Turaren wuta: Amfaninsa ga tufafi

Turare abin so ne ga kowa, domin yana sanya natsuwa da kuma kwanciyar hankali. Don kawata kwalliyarki yana da kyau ki fesa turare kullum. Akwai turaren gargjiya kamar su ‘humra’ da ‘turaren wuta’ da ‘kullaccam’ irin na ‘yan Maiduguri da kuma turaren kanti kamar su ‘Dior’ da ‘cool water’ da sauransu. Yadda za a yi […]

Turaren wuta: Amfaninsa ga tufafi
Turaren wuta: Amfaninsa ga tufafi

Turare abin so ne ga kowa, domin yana sanya natsuwa da kuma kwanciyar hankali. Don kawata kwalliyarki yana da kyau ki fesa turare kullum. Akwai turaren gargjiya kamar su ‘humra’ da ‘turaren wuta’ da ‘kullaccam’ irin na ‘yan Maiduguri da kuma turaren kanti kamar su ‘Dior’ da ‘cool water’ da sauransu.

Yadda za a yi amfani da turaren gargajiya
Ki zuba garwashi a cikin kasko, sannan ki dora ‘kabbasa’ (za a iya samunsa a Barno) a kan kaskon. Daga nan ki zuba turaren wuta a cikin kaskon, sannan ki rufe kabbasa da tufafin da za ki sanya a ranar ko kuma wanda za ki je unguwa da shi. Ki bari hayakin ya shiga tufafin sosai.
Bayan haka, sai ki shafa ‘kulaccam’ (kamar man shafawa yake, amma da turarurruka ake hada shi). Bayan kin yi wanka sai ki shafa a matsayin man shafawa.
Daga nan ki shafa humra; fari ko baki a jikin tufafin. Idan tufafin mai duhu ne sai ki shafa bakar humra, idan kuma tufafin mai haske ne sai ki shafa farar humra.
Idan kuma kina son amfani da turaren kanti, fesawa kawai za ki ba tare da kin yi wani abu ba. Amma na gargajiya ya fi dadewa kasancewar ko tufafi ya yi datti da kyar a ji wari na tashi saboda kamshin turaren.