Tunawa da marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam
Wanda ya mutu bai sauri ba, wanda kuma ke raye bai yi jinkiri ba.Shekara 13 ke nan cur da wadansu ballagazai, shashashai, wadanda suka kwashe shimfidarsu daga gaban Allah, suka zabi kaskanci, suka yi wa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam kisan gilla. Tare da jimami da alhini, a yau GIZAGO (08065576011) ke tuna […]
Wanda ya mutu bai sauri ba, wanda kuma ke raye bai yi jinkiri ba.Shekara 13 ke nan cur da wadansu ballagazai, shashashai, wadanda suka kwashe shimfidarsu daga gaban Allah, suka zabi kaskanci, suka yi wa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam kisan gilla. Tare da jimami da alhini, a yau GIZAGO (08065576011) ke tuna wannan bawan Allah.
ranar Juma’a, 13 ga watan Afrilun 2007, wadansu ’yan bindiga da sanyin asuba, suka halarci masallacin da Sheikh Ja’afar Mahmud Adam yake limanci a Unguwar Dorayi, birnin Kano, suka iske shi yana jagorancin mafificiyar Sallah mai daraja, Sallar Asuba, suka dirka masa dalmomi a jiki. Malamin yana cikin sujada ga Allah (SWT) ya yi shahada.
Babban abin takaici game da lamarin, ba wai yanayin mutuwarsa ba ne, a’a, asarar da aka dibga ga al’umma. A lokacin da Malam ya rasu, lokaci ne da al’ummarmu take matukar bukatar muhimmin malami irinsa. Mutum ne shi da ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen karatu da karantarwa, fadaka da fadakarwa, ankara da ankararwa.
A lokacin da mafi yawan malaman addini suka zama makwadaita, shi Malam Ja’afar sai ya zama daban, ya kasance wanda ya san kansa kuma ya rike mutuncin kansa.
A lokacin da wadansu malaman suka siffantu da karkatar da mabiyansu saboda neman girma da neman abin duniya, Malam Ja’afar ya kasance kaifi daya. Ya dora koyarwarsa bisa turba daya, bisa hujja mai inganci ta Alkur’ani da Hadisi da Ijma’in Malaman Sunnah magabata.
Wannan hali ne ya ba shi damar kasancewa jajirtacce, wanda ba ya kyuya ko kasala. A kullum yana cikin nazari da bincike kuma ba ya furta wata fatawa ba ya ambata kowane karatu, face yana da hujja da kwakkwarar madogara. Malami ne da ya kauce wa al’amuran kungiyanci. Idan gaskiya ta zo, ba ya shayin fadinta, ya alla ga ’yan Izala ko ga ’yan Shi’a ko ga ’yan Darika ko kuma ga Kirista da ma wadanda ba su da addini.
Allah Ya jikansa da gafara, a lokacin da ya fara ganin take- taken marigayi shugaban ’yan Boko Haram, Malam Muhammad Yusuf, Sheikh Ja’afar ya yi iyaka kokarinsa wajen fadakar da shi, game da fitinar da yake neman kunnowa ga al’umma. Malamin ya yi kunnen uwar shegu da hudubar Ja’afar, sai ga shi kuwa abin da ya hango ya tabbata. A yau Kungiyar Boko Haram ta zama annoba ga al’umma.
Managarcin malami, marigayi Ja’afar ya haifar da sauyi mai girma ga al’umma, musamman ma ga matasa maza da mata, inda suka fahimci tsantsar abin da Musulunci ke koyarwa. Ta hanyar wa’azozinsa, al’umma sun karu sosai da nagartaccen ilimi kuma ana ci gaba da amfana.
Matasa sun fahimci tsantsar abin da ake nufi da rayuwa, sun gane tasirin neman ilimi, sun gane tasirin neman aiki ko sana’a, kamar yadda suka gane illar zaman kashe wando.
A karantarwarsa, Malam bai bar shugabanni ba, bai bar masu sarautar gargajiya ba, haka kuma bai bar ma’aikatan gwamnati ba, bai bar ’yan kasuwa ba, kamar yadda bai bar talaka ba. Idan mai mulki ya kauce wa gaskiya, balo- balo zai fito ya fayyace masa illar haka. Ya yi yaki da azzaluman duniya, ya fayyace fari daga baki.
Ya sassaita tunanin al’umma da hasken iliminsa.
Wani abin takaici shi ne, har zuwa yau din nan da aka cika shekara 13 da kisan gillar da aka yi wa Malam, babu wani da aka kama daga cikin wadanda suka gudanar da aika-aikar. Kuma muna gadarar wai muna da jami’an tsaro, muna da shugabanni!
Sakonmu ga gafalallun da suka yi wannan aika-aika da ma dukkan wadanda suka daure musu gindi shi ne, jinin Malam Ja’afar bai zuba a banza ba, kuma lallai bai mutu ba, yana nan a raye, domin kuwa dimbin almajiransa da dimbin ilimin da ya bari a doron kasa suna nan a raye kuma suna ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya. Malam Ja’afar bai mutu ba, a yanzu haka muna kyautata zaton yana a makwancinsa na ni’ima. Ku kuwa makasa, mashaya jinin al’umma, na tabbata kuna cikin bakin ciki da kaskanci da wulakanci. A kullum addu’armu gare ku ita ce, Allah Ya dawwamar da ku cikin bakin ciki, a nan duniya da kuma gobe Kiyama.
Malam Ja’afar Mahmud Adam an haife shi ne a ranar 12 ga Fabrairun 1960, a garin Daura ta Jihar Katsina. Ya samu gurbin karatun gaba da firamare a 1984, inda ya shiga Kwalejin Horar da Malamai ta Gwamnati da ke (GTC) Gwale, wacce a yanzu ake kiranta da Kwalejin Larabci ta Gwamnati (GAC), Gwale. Ya kammala a 1988, daga nan ya samu gurbin ci gaba da karatu a Jami’ar Musulunci ta Madina a Saudiyya. Ya yi karatunsa a can na tsawon shekara hudu, inda ya kammala a 1993.
Marigayi Malam Ja’afar ya kasance: “Ina-ka-fito-nazari, Ina-za-ka-da’awa.” Gaba dayan rayuwarsa ta kasance a hidimar Musulunci.
Muna rokon Allah Ya jikansa da gafara, Ya amshi shahadarsa, Ya ci gaba raya ayyukansa a fadin duniya. Allah Ya yi masa sakayyar zaluncin da aka shuka masa, Ya tona asirin makasansa da duk wadanda suka ba da goyon bayan haka ta tabbata. Allah Ka tada mana da magajinsa, wanda zai ci gaba da haskaka addininKa ga al’umma.
Malam Ja’afar Adam, muna tuna ka, muna yi maka addu’a a kullum. Allah Ya jikanka!