Tunawa da marigayi Janar Murtala Muhammad shekaru 40 baya

  A gobe Asabar, 13-2-2016, shekaru 40 ke nan cur da mutuwar muzakkarin Shugaban kasa Janar Murtala Ramat Muhammad. Shahararren marubuci kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, MALAM MAHMUD JEGA ya yi dogon sharhi da nufin tunawa da shi a jaridar Turanci, Daily Trust ta ranar Litinin, 8-2-2016. Muhimmancin wannan shugaba da kuma […]

Tunawa da marigayi Janar Murtala Muhammad shekaru 40 baya
Tunawa da marigayi Janar Murtala Muhammad shekaru 40 baya

 

A gobe Asabar, 13-2-2016, shekaru 40 ke nan cur da mutuwar muzakkarin Shugaban kasa Janar Murtala Ramat Muhammad. Shahararren marubuci kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, MALAM MAHMUD JEGA ya yi dogon sharhi da nufin tunawa da shi a jaridar Turanci, Daily Trust ta ranar Litinin, 8-2-2016. Muhimmancin wannan shugaba da kuma dinbin abin tarihin da ke tattare da sharhin nan ya sanya BASHIR YAHUZA MALUMFASHI ya fassara, ya kawo shi nan. Ga abin da yake cewa:

A ranar 25 ga Yuli, 1975, a matsayinmu na daliban sakandare, mun tashi da safe cikin bacin rai, da muka ji muryar Kanar Joseph Garba yana jawabin juyin mulkin da ya kawar da Janar Yakubu Gowon. Shugaban kasa mai saukin kai da fahimta, wanda daliban Najeriya ke kauna. Sai dai ba a jima ba sai yanayinmu ya canza, a lokacin da Gwamnatin Janar Murtala ta fara aikinta. daliban Najeriya suna matukar kaunar Murtala Muhammad saboda tsaurin ra’ayinsa, musamman ma yadda ya tunkari mulkinsa kasa rika.
A ranar Asabar, 14 ga Fabrairu, 1976, mun yi dandazo a kusa da akwatin rediyo, inda muka rika sauraron babban jami’in soja yana cewa: “Cikin jimami, Majalisar koli ta Mulkin Soja ke sanar da rasuwar mai girma Shugaban kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya, Janar Murtala Muhammad.” Gaba dayanmu sai kwalla ke fita daga idanuwanmu. A yammacin ranar, sabon Shugaban kasa Laftanar-Janar Obasanjo a jawabinsa, ya bayyana cewa: “A jiya ne aka harbe marigayi Shugaban kasa, a kan hanyarsa ta zuwa ofis. Mai tsaron lafiyarsa, Laftanar Akinfehinwa da odalensa da direbansa da suke tare da shi, duk an halaka su.”
Murtala Muhammad ya yi mulkin Najeriya ne na tsawon kwanaki 200 kacal, amma wadannan kwanaki ne suka kasance jajirtattun kwanaki da aka gabatar da manyan ayyuka kuma aka dauki matakai mafi tsauri. Haka kuma watanni shidan mulkin nan, su ne watanni mafi tasiri da aka taba samun irinsu a tarihin mulkin Najeriya. A matsayinmu na dalibai, mun koyi kalamai masu nuna gada da-gaba dai daga bakin Shugaba Murtala, domin a kowane lokaci, an san shi da furta tsauraran kalamai, masu isar da sako cikin izza. Ko ta fannin saka kayansa na aiki, Murtala ya bambanta da sauran jami’an sojoji. A yayin da sauran ke yin zanzaro, shi rigarsa saman wando take saukowa, sannan ya matse ta da bel, sannan kuma hularsa mai ciko, saukowa take ta rufe idanuwansa. Wanda haka ke nuna cewa shi mutum ne mai daukar komai da muhimmanci, babu wasa a idanuwansa.
A lokacin da yake dalibta a Kwalejin Barewa, Zariya, an san shi da sunan Murtala Kurawa amma lokacin da aka zo bayyana sunansa a rediyo, a ranar 29 ga Yuli, 1975 a matsayin sabon Shugaban kasa, sai aka ambata Birgediya Murtala Rufa’i Muhammad. Bayan kuma ’yan kwanaki, sai Hedikwatar koli ta bayyana cewa ya canza sunansa zuwa Murtala Ramat Muhammad, watau ya sakala sunan mahaifiyarsa a tsakiya, ta’adar dab a a saba da ita ba a Najeriya.
A ranar 30 ga Yuli, 1975 ce Murtala ya fara jawabi ga al’ummar kasa, inda ya rika bayani kamar da azazza. Ya rika cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci rashin da’a ba, ba za ta lamunci cin zarafin mutuncin aikin gwamnati ba. Watannin da suka biyo baya kuwa, kalmomi ne da ke ishara da bankade-bankaden almundahana da kore-koren bara-gurbin ma’aikata da wadanda suka tsufa a aiki. A wannan rana ce kuma ya bayyana kirkiro sababbin jihohi. A nan take ya kara tada jijiyar wuya, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta dauki raini ba, ba za ta lamunci karya doka da oda ba.
A dai jawabin nasa na farko, Murtala ya bayyana hukuncin jingine kidayar jama’a da aka gudanar a 1973, ya daga batun Bikin Kalankuwar Bakaken Fatar Duniya (FESTAC), sannan ya ambata yi wa duk wani jami’in soja mai rike da mukamin sama da Birgediya ritaya. Haka kuma ya rushe hukumar ICSA a Arewa da takwararta ESIALA ta Kudu. Daga bisani ne ya biyo baya da daukar matakan amshe Jami’ar Ahmadu Bello da kamfanin jaridun New Nigeria daga Gwamnatin Arewa da kuma amshe kasha 60 cikin 100 na hannun jarin jaridun Daily Times.
A zamanin Murtala ne aka samu guguwar kore-kore daga aiki, inda aka yi wa wasu ma’aikatan jihohi da na tarayya ritaya, wasu kuwa da aka samu da laifin almundahana, aka kore su daga aiki. Sanadiyyar wannan al’amari, daga bisani wasu tsofaffin ma’aikatan sun nuna cewa shi ne ummulhaba’isin faruwa da hauhawar almundahana da rashawa da cin hanci a ma’aikatun Najeriya. Domin kuwa kamar yadda suka ce, tun daga lokacin ne ma’aikata suka shiga tsoro, domin rashin sanin tabbas da makomarsu a aiki.
A Gwamnatin Gowon, an samu bukatu da yawa na son a kirkiro sabbin jihohi, don haka a zamanin Murtala, a ranar 3 ga Fabrairu, 1976, ya kirkiro sabbin jihohi guda 7, wadanda suka hada da Neja da Bauchi da Gongola da Benuwai da Ogun da Ondo da Imo sannan kuma ya canja wa Jihar Arewa ta Tsakiya suna zuwa Jihar Kaduna, Jihar Yamma ta Tsakiya kuma zuwa Bendel, ita kuma Jihar Kudu maso Gabas, ta koma Kurosriba. A lokacinsa ne kuma aka yanke kudurin canja hedkwatar kasa daga Legas zuwa Abuja.
Murtala ya zuba wa idanunsa toka, ya kwace dukiyar tsofaffin shugabanni. Inda ya bayyana cewa cikin gwamnonon soja da na farar hula da suka gabaci gwamnatinsa, guda biyu ne kadai suka kasance wankakku, da ba su azurta kansu da dukiyar gwamnati ba.
Alama ta nuna cewa Murtala bai kuduri aniyar dadewa a karagar mulki ba, domin kuwa ya shirya mayar da mulki a hannun ’yan siyasa bisa tsarin dimokuradiyya. Inda nan take aka kafa Kwamitin Shirya Kundin Tsarin Mulki bisa shugabancin Mai Shari’a Chif Rotimi Williams. Wannan kwamiti ne kuwa ya samar da Kundin Tsarin Mulki na 1979.
Ana tuna Janar Murtala a matsayin dan kishin Afirika, musamman irin yadda ya yi tsayin daka wajen tabbatar da ’yancin kasar Angola.
A tarihin rayuwa da ayyukan Janar Murtala, ba za a mance Laftana-Kanar Bukar Suka Dimka ba, domin kuwa shi ne ya yi masa kwanton bauna, ya bindige shi a ranar 13 ga Fabrairu, 1976. Ya samu nasarar wannan ta’addanci ne a sanadiyyar marigayin yana cikin mota daya ce kacal, ba kamar yanzu ba da shugabanni ke tafiya a jerin gwanon motocin sulke da ’yan rakiya. Haka kuma, Shugaba Murtala, a lokacin nan ba a Barikin Dodan, fadar gwamnati yake zaune ba. Wannan rana dai ita ce ta kasance mafi munin rana, a tarihin Najeriya.