Tunde Onakoya: Ɗan Nijeriya ya kafa tarihi a wasan dara

An tara jimillar dala dubu $22,000 cikin awannin 20 da fara wasan.

Tunde Onakoya: Ɗan Nijeriya ya kafa tarihi a wasan dara

Wani zakaran dara na wasan Chess kuma ɗan Nijeriya, Tunde Onakoya ya buga wasan na tsawon awa 58 inda ya haura tarihin da aka kafa a baya na wanda ya fi daɗewa yana buga wasan chess ba tsayawa, na awa 56.

Sai dai kawo yanzu Kundin Bajinta na Guinness World Record bai tabbatar da wannan yunƙuri na Tunde ba, inda wasu lokutan yakan ɗauki Kundin makonni kafin ta tabbatar da sabon tarihin bajinta.

Tunde mai fafutukar koyar da ilimin yara ya buga dara na tsawon sa’o’i 58 ba tare da tsayawa ba a dandalin Times Square na birnin New York domin karya tarihin duniya na tsawon wasan chess mafi dadewa.

Tunde Onakoya, mai shekaru 29, yana fatan tara kuɗi dala miliyan 1 don ilimantar da yara a fadin Afirka.

Ya fafata wasan ne da Shawn Martinez, zakaran chess na Amurka, daidai da ka’idodin Guinness World Record cewa wajibi ne ’yan wasan biyu su yi duk wani ƙoƙari na zarta tarihin da aka kafa, inda za su ci gaba da fafata wasan har na tsawon lokacin.

A daidai ƙarfe 2 da rabi na safiyar Asabar ne Tunde ya haura awanni 58, inda hakan ke nufin ya haura tarihin da ake da shi a yanzu na buga chess ba tsayawa, na awa 56, da minti 9 da sakan 37, wanda a 2018 Hallvard Haug Flatebø da Sjur Ferkingstad daga Norway suka kafa.

Tunde na ta samun ƙaruwar magoya baya a intanet da ma dandalin da yake wasan, inda aka ji kiɗan Afirka na tashi don nishaɗantar da ‘yan kallo da magoya baya da suke tafi suna jinjina masa.

Yunƙurin kafa sabon tarihin bajintar don “tabbatar da burin miliyoyin yara ne a faɗin Afirka waɗanda ba sa iya zuwa makaranta,” cewar Tunde Onakoya, wanda shi ne ya kafa ƙungiyar sa-kai ta Chess in Slums Africa a shekarar 2018.

Ƙungiyar tana da burin tallafa wa ilimin aƙalla yara miliyan 1 a unguwannin marasa galihu a nahiyar Afirka.

Tunde ya faɗa ranar Alhamis bayan ya cika awanni 24 da fara wasan cewa, “Ina jin ƙarfi ɗari bisa ɗari a yanzu, saboda mutanena suna nan suna ba ni goyon baya da kaɗe-kaɗe.”

Kayan abincin da Tunde ke ci sun haɗa da: Ruwan sha, da shinkafa jollof, wadda sanannen girki ne na Yammacin Afirka.

Bayan duk awa ɗaya na buga wasa, Tunde da abokin karawarsa suna samun hutun minti biyar kacal.

Wani lokacin suna haɗe hutun inda Tunde ke amfani da shi wajen hira da ’yan Nijeriya da ’yan New York da ke ba shi ƙwarin gwiwa kuma yakan shiga ya yi rawa tare da su.

An tara jimillar dala dubu $22,000 cikin awannin 20 da fara wasan, in ji Taiwo Adeyemi, manajan Tunde Onakoya.