Tura ta kai bango: Ku sayi matatar maina —Dangote ga NNPC
Alhaji Aliko Dangote ya nemi Kamfanin NNPCL ya zo ya saye matatar tasa ce cikin bacin rai da takaici
Shugaban Matatar Man Fetur ta Dangote kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya bukaci Kamfanin Mai na kasa (NNPCL) ya zo saye matatar mansa, wadda ita ce ta biyu mafi girma a duniya, a wani abu da ake ganin kamar an kai shi bango ne a kan matatar.
Alhaji Aliko Dangote ya nemi Kamfanin NNPCL ya zo ya saye matatar tasa ce cikin bacin rai da takaici, kan dambarwar da ta kunno kai a kan matatar a tsakaninsa da hukumomin kula da bangaren mai na Nijeriya.
Wannan dambarwa ta hana matatar samun danyen man da take bukata domin fara samar da tataccen man fetur a kasuwa.
A makon jiya Alhaji Ailko Dangote ya yi zargin cewa wasu miyagu a Nijeriya da kasashen waje sun sha yin kokarin ganin matatar tasa ba ta fara aiki ba.
- Shugaban Gabon ya gayyaci Dangote ya kafa masana’antun taki da siminti a kasarsa
- Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin tallafin karatun ɗaliban da ke ƙetare
Bayan ’yan kwanaki sai Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta yi zargin cewa Matatar Dangote tana samar da mai marar inganci idan aka kwatanta da na kasashen waje.
Babban Shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, ya yi zargin cewa ingancin man dizel da matatar take samarwa a ganinsa ya yi kasa da wanda ake samarwa a kasashen waje, yana mai gargadin cewa Nijeriya ba za ta dogara da Matatar Dangote kadai ba wajen samar da mai.
Ya kuma ce matatar ba ta da cikakken lasisin fara aiki a kasar nan.
Ahmed ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Gwamnati da ke Abuja ranar Alhamis ta makon jiya.
Ya kuma musanta zargin da ake yi cewa hukumar na yunkurin durkusar da ayyukan matatar mai zaman kanta saboda karancin danyen mai daga kamfanonin mai na duniya da ke Nijeriya.
A wata hira ta musamman da ya yi wa jaridar Intanet ta PREMIUM TIMES, attajirin Afirkan ya ce: “Ya kamata Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sayi matatar man tawa, ya tafiyar da ita ta yadda zai iya.
“Amma su ce wai ina kaka-gida, wannan ba adalci ba ne. Idan suka sayi matatar, shi ke nan maganar zargin kaka-gida ta kare.”
A shekarar 2023 aka kaddamar da Matatar Dangote mai karfin tace gangar danyen 650,000 a kullum, wadda aka gina a kan Dala biliyan 19.
Ana kuma kyautata zaton matatar za ta taimaka wajen rage matsalar mai da dogaro da kasashen waje a bangaren.
Hakan zai rage kashi 30 na kudaden da kasar nan take asara a bangaren musayar kudaden waje domin shigo da kayayyaki.
A hiharsa da Premium Times, Aliko Dangote ya ce: “Tun shekarun 1970 ake fama da matsalar mai a kasar nan. Wannan matata za ta taimaka wajen magance matsalar, amma akwai mutanen da ba su so, saboda tawa ce.
“Saboda haka a shirye nake in bar musu matatar, NNPCL ya zo ya saya kawai ya ci gaba da gudanar da ita,” in ji shi.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa Shugaban NMDPRA ya gurfana a ranar Litinin a gaban kwamitin Majalisar Wakilai don amsa tambayoyi kan wannan lamari.
Majalisar na so ta gano ko da gaske gwamnati tana da hannu a makarkashiyar da Aliko Dangote ke zargi.
Kwararru a fannin tattalin arziki dai sun shawarci Gwamnatin Tarayya da hukumominta su ba da damar kafa matatun mai masu zaman kansu irin ta Dangote, don bunkasa tattalin arzikin kasa
Aminiya ta nemi jin gaskiyar ikirarin da Farouk ya yi cewa Fadar Shugaban Kasa na goyon bayan hukumar kan dambarwarsu da Matatar Dangote.
Wakilinmu ya tuntubi Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Yada Labarai, Bayo Onanuga, amma ya ki cewa komai.
Amma ya ba da lambar Babbar Mai Ba Shugaban kasa Shawara kan Harkokin Makamashi, Misis Olu berheijen.
Sai dai duk kokarin Aminiya na samun ta ya faskara, domin kuwa ba ta amsa kiran waya ba, haka kuma ba ta amsa rubutaccen sakon da ta aika mata ba.
Mun so yin amfani da damar domin jin irin matakin da Shugaban kasa ya dauka ko zai dauka kan lamarin, a matsayinsa na mai rike da mukamin Ministan Mai.
Wannan dambarwa dai ana ganin babbar illa ce ga gwamnati, kasancewar wasu ’yan kasar nan sun fara cewa zargin ana yi wa matatar zagon kasa.
Masana na ganin cewa wannan rikici zai kawo wa kasar nan cikas, domin zai kashe wa masu son zuba jari a kasar nan gwiwa
Yadda matsalar Matatar Dangote ta fito fili Da yake magana a taron shekara-shekara na Afreximbank a Nassau a kasar Bahamas, a watan Yuni, Alhaji Aliko Dangote ya ce matatarsa za ta samar da ganga 650,000 a kowace rana.
Mataimakin Shugaba mai kula da Harkokin Man Fetur da Iskar Gas a Kamfanin Dangote Industries Limited, Debakumar Edwin ya zargi kamfanonin mai na duniya da ke Nijeriya da kokarin durkusar da matatar ta Dangote.
Edwin ya ce da gangan kamfanonin suke kawo cikas ga kokarin da matatar ke yi na sayen danyen mai a cikin gida ta hanyar kara farashi sama da farashin kasuwa, lamarin da ya tilasta mata shigo da danyen mai daga kasashe irin su Amurka, wanda hakan ya haifar da tsadar farashin kayayyakinta.
A baya-bayan nan Hukumar NUPRC ta gana da masu samar da danyen mai da masu matatun mai a Nijeriya domin tabbatar da cikakkiyar biyayya ga ka’idojin samar da danyen mai a cikin gida kamar yadda aka bayyana a karkashin Sashe na 109(2) na Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA).
A cewar hukumar ana sa ran kamfanonin mai na kasashen duniya su biya bukatun mai na cikin gida ta hanyar samar da danyen mai ga matatun kasar nan kafin fitar da shi zuwa kasashen waje.
Dokar wadda tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba wa hannu, kwanan nan ne Hukumar NUPRC ta sa ido kan aiki da ita.
A cewar hukumar, an wajabta wa kamfanonin na duniya fara sayar wa matatun mai na cikin gida kafin fitar da su zuwa kasashen waje.
Hukumar NUPRC ta ce za ta kasance mai shiga tsakanin masu tace mai na gida da masu samar da man a lokacin da ba a iya kammala yarjejeniya kan danyen man fetur ba, wanda hakan zai taimaka wajen shirya yarjejeniyar saye da sayar da kayayyaki bisa tsarin mai saye da mai bukatar saya.
Har ila yau, a wata hira da ya yi da CNN a kwanan baya, Aliko Dangote, ya ce: “Kamfanin NNPC na yin iya bakin kokarinSa, amma wasu daga cikin kamfanonin mai na duniya, suna kokarin hana mu danyen mai, saboda kowa ya saba fitar da shi zuwa kasashen waje, kuma ba wanda yake son ya daina fitar da danyen man zuwa kasashen waje.”
Hukumomin sa-ido kan harkokin mai sun mayar wa Dangote martani
Babban Jami’in Hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe, a wata hira da ya yi da shi kwanan nan a gidan talabijin na ARISE Tb, ya ce kuskure ne a yi ikirarin cewa kamfanonin mai na duniya suna kin samar da danyen mai ga masu tace shi a cikin gida.
Zargin da Ahmed ya yi, ya jawo martani daga jama’a
Da yake mayar da martani ga sanarwar, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum mai suna dan Katsina ya ce: “Wannan dabara ce ta kawo cikas ga Matatar Dangote. Wannan shi ne wasan da ake yi a gidajen mai wanda ya sa kasar baki daya ba ta da matatar mai guda da ke aiki tsawon shekaru. Su kyale shi ya sayar mana da nasa haka, za mu saya.”
Shi ma da yake mayar da martani, Bob Eakins ya ce: “Muna magana ce kan inganta samar da kayayyaki a cikin gida da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje domin rage bukatar kudaden musaya da kuma karfafa darajar Naira.”
“Ya kamata ku yi magana game da yadda za a inganta masana’antunmu na cikin gida maimakon yunkurin murkushe su. Kuna so ’yan Nijeriya su mai da hankali kan farfagandarku cewa Dangote na son zama mai kaka-gida. To, Nijeriya ce za ta sha wahala domin Matatar Dangote za ta mayar da hankali ne kawai wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.”
Johnson Ayodeji ya yi tambaya, “Shin Dangote ne ya sa matatun gwamnati suka daina aiki tsawon shekaru? Ko Dangote ya hana wani mutum gina matatar mai? Mun san makiya kasarmu.”
Wani masanin tattalin arziki, Kelbin Emmanuel, ya ce NNPCL ne ke da alhakin rashin samun isasshen danyen mai a cikin gida, maimakon kamfanonin kasashen waje.
Emmanuel ya bukaci Majalisar Dokoki ta kasa da Shugaba Tinubu su nuna damuwa kan gazawar NNPC wajen sa wa Matatar Dangote jarin Dala biliyan 1.7 da ake bukata domin kammala sayen kashi 20 na matatar.
Gwaje-gwaje sun tabbatar da ingancin man Matatar Dangote
A halin da ake ciki, Alhaji Aliko Dangote, ya fadi a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, cewa kayayyakin matatar ba wai kawai sun bi ka’idojin da aka gindaya ba ne, har ma sun zarce na wasu da ake shigowa da su.
“Ta fuskar inganci, babu wanda zai iya samar da wani abin da ya fi namu.
“Na samu sakamako mai dadin ji daga jami’inmu minti biyar da suka wuce, yanzu mun kasa kaiwa ko da 32 ppm,” in ji Dangote.
Ya kalubalanci mahukunta ciki har da Hukumar NMDPRA ta je matatar ta duba ingancin kayayyakinta.
Na janye shirin sa hannun jari a harkar karafa
A wani labarin, Alhaji Aliko Dangote ya ce ya janye shirin sa hannun jari a sabuwar masana’antar karafa a Nijeriya bayan da gwamnati ta zarge shi da neman zama mai kaka-gida a harkokin kasuwanci a kasar nan.
Attajirin ya bayyana a farkon wannan shekarar cewa da zarar babbar matatar ta kammala, inda zai sa jarinsa na gaba shi ne fara gina masana’antar sarrafa karafa ta tan 5,000 da za ta samar da kayayyaki ga kasuwannin Yammacin Afirka.
“Su ma sauran ’yan Najeriya su je su yi hakan, domin ba mu kadai ne ’yan Nijeriya a nan ba, akwai ma wasu ’yan kasar da suke da kudi.
“Ya kamata su shigo da wadannan kudade daga Dubai da sauran sassan duniya don su zuba jari a kasarmu ta haihuwa. Zargin kaka-gida yana da ban takaici sosai. Duk abin da aka ba Dangote, sauran mutane ma an ba su. A gaskiya ma, wasunsu sun fi mu,” in ji Dangote.
Masana sun yi magana
Wani masanin tattalin arziki kuma Babban Jami’i Zartarwar Cibiyar Bunkasa Masana’antu Masu Zaman Kansu, Dokta Muda Yusuf, a tattaunawa da AMINIYA ya ce: “Abin da tattalin arzikin kasar nan ke bukata a wannan lokaci shi ne bunkasa. Tattalin arziki, baya ga inganta zaman lafiya, yana inganta arzikin mutane ta hanyar rage dogaro da shigo da kayayyaki daga kasashen waje.
“Saboda haka, gwamnati da hukumominta, suna bukatar bayar da duk wani tallafi mai yiwuwa don tallafa wa tace man fetur a cikin gida.”
Wani farfesa a fannin tattalin arziki, Kingsley Nwokoma, ya ce kamata ya yi gwamnati ta mayar da hankali wajen kammala nata matatun mai domin kara zurfafa kasuwannin cikin gida ta yadda matatun mai za su rika aiki irin yadda matatun mai na zamani ke yi.
Nwokoma, wanda shi ne Daraktan Cibiyar Bincike da Nazarin Siyasa ta Jami’ar Legas, ya ce: “Zargin da ake yi na yin kaka-gida babu tushe a ciki, domin gwamnati ta riga ta yi shirin gyara matatun Fatakwal, Warri har da Kaduna. Don haka, idan wadannan matatun uku suna aiki kamar yadda ake samar da mai a yau da kullum, duk wannan korafin zai kau, haka kuma in jihohi suna da nasu matatun mai na yau da kullum.”
Minista ya shiga don sasanta NNPC da Dangote
Minista a Ma’aikatar Man Fetur, Mista Heineken Lokpobiri ya shiga tsakani da nufin sasanta rikicin da ya kunno kai a tsakanin Matatar Dangote da Kamfanin Mai na kasa (NNPCL).
Ministan ya kira taron gaggawa na masu ruwada-tsaki domin samun hadin kai da kuma shawo kan matsalar.
Masu ruwa-da-tsakin sun hada Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da Shugaban Kamfanin NNPCL, Malam Mele Kolo Kyari.
Sauran su ne Shugaban Hukumar MNDPRA, Farouk Ahmed da takwaransa na Hukumar Hako danyen Mai ta kasa (NUPRC), Mista Gbenga Komolafe
Daga Wakilinmu: Sunday M. Ogwu, Muideen Olaniyi, Abuja da Abdullateef Aliyu, Legas Fassara Ahmed Mohammed, Bauchi