Tuni ga Gwmanan Neja
Ina son yin tunin alkawarin da Gwmanan Neja ya yi wa al’ummar Rijau da Kontagora kan gyaran hanya da gada a lokacin da aka yi wata takaddama tsakajnin mahaifinsa da ya so tabbatar da ayyukan alheri,amma tdsohon Gwmanan Neja ya hana. Kyawun alkawari cikawa. A lokacin yakin neman zaben shekara ta dubu biyu da goma […]
Ina son yin tunin alkawarin da Gwmanan Neja ya yi wa al’ummar Rijau da Kontagora kan gyaran hanya da gada a lokacin da aka yi wata takaddama tsakajnin mahaifinsa da ya so tabbatar da ayyukan alheri,amma tdsohon Gwmanan Neja ya hana. Kyawun alkawari cikawa.
A lokacin yakin neman zaben shekara ta dubu biyu da goma sha biyar (2015), Mahaifin gwamnan jiharmu ta Neja Alhaji Sani Bello ya dauko ma’aikata domin gyaran wata gada da ta karye tsakanin hanyar Rijau Zuwa Kontagora gadar da ake cema GADAR LIYOJI, amma tsohon Gwamnan Jihar tamu ta Neja, wato Dokta Mu’azu Babangida Aliyu Talban Minna ya hana ayi aikin, inda ya nuna bacin ransa a kan babu wanda ya isa ya zo cikin jiharsa ya yi aiki a matsayinsa na gwamna. Nan take kamfani suka kwashe kayansu suka tafi.
A wannan lokacin Alhaji Sani Bello ya dauki alkawarin idan har dansa ya ci zabe a shekara ta 2015 to sun dauki alkawarin gyara hanyar RIJAU Zuwa KONTAGORA gaba daya ba ma gada ba. To da haka fa aka yi ta yi mana KAMFE da sunan wannan gadar, amma yau ga shi har an yi zabe an gama shekara ukku (3) ke nan Gwamna Abubakar Sani Bello na saman mulki, amma ba wani labari a kan alkawarin da suka dauka na gyaran wannan hanyar.
Don haka nake amfani da wannan damar wajen tunatar da mai girman gwamna kan alkawarin da suka daukar wa talakawan Rijau da Kontagora, domin alkawari kaya ne, kuma kowa ya yi da kyau zai ga da kyau; kan mage dai ya waye, daga karshe nake rokon Allah Subhanahu Wata’ala da ya sa Gwanan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello Lolo Ya ga wannan korafi nawa.
Actibist Nura Sani Rijau 08108291641
08026664213 Nura sani Rijau