Tura ta kai bango —Ma’aikatan Najeriya da ba a biya albashin Janairu ba
Ma’aikatan gwamnatin tarayya a Najeriya sun chachaki gwamnatin kasar game da rashin biyan su albashin watan Janairun da ya gabata.
Ma’aikatan sun ce wannan shi ne karon farko da gwamnati ta dauki tsahon lokaci haka ba tare da biyan su albashi ba, tun kafin zuwa cutar Corona, lokacin da ma’aikatan ke zaune a gida.
Ofishin Akanta janar na kasar ya ce jan kafa wajen biyan albashin ya samo asali ne sakamakon rashin kammala aikin tattara bayanan ma’aikata a kan lokaci da ake yi duk wata.
Sanarwar ta bukaci ma’aikatan da su yi wa gwamnati uzuri da kara hakuri, tana mai cewa nan da kowanne lokaci za su sami albashin nasu.
Ba shakka wannan mataki na gwamnati zai zama kari kan tashin hankali da kuma tsadar rayuwa da ’yan aksar ke kokawa da ita tun bayan da gwamnatin ta yanke shawarar cire tallafin man fetur.
’Yan Najeriya na fuskantar tsadar rayuwa wadda rabon da aga irin ta tun shekaru sama da 100 da suka gabata, lamari da ke kara tagayyara iyalai.