Tunisia ta kori kocinta bayan wasan farko a Gasar Kofin Duniya

Rahotanni sun nuna cewa ya zama koci na uku a tarihin Gasar Kofin Duniya da aka kora yayin da gasar ke gudana.

Tunisia ta kori kocinta bayan wasan farko a Gasar Kofin Duniya

Ƙasar Tunisia ta sanar da raba gari da kocin tawagarta, Sabri Lamouchi, bayan rashin nasarar da tawagar ta yi a wasan farko na Gasar Kofin Duniya ta 2026.

Tawagar ta Carthage Eagles’ ta sha kashi da ci 5-1 a hannun Sweden a wasan da suka fafata da safiyar Litinin, lamarin da ya jefa tawagar cikin tsaka mai wuya tun daga farkon gasar.

Lamouchi, wanda ɗan asalin Faransa da Tunisiya ne, ya shafe watanni biyar kacal yana jan ragamar tawagar kafin hukuncin korarsa.

Rahotanni sun nuna cewa ya zama koci na uku a tarihin Gasar Kofin Duniya da aka kora yayin da gasar ke gudana, bayan sakamakon da ya kasa gamsar da mahukuntan ƙwallon ƙafar ƙasar.

Ana sa ran hukumar ƙwallon ƙafar Tunisiya za ta sanar da wanda zai jagoranci tawagar gabanin wasanta na gaba a gasar.

Idan ba a manta ba, Tunisia ta sallami tsohon kocin tawagar ƙasar, Sami Trabelsi, bayan gaza tsallake zagayen ’yan 16 a Gasar Kofin Afirka na AFCON a watan Janairun bana.