Turken turnukun –kiyayya
Iro-Dogon Turke ja-gaban al’ummar Turakun-tarairayar uwa da ’ya’ya ya afka taskun turka-turkar turnukun kiyayya, bayan da baraden bindigar kasarsa suka yi yunkurin yi wa gwamnatinsa juyin masa matar mai sana’ar na-duke. A farfajiyar wannan makaranta mun dai taba labarta muku yadda uwargidan wani mai sana’ar na-duke da limbu-limbu a cikin lambu ta afka lambatu, bayan […]
Iro-Dogon Turke ja-gaban al’ummar Turakun-tarairayar uwa da ’ya’ya ya afka taskun turka-turkar turnukun kiyayya, bayan da baraden bindigar kasarsa suka yi yunkurin yi wa gwamnatinsa juyin masa matar mai sana’ar na-duke. A farfajiyar wannan makaranta mun dai taba labarta muku yadda uwargidan wani mai sana’ar na-duke da limbu-limbu a cikin lambu ta afka lambatu, bayan da ta yi masa isgilin cewa, ita tamkar ‘waina take,’ idan ta bar gidansa, za ta juya ne kawai cikin katafaren matsugunin hamshakin attajiri; sai dai ina, sai da ta shekare a akurkin iyayenta, inda ta karke da neman a lallabo tsohon mai gidanta ya dawo da igiyar turkensu.
Baraden bindiga sun yi fafutikar datse igiyar turken Ja-gaban Turkawa, amma ina, nan da nan ya aike wa magoya bayansa da sako, inda suka fafata wajen tarwatsa aniyar miyagu. Sai dai tsugunne ba ta kare ba, domin bayan da Mai-duka, Mai-kowa, Mai-komai ya tseratar da Iro-Dogon Turke sai ya shiga fafutikar tarwatsa magabtansa da ya jefa azargagiyar zargi mai karfi a kan su. Yanzu ya cumimiye baraden bindiga da farar tagiya har dubu madambaci da ’yan mutsamutsai. Wadanda ya kasa cafko su, to ya yi musu bita-da-kulli, domin a makon da ya arce na ji an ce, wai Gwamnatin Turakun Tarairayar Uwa-da-’ya’ya ta bijiro da bukatar garkame cibiyoyin koyon watsattsake da buda wagagen littattafai sili da kwanciyar magirbi da ke fadin kasar Haurobiya, wadanda akasarinsu mallakar mutanen Iro-Dogon Turke ne, amma mabiya Shehun Malamin addini da ya cilla gudun hijira a kasar Uban-mama Jikan Kenyawa, Jagoran Amurkawa.
Kuma a lokacin da Siriyawa suka saduda a hannun Bashiru dan Asadu, Turakun turke a tarairayi ’yan gudun hajaran, majaran da masu artabun tada kayar baya. Kyakkyawar aniyar magabata dai ta cece su daga magabta, har Mai-duka ya datar da su da nagargarun makusanta. Ni dai ban a jin batutuwa a yaren Iro-Dogon Turke, don haka a samu wanda zai nusar da shi cewa, lallai ya tsahirta da damke wadanda aka goga musu rabu.
Haurobiyawa Iro-Dogon Turke mutumin mutane, in an yi la’akari da siyasar Turakun tarairayar Uwa-da-’ya’ya, amma tafarki takunsa na iya haifar masa matsala. Saboda haka nike ganin akwai wadanda suka taka sawun kusu, idan har an gano cewa wasu ne suka goga musu rabu sai a yi hanzari warware musu sasari, tun kafin a dawo da dabbaka dokar kisan gilla da ake amfani da ita. Kuma batun kassara harkokin hada-hadar kasuwancinsu bai dace ba. Mafita a wannan lamari it ace a dumfari masu aika-aika na hakika, don gudun ka da a karke da dukan taiki, alhali an kyale aura yana hauragiyarsa.
Kuma ya kamata Gwamnatin Turakun Tarairayar Uwa-da-’ya’ya ta fasko cewa, akwai dimbin masu jini a jika da aka yi musu ingiza mai kantu ruwa, matukar a samu tsame rukunin irin wadannan mutane, to sai a yi kokarin ba su horon tarairaya da biyayya ga dokokin kasa, t ayadda za su daina sha’awar soye-soyen zukatan masu tunkuda su cikin rukuki.
Haurobiyawa ban so yin tsokaci akan turka-turkar turnukun kiyayya da ke hankoron maye gurbin tarairaya da biyayya, a kasar da ke samun tumbatsa da kasura, in an kwatanta da tsararrakinta da ke nahiyar Asiya ko wani yankin Turai da ta dade da hankoron yin kutse. Magabtan Dama-dama-da-kurda-kurdar was an Samson siya-siya da suka tsuwurwurta juyin waina a hamshakiyar kasa, ba su samu lagon jagora ba ne, don yana kyautata wa al’ummarsa, amma duk da haka akwai sauran rina a kaba, kuma Mai-duka ya tarfa wa garinsu nono domin yanzu babu tada karyar Kurdawa.
’Yan makaranta an ce ba a guzurin magabci da makusanci, kusan duk inda mutum ya taka ya je, tabbas zai iske su. Don haka tabbaci a kan haka, wasu daga cikin magabtan Baban-burin-huriyya sun rikide sun zama masoyan makusanta, kuma akwai makusantan da suka yi wuntsulagudi-gudi suka kide zuwa gunduma-gunduman magabta, musamman ganin yadda ya tsananta wa masu kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma. Irin wadannan magabta na yunkurin ingiza al’umma cikin taskun turnukun kiyayya. Duk da cewa, ba ma wassafa cewa akwai miyagun da za su iya kwata juyin wainar da aka yi wa Gwamnatin Iro-Dogon Turke, amma matukar ba a yi wa tufkar hanci ba, suna iya kawo wa kasar nan tarnaki.
Labin da ya dace abi don bullewa, shi ne, a nusar da masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai illar da ’yan watanda suka yi wa Haurobiya, al’amarin da suka dade da tsuwurwurtawa tun zamanin mulkin mulaka’u na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, kodayke dai kaikayi ya koma kan mashekiyya, tunda kiyayya ta kullu tsakanin bangaren Mudun Sharfadidi da karfafan mutumin nan dan garin masu rake.
A wannan barayin nike karajin kiran Baban-burin-huriyya kan lallai ya bullo da dabarar inganta rayuwar direbobin alli, tare da yi musu manhaja mara hajijiya, ta yadda za su ji dadin horar da ’yan dugwi-dugwi ko da Turakun tarairayar Uwa-da-’ya’ya sun garkame kofar cibiyoyin koyon watsattsake da buda wagagen littattafai da ke fadin kasar nan. Matukar mahukuntanmu ba su fasko rudanin siyasar da ya baibaye magabta da makusanta Iro-Dogon turke ba, to ka da mu yi kutse cikin lamarinsu. Sannan gwamnatin Haurobiya ta bijiro da bukatar a cefanar mata da Turken hadakar Haurobiya da Turakun tarairayar uwa-da-’ya’ya, don gudun ka da su kwata mana tabargazar da suka yi wa kasar cikin makonnin da suka arce.
Su kuwa jami’an Asusun ilimi da ke Jam’in jama’ar jami’o’in Haurobiya ya kamata a yi musu saiti, ta yadda za su daina tsallen badake wajen laluben karin lada da la’adar kadagon kwadago. Kai lallai ka da a yasar al’amarin Bokayen Turai, ta yadda za su rika tarairayar majinyata ba sai an tsallaka ketare ba.
Wannan kira namu ya zama dole. Musamman in an yi la’akari da cewa wanzuwar tsilli-tsillin matsalolin da ke ci wa al’umma tuwo a kwarya su ke haifar da juyin wainar matar mai sana’ar na-duke. Kuma badala da juhala suka haifar aka yin yunkurin kifar da Gwamnatin Iro-Dogon Turke. Don haka mu dauki izina Haurobiyawa.
Farfajiyar wannan makaranta na fatan ganin Haurobiya ta zama Turakun soyayya, amma ba na soye-soyen zukatan illata kasa ba. Kuma ta zama cibiyar tunanin zama-babu-zamiya, tamkar yadda ta wanzu a yankin Mwanza na kasar Tanzaniya. Jam’iyyar Baban-burin-huriyya da Tunanin-bunu, lallai ta kara himma wajen magance zogi da radaddin kurungun al’umma, tare da nusar da al’ummar kasa bin doka da oda.