Turkiyya ta ayyana dokar ta-baci ta wata 3 a yankunan da girgizar kasa ta yi barna
Mutanen da suka rasu yanzu sun haura 5,200
Shugaban Kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya ayyana dokar ta-baci ta tsawon wata uku a larduna 10 na kasar bayan girgizar kasa ta halaka sama da mutum 5,200.
Girgizar kasar dai mai karfin 7.8, wacce ta auku a yankuna Kudu maso Gabashin Turkiyya da kuma Arewa maso Yammacin Siriya ta mayar da gine-gine da dama kufai.
- Dillalan man fetur a fadin Najeriya sun tsunduma yajin aiki
- HOTUNA: Tinubu ya ziyarci mahaifiyar ’Yar’aduwa a Katsina
A cikin wani jawabinsa da aka watsa a gidajen talabijin din kasar, Shugaba Erdogan ya ce, “Mun yanke shawarar ayyana dokar ta-bacin ne saboda ma’aikatan kwana-kwananmu su sami zarafin aikin ceto cikin gaggawa.”
Shugaba Erdogan ya kuma ce ya zuwa yanzu, akalla kasashe 70 ne suka yi tayin taimaka wa aiki nemowa da kuma ceto mutane.
Ya kuma ce kasar za ta yi amfani da gine-ginen otel dinta da birnin yawon bude ido na Antalya, a matsayin gidajen wucin gadi ga mutanen da iftila’in ya fada wa.
Shugaban na Turkiyya ya ce ya zuwa ranar Talata, yawan mutannen da suka mutu a kasarsa sun kai 3,549 sai wasu kuma a Siriya, wadanda idan aka hada jimlarsu, sun haura 5,000.
Jawabin Shugaban na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da aiki ceto a rana ta biyu tun bayan girgizar kasar, cikin tsananin sanyi.