Tura ta kai bango

Abu kamar wasa ga shi nan zaman lafiya da kwanciyar hankali sun gagari al’ummomin yankin Arewacin kasar nan. Tun jama’a na zama cikin dar-dar, har sai da ta kai suna barci da ido daya a bude don gudun abin da zai je, ya zo. A yanzu ma ya zamanto ma wasu tilas su bar muhallansu, […]

Tura ta kai bango
Tura ta kai bango

Abu kamar wasa ga shi nan zaman lafiya da kwanciyar hankali sun gagari al’ummomin yankin Arewacin kasar nan. Tun jama’a na zama cikin dar-dar, har sai da ta kai suna barci da ido daya a bude don gudun abin da zai je, ya zo. A yanzu ma ya zamanto ma wasu tilas su bar muhallansu, su kuma gudu su bar ladansu, su shiga uwa duniya, zuwa wuraren da za su zauna cikin kunci da matsin rayuwa, cike da bakin cikin da bakar wahala ke hadasawa, sa’anan kuma babu wani mai kawo musu dauki ko wata hukuma mai agazawa. Ta haka ne wasu suka marmace, wasu kuma suka jikkata sakamakon tozartawar da wasu ‘yan ta’adda ke yi musu da sunan addini.
Abin takaici game da haka shi ne yadda gwamnatin da ya kamata ta kare jama’arta daga fadawa cikin irin wannan mawuyacin yanayin babu abin da take yi don kawo karshen wannan mummunan lamari, hasali ma  tana ji, tana gani, ‘yan ta’addan ke kwakkwace manyan garuruwa a jihohi ukun da da ta’addancin ya fi kamari, kuma maimakon askarawa su tabuka don korarsu da kuma kare wuraren jama’a sai arcewa suke yi, suna yar da makamansu, ana bin su kamar wasu gafiyoyi, ana bubbugewa, ko kakkamewa.
Ganin yadda askarawan Najeriya suka gaza wajen nuna jarumtaka don kai dauki  ga jama’ansu da suka lashi takobin karewa, sai mafarauta da kuma maharba, maza da mata, suka yi ta sun gumo bindigar toka, suna rarumo gwalmi da kulake, wasu ma har da adduna, suka yi kukan kura, suka farma ‘yan ta’addan, aka yi kare-jini-biri-jini, har sai da suka fatattake su daga wasu wuraren da suka yi kaka-gida, suna ta cin karensu ba babbaka. Hakan ya sa ‘yan ta’addan sun kara bazama don halaka jama’an da suka yi ta razanawa, suna firgiciewa, har suka yi ta garzayawa cikin rukukin dazuzzuka don tsira da ransu. Dangane da haka ne jama’ar  da aka yi ta fafara suka fara sukewa, suna hakura da irin kaddarar da ta afka musu, aka yi ta mutsuke su tamkar kiyashi.
Dangane da haka ne wasu suka fara turzawa, suna jajircewa, suna fuskantar masifar da ke dumfarowa, suka daina gudu ko ja-da-baya, suka tsaya aka yi ta zube-ban-kwaryata da ‘yan ta’addan. Hakan ya zamanto musu wajibi, domin tura ta rigaya ta kai bango, babu inda za su, illa su tsaya su yi fadan ceton rai. Ana cikin haka ne sai Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu ya kara karfafa musu gwiwa, sa’ilin da ya bukaci kowa a kasar nan, musamman ma a yankin Arewa da ya tashi haikan don kare kansa, saboda tsira daga wulakancin marasa mutunci da tsoron Allah, masu yi wa mutane yankan rago ko na akuya a banza. Sarki Sanusi  ya ce hakan shi ne mafi a’ala a gare su maimakon dogaro da askarawan gwamnati wadanda ke  yin takansu  idan sun yi kicibis da ‘yan ta’addan, suna rantawa a na kare, bayan sun yar da bindigoginsu.
Haka nan ita ma kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta nanata irin wannan tsokaci na Sarki Sanusi, yayin da Babban Sakatarenta, Dr Khalid Abdullahi Aliyu ya bayyana wa manema labarai a Kaduna cewa bai kamata jama’a su yi kasake, suna jiran sojojin da ‘yan ta’adda suka rigaya suka razana ba, domin kuwa ko su ma  ba su iya kare kansu daga harin da ake kai masu, balle su yi wani abin-a-zo-a-gani wajen ceton jama’ar da ba su iya kare kawunansu.
Wannan masifar da ta zame tamkar cin kwan makauniya, ta addabi kowa da kowa, domin kuwa ta mayar da yankin Arewa filin daga, ta kuma daidaita al’ummomin cikinta, ta gurgunta harkokin tattalin arzikinta, sa’annan kuma ta janyo koma-bayan da sai an yi shekaru fiye da shirin ba a wartsake ba. Dukkan kokarin da aka sha yi don shawo kan masifun da suka yi ta afkuwa sun ci tura, hasali ma hakan wata masifar, sabuwa fil, ya kara hadasawa, domin kuwa jama’ar da ake yi dominsu suna ta yin kuka da sojojin da aka tura su kare mutuncinsu da dukiyarsu da kuma mutuncinsu, domin maimakon su taimaka su ne ke kara takura wa fararen hula, suna muzguna musu da azabtar da su, babu gairan balle dan dalili. Har ma ta kai jama’a sun fi gwammacewa su fuskanci kaskanci da wulakancin ‘yan ta’adda, domin hakan ya fi musu sauki daga ukubar da suke fuskanta a hannun askawaran Najeriya. Sa’annan kuma hakan na daga cikin dalilan da suka kara ruruta wutar rikici a yankin Arewa-maso-Gabas da kuma kawo rashin ingantaccen yanayin tsaro.
Wannan abin takaici ba a yankin Arewa-maso-Gabas kadai ya tsaya ba, har ma da yankin Arewa-maso-Yamma, inda ake tafka ta’asa daidai da wadanda ke afkuwa a inda ta’addancin ya fi kamari. ‘Yan bindiga sun hana kowa sakat, sun buwaye su da sace-sace da kashe-kashe da  yi wa mata fyade, kuma a kullum sai sun aikata muggan kaba’irai.  Cikin ruwan sanyi aka mayar da Arewa tamkar tsumma makunsar cuta, aka jefa jama’ar cikinta cikin halin kaka-ni-ka-yi, kuma bisa ga dukkan alamu babu wata mafita cikin dan kankanen lokaci, sai an yi da gaske. Hanyar tsira daga irin wadannan masifun shi ne zama cikin shirin ko-ta-kwana da niyyar kare kai daga a makiyan da askarawan gwamnati suka kasa magancewa. Ashe ke nan fadakarwar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi da Jama’atu Nasril-Islam suka yi abin dubawa ne, a yi amfani da su, idan dai jama’a ba suna so a biyo su har cikin uwar dakunansu ne ba, a yi masu kisan mummuke. An ce idan duka ya yi yawa na kai ake karewa.