Tunkiya mafi tsufa a duniya ta cika shekara 25

An yi ittifakin tinkiyar ta fi kowacce tsufa a duniya

Tunkiya mafi tsufa a duniya ta cika shekara 25

Tinkiya da ake jin ta fi kowace tsufa a duniya

Wata tunkiya mai shekara 25 a duniya ta wasu ma’aurata a kasar New Zealand, ka iya zama mafi tsufa a duniya.

Vicki da Aled Cordier na Wainuiomata da ke yankin Tsibirin Wellington na Arewacin Tsibirin New Zealand sun ce tunkiyarsu mai suna Wainui da aka haifa ranar 2, ga Janairun 1998, wacce kuma ke zaune tare da su tun shekarar 2002, ita ce tunkiya mafi tsufa a duniya a yanzu.

Ma’auratan sun nemi a sa tunkiyar a cikin Kundin Tarihi na (Guinness) mai bayar da bayanan abubuwan ban mamaki na duniya.

Tunkiyar da take rike da wannan matsayi a yanzu ita ce Mananita, wacce take da shekara 24 da kwana 320 a duniya a lokacin da aka tantance shekarunta a watan Nuwamban 2021.

Ma’auratan sun ce sun nemi wannan matsayi ne saboda sun kasa tantance ko Mananita mai rike da matsayin na raye ko ta mutu. Ma’aurartan sun ce tunkiya Wainui na nan da ranta kuma cikin koshin lafiya.

“Tana samun kulawa. Tana da rigar kwat da ake sa mata a kowane dare. Kuma tana cin karin kumallonta da abincin dare a-kai-a-kai. Tana cikin koshin lafiya in ban da idanunta, wanda ya yi dan rauni ta fuskar gani a halin yanzu,” in ji Vicki a hirarta da newshub.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

Tags