‘Tunkiya da karen daji’
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana yi wa iyaye ladabi da biyayya daidai gwargwado. A yau na kawo muku labarin Tunkiya da Karen daji Labarin na qunshe da yadda Manyan gobe yakamata su riqa jin maganar iyayensu. A sha karatu lafiya: Akwai wata tunkiya da suka […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana yi wa iyaye ladabi da biyayya daidai gwargwado. A yau na kawo muku labarin Tunkiya da Karen daji Labarin na qunshe da yadda Manyan gobe yakamata su riqa jin maganar iyayensu. A sha karatu lafiya:
Akwai wata tunkiya da suka fita neman abinci a daji tare da mai kiwonsu. Kullum idan sun fita kiwo, sai ta yi ta mamakin dalilin da ya sa manomi ba ya son su qetare wani fili. Ita ko tana ganin cewa harawar dake nesa za ta fi daxi tunda ba a zuwa wajen kiwo.
Sai rannan ta faki idon ‘yanuwanta da manomi ta je inda aka hana su zuwa kiwo. Isarta wurin ke da wuya sai ta haxu da Karen Daji. Nan da nan Kare ya nuna ya samu abinci. Sai tunkiya ta tsorata. Can sai ta hango inuwar zomo, sai ta kira zomo don ya taimaka mata.
Jin hakan sai ta ba karen daji dariya. Ya ce ai zomo qaramin alhaki ne domin shi kanshi ai bai tsira daga halaka b.
Sai zomo ya ce lallai zancen ka haka yake amma bari in duba na ga ko babu mafarauta a kusa, don za su iya zuwa su kashe ka. Sai karen daji ya ce yana jiransa ya je ya dawo.
Da zomo ya bar wurin sai ya samu takarda da alqalami ya yi rubutu ya ninke. Karen daji na ganinsa sai ya ce ka haxu da su? Ya ce bai ga kowa ba amma ya yi tsintuwar wasiqa. Karen daji ya ce ya karanta masa saboda shi bai iya karatu ba.
Karen daji ya ce saqo daga fadar sarki, A kan cewa ana neman fatar karen daji domin yi wa sarki riga. An samu qwata 74 saura xaya ake buqata don a cika su zama 75. Jin hakan sai Karen daji ya ruga a guje domin ya tsira da ransa. Daga nan sai tunkiya ta gode wa zomo a kan dabarar da ya yi har ya kuvutar da ita daga wajen Karen Daji. Daga nan zomo ya gargaxe ta cewa kada ta sake zuwa wurin da aka hana ta.