Tunawa da marigayi Janar Murtala Muhammad shekara 42 baya

A ranar 25 ga Yuli, 1975, a matsayinmu na daliban sakandare, mun tashi da safe cikin bacin rai da muka ji muryar Kanar Joseph Garba yana jawabin juyin mulkin da ya kawar da Janar Yakubu Gowon. Shugaban kasa mai saukin kai da fahimta, wanda daliban Najeriya ke kauna. Sai dai ba a jima ba sai […]

Tunawa da marigayi Janar Murtala Muhammad shekara 42 baya

A ranar 25 ga Yuli, 1975, a matsayinmu na daliban sakandare, mun tashi da safe cikin bacin rai da muka ji muryar Kanar Joseph Garba yana jawabin juyin mulkin da ya kawar da Janar Yakubu Gowon. Shugaban kasa mai saukin kai da fahimta, wanda daliban Najeriya ke kauna. Sai dai ba a jima ba sai yanayinmu ya canja, a lokacin da Gwamnatin Janar Murtala Muhammad ta fara aikinta. daliban Najeriya suna matukar kaunar Murtala Muhammad saboda tsaurin ra’ayinsa, musamman ma yadda ya tunkari mulkinsa kasa rika. 

A ranar Asabar, 14 ga Fabrairu, 1976, mun yi dandazo a kusa da akwatin rediyo, inda muka rika sauraron babban jami’in soja yana cewa: “Cikin jimami, Majalisar koli ta Mulkin Soja ke sanar da rasuwar Mai girma Shugaban kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Janar Murtala Muhammad.” Gaba dayanmu sai kwalla ke fita daga idanuwanmu. A yammacin ranar, sabon Shugaban kasa Laftana-Janar Obasanjo a jawabinsa, ya bayyana cewa: “A jiya ne aka harbe marigayi Shugaban kasa, a kan hanyarsa ta zuwa ofis. Mai tsaron lafiyarsa, Laftana Akinfehinwa da odalnsa da direbansa da suke tare da shi, duk an hallaka su.”

Murtala Muhammad ya yi mulkin Najeriya ne na tsawon kwanaki 200 kacal, amma wadannan kwanaki ne suka kasance jajirtattun kwanaki da aka gabatar da manyan ayyuka kuma aka dauki matakai mafiya tsauri. Haka kuma watanni shidan mulkin nan, su ne watanni mafiya tasiri da aka taba samun irinsu a tarihin mulkin Najeriya. A matsayinmu na dalibai, mun koyi kalamai masu nuna gaba dai-gaba dai daga bakin Shugaba Murtala, domin a kowane lokaci, an san shi da furta tsauraran kalamai, masu isar da sako cikin izza. Ko ta fannin saka kayansa na aiki, Murtala ya bambanta da sauran jami’an sojoji. A yayin da sauran ke yin zanzaro, shi rigarsa saman wando take saukowa, sannan ya matse ta da bel, sannan kuma hularsa mai ciko, saukowa take ta rufe idanuwansa. Wanda haka ke nuna cewa shi mutum ne mai daukar komai da muhimmanci, babu wasa a idanuwansa.

A lokacin da yake dalibta a Kwalejin Barewa, Zariya, an san shi da sunan Murtala Kurawa amma lokacin da aka zo bayyana sunansa a rediyo, a ranar 29 ga Yuli, 1975 a matsayin sabon Shugaban kasa, sai aka ambace shi da Birgediya Murtala Rufa’i Muhammad. Bayan kuma ’yan kwanaki, sai Hedikwatar koli ta bayyana cewa ya canja sunansa zuwa Murtala Ramat Muhammad, wato ya sakala sunan mahaifiyarsa a tsakiya, ta’adar da ba a saba da ita ba a Najeriya.

A ranar 30 ga Yuli, 1975 ce Murtala ya fara jawabi ga al’ummar kasa, inda ya rika bayani kamar da azazza. Ya rika cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin da’a ba, ba za ta lamunci cin zarafin aikin gwamnati ba. Watannin da suka biyo baya kuwa, kalmomi ne da suke ishara da bankade-bankaden almundahana da kore-koren bara-gurbin ma’aikata da wadanda suka tsufa a aiki. A wannan rana ce kuma ya bayyana kirkiro sababbin jihohi. A nan take ya kara ta da jijiyar wuya, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta dauki raini ba, ba za ta lamunci karya doka da oda ba.

A dai jawabin nasa na farko, Murtala ya bayyana jingine kidayar jama’a da aka gudanar a 1973, ya daga batun Bikin Kalankuwar Bakaken Fatar Duniya (FESTAC), sannan ya ambaci yi wa duk wani jami’in soja mai rike da mukamin sama da Birgediya ritaya. Haka kuma ya rushe Hukumar ICSA a Arewa da takwararta ESIALA ta Kudu. Daga bisani ne ya biyo baya da daukar matakan amshe Jami’ar Ahmadu Bello da kamfanin buga jaridun New Nigerian daga Gwamnatin Arewa da kuma amshe kashi 60 cikin 100 na hannun jarin jaridun Daily Times. 

A zamanin Murtala ne aka samu guguwar kore-kore daga aiki, inda aka yi wa wadansu ma’aikatan jihohi da na tarayya ritaya, wadansu kuwa da aka samu da laifin almundahana, aka kore su daga aiki. Sanadiyyar wannan al’amari, daga bisani wadansu tsofaffin ma’aikata sun nuna cewa shi ne ummulhaba’isin faruwa da hauhawar almundahana da rashawa da cin hanci a ma’aikatun Najeriya. Domin kuwa kamar yadda suka ce, tun daga lokacin ne ma’aikata suka shiga tsoro, domin rashin sanin tabbas da makomarsu a aiki.

A gwamnatin Gowon, an samu bukatu da yawa na son a kirkiro sababbin jihohi, don haka a zamanin Murtala, a ranar 3 ga Fabrairu, 1976, ya kirkiro sabbin jihohi 7, wadanda suka hada da Neja da Bauchi da Gongola da Benuwai da Ogun da Ondo da Imo sannan kuma ya canja wa Jihar Arewa ta Tsakiya suna zuwa Jihar Kaduna, Jihar Yamma ta Tsakiya kuma zuwa Bendel, ita kuma Jihar Kudu maso Gabas, ta koma Kuros Riba. A lokacinsa ne kuma aka yanke kudurin canja hedkwatar kasa daga Legas zuwa Abuja.

Murtala ya zuba wa idanunsa toka, ya kwace dukiyar tsofaffin shugabanni, inda ya bayyana cewa cikin gwamnonin soja da na farar hula da suka gabaci gwamnatinsa, guda biyu ne kadai suka kasance wankakku, da ba su azurta kansu da dukiyar gwamnati ba.

Alama ta nuna cewa Murtala bai kuduri aniyar dadewa a karagar mulki ba, domin kuwa ya shirya mayar da mulki a hannun ’yan siyasa bisa tsarin dimokuradiyya, inda nan take aka kafa Kwamitin Shirya Kundin Tsarin Mulki bisa shugabancin Mai Shari’a Chif Rotimi Williams. Wannan kwamiti ne kuwa ya samar da Kundin Tsarin Mulki na 1979.

Ana tuna Janar Murtala a matsayin dan kishin Afirka, musamman irin yadda ya yi tsayin daka wajen tabbatar da ’yancin kasar Angola.

A tarihin rayuwa da ayyukan Janar Murtala, ba za a mance Laftana-Kanar Bukar Suka Dimka ba, domin shi ne ya yi masa kwanton bauna, ya bindige shi a ranar 13 ga Fabrairu, 1976. Ya samu nasarar wannan ta’addanci ne saboda marigayin yana cikin mota daya ce kacal, ba kamar yanzu da shugabanni ke tafiya a jerin gwanon motocin sulke da ’yan rakiya ba. Haka Shugaba Murtala, a lokacin ba a Barikin Dodan, fadar gwamnati yake zaune ba. Wannan rana dai ta kasance mafi munin rana, a tarihin Najeriya.