Tunatarwar da Sarkin Kano ya yi tana da matukar muhimmanci – Sarkin Hausawan Alaba Rago
Sarkin Kasuwar Alabar Rago a Jihar Legas, Alhaji Umaru Nagwaggo Sakkwato, ya ce, “ya kamata Shugabannin Najeriya su yi koyi da Maimartaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi 11 dangane da matakin hanzarta dawowa gida daga aikin Umara a kasar Saudiya da ya yi domin jajanta wa al’ummarsa da tunatar da su muhimmancin mika al’amuransu baki […]
Sarkin Kasuwar Alabar Rago a Jihar Legas, Alhaji Umaru Nagwaggo Sakkwato, ya ce, “ya kamata Shugabannin Najeriya su yi koyi da Maimartaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi 11 dangane da matakin hanzarta dawowa gida daga aikin Umara a kasar Saudiya da ya yi domin jajanta wa al’ummarsa da tunatar da su muhimmancin mika al’amuransu baki daya ga Allah (TWT).
“Irin haka ne ya kamaci shugabannin kasar nan su rinka yi a duk lokacin da wata masifa ko annoba ta fadawa jama’ar su. Bayyanar shugabanni a gaban jama’a a daidai lokacin da irin wannan al’amari ya auku, zai taimaka wajen rage radadin ciwo kuma zai karfafa wa jama’a guiwar yin aiki da shawarwarin da shugabanni suka ba su.” Inji Alhaji Umaru Nagwaggo Sakkwato wanda ya fadi haka a ranar talata cikin hira da wakilinmu ta wayar tarho.
“Kamar yadda Mai martaba Sarkin Kano, ya nemi al’ummar musulmi su koma ga Allah kuma su yi azumi na musamman na tsawon kwanaki 3 da yawaita rokon Allah madaukaki domin magance wannan al’amari, ina fata dukkanmu za mu kara sanya tsoron Allah a zukatanmu domin samun saukin rayuwa. Muddin shugabanni suka ci gaba da nuna rashin adalci su kuma masu kudi suka ki yin amfani da dukiyoyinsu wajen taimakon talakawa to, mu kuka da kanmu.” inji shi.
A kan batun ci gaba da aikata danyen aikin da ‘yan boko haram ke yi, sai Alhaji Umaru Nagwaggo yace, “zan iya amincewa da kalaman da Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo ya yi a sashen Hausa na rediyo BBC a ranar Litinin, cewa babu hannun gwamnati a kan al’amarin boko haram sai dai, sako-sakon da gwamnatin ta yi tun farko na kasa wadata sojoji da ‘yan sanda da manyan makamai shi ne ya haifar da halin da ake ciki da ‘yan boko haram suke samun nasara da kara kai hare-hare da suke kashe mutane kamar dabbobi, bayan wadanda aka raba su da muhallai da yanzu haka gwamnatin ta kasa wadata su da kayan abinci a sansanonin gudun hijira da suke zaune.”
A kan batun tsaron kai da Sarkin Kano ya shawarci al’ummomin kasa su yi, sai Alhaji Umaru Nagogo, ya ce, “wannan muhimmin abu ne da aka yi gadonsa kaka da kakanni a garuruwan Arewacin kasa, amma daga baya aka yi watsi da shi. Saboda haka ya kamata mu girmama wannan tunatarwa da Sarkin Kano yayi mana ta fannin dawo da binciken kwakwaf ga bakin mutane a cikin unguwanni da kafa kungiyoyin ‘yan sintiri da jama’a za su rinka daukar nauyin ayyukansu tsakani da Allah, domin kare kawunanmu daga miyagun iri.”
Sarkin Kasuwar Alabar Rago, ya jajantawa Mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar da dukkan Sarakunan Arewa dangane da irin halin ni ‘yasu da jama’a musulmi da kirista suka samu kansu a ciki musamman a Arewacin kasa. Ya mika irin wannan jaje ga Sarkin Hausawan Legas Alhaji Aminu Dogara da Sarkin Fulanin Legas da dukkan Sarakun Hausawa a jihohin kudu da ya nemi su bayar da ta su gudunmawar addu’o’in rokon Allah ya magance wannan al’amari kuma su tashi tsaye wajen lalubo hanyoyin kare kawunansu ba tare da sun shiga cikin rigar jami’an tsaro na kasa ba.