Tunkiyar da aka haifa da qafafuwa biyar da rabi
Wata tunkiya ta haifi tunkiya mai qafafu biyar da rabi a gidan gona na ‘Lodge House farm’ a Unguwar Cornsay da ke Qaramar hukumar Durham a tsibirin Texel na qasar Neitherland. Angie Jewitt wacce ta mallaki tunkiyar ta ce, tana fatan ’yar tunkiyarta ta rayu a yadda aka halicce ta. Ta yanke shawarar ware tunkiyar […]
Wata tunkiya ta haifi tunkiya mai qafafu biyar da rabi a gidan gona na ‘Lodge House farm’ a Unguwar Cornsay da ke Qaramar hukumar Durham a tsibirin Texel na qasar Neitherland.
Angie Jewitt wacce ta mallaki tunkiyar ta ce, tana fatan ’yar tunkiyarta ta rayu a yadda aka halicce ta. Ta yanke shawarar ware tunkiyar da aka haifa daga cikin sauran tumakanta don ba ta lura ta musamman.
Ana iya haihuwar tunkiya mai qafafu biyar ne sau xaya a cikin miliyan na haihuwar dabbobi da ake yi a Ingila. Haihuwar wannan tunkiyar mai qafafu biyar da rabi ya zama abin al’ajabi. Qafa ta biyar ta kasance kamar sauran qafafu huxu yayin da rabin ta xangale a gefen jikinta.
Qaruwar qafafun tunkiyar bai hana ta yin tafiya da sauri kamar sauran tumakai ba. Kuma duk da irin halittar da aka haifi ’yar tunkiyar da ita ba ta hana ta kuzari ba.
A cewar likitocin dabbobi ba a buqatar yi wa tunkiyar mai qafafu biyar da rabi tiyata don samun cikakkiyar lafiya.
Angie Jewitt ta ce, tana fata qarin qafafun tunkiyar ba zai yi ma ta illa ba, a cewar Jewitt yanzu haka akwai alamun qoshin lafiya ga tunkiyar abin da yake faranta mata rai.