Tunusiya za ta gina katanga tsakanin ta da Libya
A shekaranjiya Laraba ne mahukunta a kasar Tunusiya suka bayyana aniyyarsu ta gina doguwar katanga a kan iyakar kasar da kasar Libya domin magance tsallakawar masu tayar da kayar-baya zuwa cikin kasarta. Firaministan Tunusiya, Habib Essid, ya ce katangar za ta kai tsawon kilomita 160 kuma za a kammala ginin a karshen shekarar bana.Habib Essid […]
A shekaranjiya Laraba ne mahukunta a kasar Tunusiya suka bayyana aniyyarsu ta gina doguwar katanga a kan iyakar kasar da kasar Libya domin magance tsallakawar masu tayar da kayar-baya zuwa cikin kasarta.
Firaministan Tunusiya, Habib Essid, ya ce katangar za ta kai tsawon kilomita 160 kuma za a kammala ginin a karshen shekarar bana.
Habib Essid ya bayar da sanarwar ce a lokacin da yake jawabi a gidan talabijin din kasar a kan matakan da yake dauka domin tunkarar matsalar masu tayar-da-kayar-baya bayan kisan da wani dan ta’adda da ke da alaka da kungiyar IS ya yi wa mutane 38 a birnin Sousse a karshen watan jiya.
Ana zargin cewa dan ta’addar ya samu horo ne a wajen ‘yan kungiyar ta IS reshen kasar Libya. A makon jiya ne faraministan ya ce, an tabbatar da cewa dan ta’adda ya samu horonsa ne daga kungiyar Ansar al-Sharia da ke Libyan. An dai kama mutum takwas wadanda ake zargin suna alaka da wanda ya kai harin. Kuma gwamnatin kasar ta ce ta bankado yadda aka kitsa harin. Mahukunta sun kara tsaurara tsaro a kasar, inda aka ake da dakaru akalla guda 1,400 zuwa otel-otel da kuma gabar teku.
A kwanaki masu zuwa, ana sa ran cewa gwamnatin kasar ta sanya hannu akan wata doka yaki da ta’addanci, wadda take gaban majalisar dokokin kasar tun bara.