Tura ta kai bango —Masu zanga-zanga

Masu zanga-zangar tsadar rayuwa sun bayyana cewa, “tura ce ta kai bango, suka fito kan tituna

Tura ta kai bango —Masu zanga-zanga

Masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, sun ce, “tura ce ta kai bango, suka fito kan tituna.

“Za mu ci gaba da fitowa yin irin wannan zanga-zangar lumana har zuwa ranar 10 ga watan Agusta da muke ciki.”

Aminiya ta gano cewa kungiyoyin matasa daban-daban ne suka jagoranci zanga-zangar da suka zagaya sassan birnin Ibadan dauke da rubutattun kwalaye damke bayani a kan bukatar mahukunta su hanzarta daukar matakin kawo karshen matsalolin da miliyoyin jama’ar kasa suka fada ciki.

Masu zanga-zangar da suka samu rakiyar jami’an tsaro sun yi tattaki ne daga harabar Jami’ar Ibadan (UI) da kan hanyar Kasuwar Bodija da Zango da Mokola Round About da Iwo Road da Challenge da Apara da sauran fitattun unguwanni a birnin Ibadan.

Sun yi ta rera wakoki da kalaman batanci ga shugabannin kasa, musamman sunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka fi ambata suna cewa shi ne ya jagoranci sabon salon mulkin da ya haifar da matsalolin da kasa ta fada ciki a yanzu.

Aminiya ta gano cewa har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto ana ci gaba da yin wannan zanga-zangar lumanar lami lafiya a Ibadan.

Ba mu shiga zanga-zanga ba, amma a magance rayuwa —Hausawan Ibadan

Kungiyoyin matasan Hausawa a birnin dai sun ki shiga zanga-zangar saboda fargabar da suke yi na yiwuwar kai masu hari a unguwanninsu da wasu ’yan daba suke yi a kowane lokaci aka yi irin wannan zanga-zangar.

Daya daga cikin shugabannin kungiyoyin matasan Hausawan, Yusuf Aboki, ya ce, “mutanenmu masu kananan sana’o’i musamman ’yan Okada tun da safe suka fito suna gudanar da harkokinsu lami lafiya ba tare da damuwa ba.

“’Yan kasuwa kuma akwai da yawa daga cikinsu da suka bude shaguna da rumfuna a cikin kasuwanni.

“Amma mafi yawancin jama’armu sun yi zamansu ne a cikin gidajensu” in ji shi.