Tuni APC ta yi wa PDP kamfe-Bafarawa
Jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce jam’iyyar APC ba ta tsinana komai ba sai ma kamfe da ta yi wa PDP ta karbe gwamnati a zabe mai zuwa. Bafarawa ya ce amma ya zama wajibi jam’iyyar PDP ta yi gaskiya da rikon amana a babban taron jam’iyyar […]

Jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ya ce jam’iyyar APC ba ta tsinana komai ba sai ma kamfe da ta yi wa PDP ta karbe gwamnati a zabe mai zuwa.
Bafarawa ya ce amma ya zama wajibi jam’iyyar PDP ta yi gaskiya da rikon amana a babban taron jam’iyyar da za a yi a ranar tara ga watan disamba muddin tana so ta ci ribar hadin kanta.
Bafarawa wanda ya ziyarci Sakkwato ya ce PDP na kan hanyar samun nasara idan wadanda suke rike da ita suka yi abin da ya dace a wata mai zuwa.