Turkiya ta gana da hukumar kwastam kan fasakaurin makamai
Jakadan kasar Turkiya a Najeriya, Mista Hakan Cakil ya gana da Shugaban Rundunar Shigi da Fici ta Kwastam, Hameed Ibrahim Ali don tattara bayanan wadanda suka yi fasakaurin makamai daga kasar Turkiya zuwa Najeriya. Ali ya bayyana damuwar Hukumar Kwastam da sauran ’yan Najeriya yadda hukumar ta rika kama dubban bindigogi masu sarrafa kansu har […]

Jakadan kasar Turkiya a Najeriya, Mista Hakan Cakil ya gana da Shugaban Rundunar Shigi da Fici ta Kwastam, Hameed Ibrahim Ali don tattara bayanan wadanda suka yi fasakaurin makamai daga kasar Turkiya zuwa Najeriya.
Ali ya bayyana damuwar Hukumar Kwastam da sauran ’yan Najeriya yadda hukumar ta rika kama dubban bindigogi masu sarrafa kansu har sau hudu da yawansu ya kai dubu biyu da 671 da aka yi fasakaurinsu daga kasar Turkiya.
Ya ce hakan na nuna akwai hannun mahukuntan kasar Turkiya cikin lamarin.
A wata sanarwa da Mai Magana Yawun Hukumar Kwastam, Mista Joseph Attah ya sanya wa hannu ta nuna cewa ganawar wacce ta dauki kimanin awa biyu ta yi armashi inda jakadan kasar Turkiya ya bayar da tabbacin ci gaba da goyon bayan jami’an tsaron Najeriya.
Ya ce kasarsa Turkiya ba za ta goyi bayan shigar da muggan abu cikin Najeriya ba.