Tunisiya ta ba Hukumar CAF hakuri

A ranar Talatar da ta gabata ne kasar Tunisiya ta aika da sakon ban hakuri ga Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka watau CAF. Ta bayar da hakurin ne a kan zargin da ta yi wa Hukumar na yi mata coge a gasar cin kofin Afirka da ya gudana a Ekuatorial Guinea, inda ta zargi […]

Tunisiya ta ba Hukumar CAF hakuri
Tunisiya ta ba Hukumar CAF hakuri

A ranar Talatar da ta gabata ne kasar Tunisiya ta aika da sakon ban hakuri ga Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka watau CAF. Ta bayar da hakurin ne a kan zargin da ta yi wa Hukumar na yi mata coge a gasar cin kofin Afirka da ya gudana a Ekuatorial Guinea, inda ta zargi alkalin wasa da laifin hada baki da CAF kuma aka yi mata coge a wasan kwata-fainal da ta buga da mai masaukin baki Ekuatorial Guinea.

Da wannan afuwa da kasar ta nema, Hukumar CAF za ta amince a fafata da kasar a gasar cin kofin Afirka da zai gudana a shekarar 2017.
Sai dai Hukumar ta ce tilas ne Tunisiya ta biya tarar da ta yi mata na Dala dubu 50 ko Fam dubu 33 da ya yi daidai da Naira miliyan 11 da dubu 253. Hukumar ta ce kasar za ta biya tarar ce saboda rashin da’ar da wasu daga cikin ’yan kwallonta suka nuna jim kadan bayan an tashi daga wasan inda suka zagi wasu daga cikin jami’an Hukumar tare kuma da lalata wasu daga cikin kayayyaki a filin wasan.