106666 ; 08060116666

[email protected]