Tunawa da marigayi Shaikh Jafar Mahmud Adam
Wanda ya mutu bai sauri ba, wanda kuma ke raye bai yi jinkiri ba. Yau shekara takwas ke nan cur da wasu ballagazai, shashashai, wadanda suka kwashe shimfidarsu daga gaban Allah, suka zabi kaskanci, suka yi wa fitaccen malamin Musulunci, Shaikh Jafar Mahmud Adam kisan gilla. Tare da jimami da alhini, muke tuna wannan bawan […]
Wanda ya mutu bai sauri ba, wanda kuma ke raye bai yi jinkiri ba. Yau shekara takwas ke nan cur da wasu ballagazai, shashashai, wadanda suka kwashe shimfidarsu daga gaban Allah, suka zabi kaskanci, suka yi wa fitaccen malamin Musulunci, Shaikh Jafar Mahmud Adam kisan gilla. Tare da jimami da alhini, muke tuna wannan bawan Allah.
A ranar Juma’a, 13 ga watan Afirilun 2007, wasu ’yan bindiga da sanyin asuba, suka halarci masallacin da Shaikh Jafar yake limanci a Gadon kaya, birnin Kano, suka iske shi kuwa yana jagorancin mafificiyar Sallah mai daraja, Sallar Asuba, suka dirka masa dalmomi a jiki. Malamin yana cikin sujada ga Allah (SWA) ya yi shahada.
Babban abin takaici game da marigayi, ba wai yanayin mutuwarsa ba ne, a’a, asarar da aka dibga wa al’umma. A lokacin da malam ya rasu, lokaci ne da al’ummarmu take matukar bukatar muhimmin malami irinsa. Mutum ne shi da ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen karatu da karantarwa, fadaka da fadakarwa, ankara da ankararwa.
A lokacin da mafi yawan malaman addini suka zama makwadaita, shi Malam Jafar sai ya zama daban, ya kasance wanda ya san kansa kuma ya rike mutuncin kansa. A lokacin da wasu malaman suka siffatu da karkatar da mabiyansu saboda neman girma da kuma neman abin duniya, Malam Jafar sai ya kasance kaifi daya. Ya dora koyarwarsa bisa turba daya bisa hujja mai inganci ta Alkur’ani da Hadisi da Ijma’in malaman Sunna.
Wannan halayya ce ta ba shi damar kasancewa mutum jajirtacce, wanda ba ya kyuya ko kasala. A kullum yana cikin nazari da bincike, kuma ba ya furta duk wata fatawa, ba ya ambata kowane karatu, face yana da hujja da kwakkwarar madogara. Malami ne shi da ya kauce wa al’amuran kungiyanci. Idan gaskiya ta zo, ba ya shayin fadinta, ya Allah ga ’yan Izala ko ga ’yan Shi’a ko ga ’yan darika ko kuma ga Kirista da ma wadanda ba su da addini.
Allah Ya jikansa da gafara, a lokacin da ya fara ganin take-taken marigayi malamin ’yan Boko Haram, Malam Muhammad Yusuf, Shaikh Jafar ya yi iyaka kokarinsa wajen fadakar da shi, game da fitinar da yake neman kunnowa ga al’umma. Malamin ya yi kunnen uwar shegu da hudubar Jafar, sai ga shi kuwa abin da ya hango ya tabbata. A yau Boko Haram ya zama annoba ga al’umma.
Managarcin malami, marigayi Jafar ya haifar da sauyi mai girma ga al’umma, musamman ma matasa maza da mata, inda suka fahimci tsantsar abin da Musulunci ke koyarwa. Ta hanyar wa’azojinsa, al’umma sun karu sosai da nagartaccen ilimi. Matasa sun fahimta da tsantsar abin da ake nufi da rayuwa, sun gane tasirin neman ilimi, sun gane tasirin neman aiki ko sana’a, kamar yadda suka gane illar zaman kashe wando.
A karantarwarsa, Malam bai bar shugabanni ba, bai bar masu sarautar gargajiya ba, haka kuma bai bar ma’aikatan gwamnati ba, bai bar ’yan kasuwa ba, kamar kuma yadda bai bar talaka ba. Idan mai mulki ya kauce wa gaskiya, balo-balo zai fito ya fayyace masa illar haka. Ya yi yaki da azzaluman duniya, ya fayyace fari daga baki. Ya sassaita tunanin al’umma da hasken iliminsa.
Wani abin takaici shi ne, har zuwa yau din nan da aka cika shekara takwas cur da kisan gillar da aka yi wa malam, babu wani da aka kama daga cikin wadanda suka gudanar da aika-aikar. Kuma muna gadarar wai muna da jami’an tsaro, muna da shugabanni!
Sakonmu ga gafalallun da suka yi wannan aika-aika da duk wadanda suka daure musu gindi shi ne. Jinin Malam Jafar bai zuba a banza ba, kuma lallai bai mutu ba, yana nan a raye, domin kuwa dinbin almajiransa da dinbin ilimin da ya bari a doron kasa suna nan a raye kuma suna ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya. Malam Jafar bai mutu ba, a yanzu haka muna kyautata ingantaccen zaton yana can a makwancinsa na ni’ima. Ku kuwa makasa, mashaya jinin al’umma, na tabbata kuna cikin bakin ciki da kaskanci da wulakanci. A kullum addu’armu gare ku ita ce, Allah Ya dawwamar da ku cikin bakin ciki, a nan duniya da kuma gobe kiyama.
Malam Jafar Mahmud Adam dai an haife shi ne a ranar 12 ga watan Fabrairu, 1960, a garin Daura ta Jihar Katsina. Ya samu gurbin karatun gaba da firamare a 1984, inda ya shiga Gobernment Teachers’ College Gwale, wacce a yanzu ake kiranta da sunan Gobernment Arabic College Gwale. Ya kammala a 1988, daga nan ya samu gurbin ci gaba da karatu a Jami’ar Musulunci ta Madina a Saudiyya. Ya yi karatunsa a can na tsawon shekaru hudu, inda ya kammala a 1993.
Marigayi Malam Jafar ya kasance ina-ka-fito-nazari. Ina-za-ka-da’awa. Gaba dayan rayuwarsa ta kasance a hidimar Musulunci.
Muna rokon Allah Ya jikansa da gafara, Ya amshi shahadarsa, Ya ci gaba raya ayyukansa a fadin duniya. Allah Ya yi masa sakayyar zaluncin da aka shuka masa, Ya tona asirin makasansa da duk wadanda suka ba da goyon bayan haka ta tabbata. Allah Ka tada mana da magajinsa, wanda zai ci gaba da haskaka addininKa ga al’umma.
Malam Jafar Adam, muna tuna ka, muna yi maka addu’a a kullum. Allah Ya jikanka!